Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 14

Mulkin da Za A Yi Bisa Dukan Duniya

Mulkin da Za A Yi Bisa Dukan Duniya

Ka san ko wane Mulki ne muke magana a kai?— E, Mulkin Allah ne, kuma shi ne zai sa duniya ta zama aljanna. Za ka so ka ƙara koya game da wannan Mulkin?—

Kowane mulki yana da sarki. Kuma sarkin yana sarauta bisa mutanen ƙasarsa. Ka san ko wane ne Sarkin Mulkin Allah?— Yesu Kristi ne. Yana sama. Ba da daɗewa ba, zai zama Sarki bisa kowa a duniya! Kana ganin za mu yi farin ciki idan Yesu ya zama Sarki bisa duniya?—

Mene ne kake so ka ga ya faru a cikin Aljanna?

Za mu yi farin ciki sosai! A cikin Aljanna, mutane za su daina faɗa da juna. Dukan mutane za su ƙaunaci juna. Babu wanda zai yi rashin lafiya ko ya mutu. Makafi za su soma gani, kurame za su soma jin magana kuma guragu za su yi gudu su yi tsalle. Mutane za su samu abinci da yawa. Dabbobi za su yi wasa da juna kuma mu ma za mu yi wasa da su. Za a ta da waɗanda suka mutu. Maza da mata da ka karanta labarinsu a wannan ƙasidar, kamar su Rifkatu da Rahab da Dauda da kuma Iliya za su tashi daga mutuwa! Za ka so ka gan su sa’ad da aka ta da su?—

 Jehobah yana ƙaunarka kuma yana so ka yi farin ciki. Idan ka ci gaba da koya game da Jehobah kuma ka yi masa biyayya, za ka yi rayuwa har abada a cikin aljanna mai kyau! Abin da kake so ke nan?—

KARANTA NASOSSIN NAN

  • Ishaya 2:4; 11:6-9; 25:8; 33:24; 35:5, 6

  • Yohanna 5:28, 29; 17:3