Koma ka ga abin da ke ciki

Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin?

Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin?

WAƊANNE tambayoyi? Tambayoyi mafi muhimmanci da mutane suke yi. Wataƙila ka taɓa yin tunani game da waɗannan tambayoyin:

  • Allah yana kula da mu kuwa da gaske?
  • Yaƙi da wahala za su taɓa ƙarewa kuwa?
  • Me ke faruwa da mu sa’ad da muka mutu?
  • Matattu suna da bege kuwa?
  • Ta yaya zan yi addu’a kuma Allah ya ji ni?
  • Ta yaya zan iya samun farin ciki a rayuwa?

A ina za ka iya samun amsoshin waɗannan tambayoyin? Idan ka je inda ake ajiye littattafai ko kuwa inda ake sayar da su, za ka iya samun dubban littattafai da suke da’awar cewa suna ɗauke da amsoshin waɗannan tambayoyin. Amma a yawancin lokaci, littattafan suna ƙaryata juna. Wasu sukan kasance kamar suna da amfani, amma daga baya sukan zama tsohon yayi kuma a sake juya su ko kuwa a sake su.

Amma akwai wani littafin da ke ɗauke da tabbatattun amsoshi. Littafi ne na gaskiya. Sa’ad da yake yin addu’a ga Allah, Yesu Kristi ya ce: “Maganarka ita ce gaskiya.” (Yohanna 17:17) A yau mun san cewa wannan Maganar ita ce Littafi Mai Tsarki. A shafuffuka na gaba, za ka sami ƙarin haske game da amsoshi na gaskiya da Littafi Mai Tsarki yake ɗauke da su game da tambayoyin da ke sama.

Allah Yana Kula da mu Kuwa da Gaske?

Mutum cikin jama’a

ABIN DA YA SA AKA YI WANNAN TAMBAYAR: Muna zaune ne a duniyar da take cike da mugunta da kuma rashin adalci. Yawancin addinai suna koyar da cewa nufin Allah ne mu sha wahala.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA: Allah ba ya jawo mugun abu. “Daɗai Allah shi yi mugunta! Mai-iko duka shi yi aikin saɓo!” in ji Ayuba 34:10. Allah yana da manufa mai kyau ga mutane. Shi ya sa Yesu ya koya mana mu yi addu’a kamar haka: “Ubanmu wanda ke cikin sama,… Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Matta 6:9, 10) Domin Allah ya damu da mu sosai shi ya sa ya ɗauki mataki mai girma don ya cika nufinsa.—Yohanna 3:16.

Ka dubi Farawa 1:26-28; Yaƙub 1:13; da kuma 1 Bitrus 5:6, 7.

Yaƙi da Wahala za su Taɓa Ƙarewa Kuwa?

Sojoji

ABIN DA YA SA AKA YI WANNAN TAMBAYAR: Yaƙi yana ci gaba da ɗauke rayukan mutane masu yawa. Wahalar da mutane suke sha ta shafi dukanmu.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA: Allah ya faɗi cewa lokaci na zuwa da zai sa salama ta kasance a dukan duniya. A ƙarƙashin Mulkinsa, wato, gwamnati na samaniya, mutane ba za su ‘ƙara koyon yaƙi’ ba. Maimakon haka, “za su… bubbuge takubansu su zama garmuna.” (Ishaya 2:4) Allah zai kawar da dukan rashin adalci da wahala. Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa: “[Allah] za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin zuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari [har da rashin adalci a yau da kuma wahaloli] sun shuɗe.”—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.

Ka dubi Zabura 37:10, 11; 46:9; da kuma Mikah 4:1-4.

Me ke Faruwa da Mu Sa’ad da Muka Mutu?

Makabarta

ABIN DA YA SA AKA YI WANNAN TAMBAYAR: Yawancin addinai a duniya suna koyar da cewa akwai wani abu a cikin mutum da ke rayuwa bayan mutuwa. Wasu sun yarda cewa matattu za su iya cutar da waɗanda suke raye ko kuwa Allah yana horon mugaye ta wajen jefa su cikin wuta har abada.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA: Mutane ba sa rayuwa sa’ad da suka mutu. “Matattu ba su san komi ba,” in ji Mai-Wa’azi 9:5. Tun da yake matattu ba za su iya sanin komi ba ko kuwa su ji wani abu, to ba za su iya cutar ko kuma su taimaka wa masu rai ba.—Zabura 146:3, 4.

Ka dubi Farawa 3:19; da kuma Mai-Wa’azi 9:6, 10.

Matattu Suna da Bege Kuwa?

Yarinya tana kukan mutuware iyayensa

ABIN DA YA SA AKA YI WANNAN TAMBAYAR: Muna son mu rayu, kuma muna son mu more rayuwa tare da waɗanda muke ƙauna. Shi ya sa muke ɗokin sake ganin ƙaunatattunmu da suka mutu.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA: Za a ta da yawancin mutanen da suka mutu daga matattu. Yesu ya yi alkawari cewa “waɗanda suna cikin kabarbaru za… su fito.” (Yohanna 5:28, 29) Cikin jituwa da ainihin manufar Allah, waɗanda aka ta da a matsayin mutane za su sami damar yin rayuwa a aljanna a duniya. (Luka 23:43) Wannan alkawarin da zai cika a nan gaba ya haɗa da koshin lafiya da rai na har abada ga mutane masu biyayya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zabura 37:29.

