Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 6

Dauda Bai Ji Tsoro Ba

Dauda Bai Ji Tsoro Ba

Mene ne kake yi idan tsoro ya kama ka?— Wataƙila kana guduwa zuwa wajen mama ko baba don su taimake ka. Amma, akwai wani kuma da zai iya taimaka maka. Ya fi kowa ƙarfi. Ka san ko wane ne shi?— Jehobah ne. Bari mu yi magana a kan wani matashi mai suna Dauda a cikin Littafi Mai Tsarki. Ya san cewa Jehobah zai taimake shi a kowane lokaci, saboda haka, bai ji tsoro ba.

Tun daga lokacin da Dauda yake jariri, iyayensa sun koya masa ya ƙaunaci Jehobah. Hakan ya sa Dauda bai ji tsoro ba a lokacin da ya haɗu da abubuwa masu ban tsoro. Ya san cewa Jehobah Abokinsa ne kuma Zai taimake shi. Akwai lokacin da Dauda yake kiwon tumaki, sai wani babban zaki ya zo ya kama tunkiyarsa da baki. Ka san abin da Dauda ya yi? Ya bi zakin da gudu kuma ya kashe zakin da hannunsa! A wani lokaci kuma, wata dabba da ake kira bear ta zo ta kama tunkiyarsa, amma Dauda ya kashe dabbar. Wane ne kake ganin ya taimaki Dauda?— Jehobah ne.

Akwai wani lokaci kuma da Dauda ya nuna cewa bai ji tsoro ba ko kaɗan. A lokacin, Isra’ilawa suna yaƙi da mutanen da ake kira Filistiyawa. Filistiyawan suna da wani soja mai suna Goliyat, dogo ne sosai kuma ƙato. Wannan ƙaton yana yi wa sojojin Isra’ila da kuma Jehobah dariya. Goliyat ya ce idan sojojin Isra’ila sun isa, su zo su yaƙe shi. Amma, dukan Isra’ilawan sun ji tsoronsa. Sa’ad da Dauda ya ji labari, sai ya gaya wa Goliyat cewa: ‘Zan yi yaƙi da kai! Jehobah zai taimake ni, kuma zan yi nasara a kanka!’ Kana ganin Dauda yana da ƙarfin hali?— Yana da ƙarfin hali sosai. Kana so ka san abin da ya faru bayan haka?

Dauda ya ɗauki majajjawarsa da duwatsu guda biyar kuma ya je don ya yaƙi ƙaton. Sa’ad da Goliyat ya ga cewa Dauda ƙaramin yaro ne, sai ya soma yi masa dariya. Amma, Dauda ya gaya masa: ‘Ka zo wurina da takobi, amma ni na zo wurinka da sunan Jehobah!’ Sai ya saka dutse ɗaya a cikin majajjawarsa, ya nufi Goliyat a guje, kuma ya jefe shi. Dutsen ya sami Goliyat a tsakiyar goshinsa. Sai ya faɗi a ƙasa ya  mutu! Hakan ya sa Filistiyawa suka ji tsoro sosai kuma suka gudu. Ta yaya ƙaramin yaro kamar Dauda ya kashe wannan ƙaton mutumin?— Jehobah ne ya taimaki Dauda, kuma Jehobah ya fi wannan ƙaton ƙarfi sosai.

Dauda bai ji tsoro ba domin ya san cewa Jehobah zai taimake shi

Mene ne ka koya daga labarin Dauda?— Jehobah ya fi kowa ƙarfi. Kuma shi Abokinka ne. Saboda haka, a duk lokacin da ka ji tsoro, ka tuna cewa Jehobah zai iya taimaka maka ka yi ƙarfin hali!

KARANTA NASSOSIN NAN

  • Zabura 56:3, 4

  • 1 Sama’ila 17:20-54