Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 9

Irmiya Ya Ki Ya Daina Yin Magana Game da Jehobah

Irmiya Ya Ki Ya Daina Yin Magana Game da Jehobah

Me ya sa mutanen nan suke fushi da Irmiya?

Jehobah ya sa a ceci Irmiya

A wani lokaci, mutane sukan yi mana dariya ko kuma su yi fushi da mu don mun yi musu magana game da Jehobah. Hakan zai iya sa mu daina yin magana game da Allah. Hakan ya taɓa faruwa da kai kuwa?— Littafi Mai Tsarki ya ba mu labarin wani matashi da yake ƙaunar Jehobah, amma saura kaɗan da ya daina yin magana game da Allah. Sunansa Irmiya ne. Bari mu ƙara koya game da shi.

A lokacin da Irmiya yake matashi, Jehobah ya aike shi ya gaya wa mutane su daina yin abubuwa da ba su da kyau. Yin hakan bai da sauƙi kuma Irmiya ya ji tsoro. Ya ce wa Jehobah: ‘Ban san abin da zan faɗa ba. Ni ƙaramin yaro ne.’ Amma Jehobah ya gaya masa: ‘Kada ka ji tsoro. Zan taimake ka.’

 Sai Irmiya ya soma gaya wa mutane cewa Allah zai yi musu horo idan ba su daina yin abubuwa da ba su da kyau ba. Kana ganin mutanen sun yi abin da Irmiya ya gaya musu?— A’a. Wasu sun yi masa dariya, wasu sun yi fushi da shi sosai, wasu kuma sun so su kashe shi! Yaya kake ganin Irmiya ya ji?— Ya ji tsoro kuma ya ce: ‘Ba zan sake yin magana game da Jehobah ba.’ Amma ya daina ne da gaske?— A’a, bai daina ba. Yana ƙaunar Jehobah sosai, saboda haka ya ƙi ya daina yin magana game da shi. Domin Irmiya ya ci gaba da yin wa’azi, Jehobah ya cece shi.

Alal misali, akwai lokacin da wasu mugayen mutane suka jefa Irmiya a cikin wani rami. Ramin ya yi zurfi sosai kuma yana da laka. Ba abinci ko ruwa a wurin. Waɗannan mutanen sun so su bar Irmiya a cikin ramin don ya mutu. Amma Jehobah ya cece shi.

Mene ne ka koya daga misalin Irmiya?— Ko da yake akwai lokatan da Irmiya ya ji tsoro, bai daina yin magana game da Jehobah ba. Idan kana yi wa mutane magana game da Jehobah, za su iya yi maka dariya ko su yi fushi da kai. Kana iya jin kunya ko tsoro. Amma kada ka daina yi wa mutane magana game da Allah. Jehobah zai taimake ka a kowane lokaci, kamar yadda ya taimaki Irmiya.

KARANTA NASSOSIN NAN

  • Irmiya 1:4-8; 20:7-9; 26:8-19, 24; 38:6-13