Ka dubi Ayuba 14:14, 15; Luka 7:11-17; da kuma Ayukan Manzanni 24:15.

Ta Yaya Zan Yi Addu’a Kuma Allah Ya Ji Ni?

Mutum yana addu’a

ABIN DA YA SA AKA YI WANNAN TAMBAYAR: Mutanen da suke cikin dukan addinai suna yin addu’a. Duk da haka, wasu suna jin cewa ba a amsa addu’o’insu.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA: Yesu ya koya mana cewa mu daina maimaita tsarin kalmomin da aka kafa a addu’o’inmu. Ya ce: “Cikin yin addu’a kuma kada ku yi ta maimaitawa ta banza.” (Matta 6:7) Idan muna son Allah ya ji addu’o’inmu, dole ne mu yi addu’a a hanyar da yake so. Don mu yi hakan, muna bukatar mu koyi nufin Allah kuma mu yi addu’a bisa hakan. 1 Yohanna 5:14 ta bayyana cewa: “Idan mun roƙi komi daidai da nufinsa, [Allah] yana jinmu.”

Ka dubi Zabura 65:2; Yohanna 14:6, 14; da kuma 1 Yohanna 3:22.

Ta Yaya Zan Iya Samun Farin Ciki a Rayuwa?

Mace da take neman farin ciki ta wajen karatun Littafi Mai Tsarki

ABIN DA YA SA AKA YI WANNAN TAMBAYAR: Yawancin mutane sun gaskata cewa kuɗi, suna, ko kuwa siffa mai kyau zai sa su farin ciki. Shi ya sa suke biɗar waɗannan abubuwan, kuma duk da haka ba sa samun farin cikin da suke nema.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA: Yesu ya bayyana ainihin abin da zai iya sa farin ciki sa’ad da ya ce: “Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu.” (Matta 5:3, Littafi Mai Tsarki) Za mu iya samun farin ciki na gaskiya idan muka ɗauki matakai don mu biya bukatarmu mafi girma, wato, muradinmu na sanin gaskiya game da Allah da kuma manufarsa a gare mu. Wannan gaskiyar tana cikin Littafi Mai Tsarki. Sanin wannan gaskiyar zai iya taimaka mana mu san ainihin abin da ya fi muhimmanci da kuma abin da bai da muhimmanci. Idan muka bar Littafi Mai Tsarki ya yi mana ja-gora a shawarwarinmu da matakan da muka ɗauka, hakan zai ƙara kyautata rayuwarmu.—Luka 11:28.

Ka dubi Misalai 3:5, 6, 13-18; da kuma 1 Timothawus 6:9, 10.

Batutuwan da ke sama bayanai ne kawai ƙalilan na amsoshin da Littafi Mai Tsarki ya ke ɗauke da su na waɗannan tambayoyin guda shida. Kana son sanin fiye da haka? Idan kana cikin waɗanda “suka san talaucinsu na ruhu,” za ka so ka sami ƙarin bayani. Wataƙila kana tunani game da tambayoyi kamar su: ‘Idan Allah yana kula da mu, me ya sa ya ƙyale mugunta da wahala har yanzu? Ta yaya zan iya kyautata rayuwar iyali na?’ Littafi Mai Tsarki ya ba da tabbattun amsoshi masu gamsarwa ga waɗannan tambayoyin da kuma wasu masu yawa.

Amma, yawancin mutane a yau ba sa son karanta Littafi Mai Tsarki. Suna yi masa kallon littafi mai yawa kuma mai wuyan fahimta a wasu lokatai. Za ka so a taimaka maka ka sami amsoshi a cikin Littafi Mai Tsarki? Shaidun Jehobah suna ba da abubuwa guda biyu da za su taimake ka.

Na farko, an tsara littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? don a taimaka wa mutanen da ba su da lokaci su bincika yadda Littafi Mai Tsarki ya amsa tambayoyi masu muhimmanci. Na biyu kuma shi ne tsarin yin nazarin Littafi Mai Tsarki na gida kyauta. Ba tare da ka biya ko sisi ba, ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah wanda ya ƙware wajen koyar da Littafi Mai Tsarki kuma yana zaune a unguwarku, zai iya zuwa gidanka ko kuwa wani waje dabam da kake so a kowane mako don ya ɗan tattauna Littafi Mai Tsarki da kai. Miliyoyin mutane a dukan duniya sun amfana daga wannan tsarin. Yawancinsu sun ce: “Na sami gaskiya!”

Babu wani abu mai kyau da ya wuce wannan. Gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki ta ’yanta mu daga camfi, ruɗuwa, da kuma mugun jin tsoro. Ta ba mu bege, manufa, da kuma farin ciki. Yesu ya ce: “Ku a san gaskiya kuma, gaskiya kuwa za ta yantadda ku.”—Yohanna 8:32.

1. Mutum yana koyon abin da Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa; 2. Mace tana koyon abin da Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa