BABI NA 5
Yadda Za Mu Ware Kanmu Daga Duniya
“Ku ba na duniya ba ne.”—YOHANNA 15:19.
1. Menene Yesu ya nanata a darensa na ƙarshe a duniya?
A DARENSA na ƙarshe a duniya, Yesu ya nuna damuwa ƙwarai domin rayuwa ta nan gaba na mabiyansa. Har ya yi addu’a ga Ubansa game da batun, yana cewa: “Ba na yin addu’a ka ɗauke su daga cikin duniya ba, amma domin ka tsare su daga Mugun. Ba na duniya su ke ba, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.” (Yohanna 17:15, 16) A wannan roƙon da ya yi, Yesu ya nuna ƙaunarsa mai zurfi ga mabiyansa da kuma muhimmancin kalmominsa da ya furta da farko ga wasunsu: “Ku ba na duniya ba ne.” (Yohanna 15:19) A bayyane yake cewa Yesu yana son mabiyansa su ware kansu daga duniya!
2. Mecece “duniya” da Yesu ya yi magana a kai?
2 “Duniya” da Yesu ya ambata tana nufin dukan mutane da suke bare daga Allah, da Shaiɗan yake mallakarsu, da suke zama bayi ga fahariya da son kai da suka fito daga wurinsa. (Yohanna 14:30; Afisawa 2:2; 1 Yohanna 5:19) Babu shakka, ‘abuta da wannan duniya magabtaka ce da Allah.’ (Yaƙub 4:4) Ta yaya, dukan waɗanda suke so su tsare kansu cikin ƙaunar Allah za su kasance a duniya kuma su ware kansu daga gare ta? Za mu tattauna hanyoyi biyar: ta wajen kasancewa da aminci ga Mulkin Allah a ƙarƙashin Kristi da kuma kasance babu ruwanmu da siyasar duniya, da tsayayya wa ruhun wannan duniyar, da kasance da filako wajen adonmu, sauƙaƙe salon rayuwarmu, da kuma ɗauka makamai na ruhaniya.
KASANCEWA DA AMINCI DA KUMA BABU RUWANMU DA SIYASA
3. (a) Yaya Yesu ya ɗauki siyasa ta zamaninsa? (b) Me ya sa za a ce mabiyan Yesu da aka naɗa sun kasance manzanni? (Ka haɗa da hasiya.)
3 Maimakon ya saka hannu cikin siyasar zamaninsa, Yesu ya mai da hankali a kan wa’azi game da Mulkin Allah, gwamnati ta samaniya da za ta zo a nan gaba wanda shi ne zai zama Sarkinsa. (Daniel 7:13, 14; Luka 4:43; 17:20, 21) Saboda haka, sa’ad da yake gaban Gwamna Bilatus Babunti, Yesu ya ce: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne.” (Yohanna 18:36) Mabiyansa masu aminci sun bi misalinsa ta wajen ba da amincinsu ga Kristi da kuma Mulkinsa ta wajen sanar da wannan Mulkin ga duniya. (Matta 24:14) Manzo Bulus ya rubuta: “Mu fa manzanni ne madadin Kristi, . . . muna roƙonku madadin Kristi, ku sulhuntu ga Allah.” *—2 Korintiyawa 5:20.
4. Ta yaya dukan Kiristoci suka nuna amincinsu ga Mulkin Allah? (Dubi akwati a shafi na 52.)
4 Domin manzanni ko jakadai suna wakiltar wata ƙasa, ba sa saka hannu a cikin ayyukan ƙasar da suke hidima a ciki. Amma manzanni suna taimaka wa ƙasar da suke wakilta. Haka yake da mabiyan Kristi shafaffu, waɗanda ‘’yangarancinsu cikin sama ya ke.’ (Filibbiyawa 3:20) Domin wa’azin Mulki da suke yi da himma, sun taimaki miliyoyin “waɗansu tumaki” na Yesu su “sulhuntu ga Allah.” (Yohanna 10:16; Matta 25:31-40) Waɗannan na baya sun kasance ’yan aikan Kristi, waɗanda suke taimakon shafaffu ’yan’uwan Yesu. Domin masu shelar Mulkin Almasihu suna garke ɗaya, dukan rukunin biyun sun kasance babu ruwansu da ayyukan siyasa na duniya.—Karanta Ishaya 2:2-4.
5. Ta yaya ikilisiyar Kirista ta bambanta da ta Isra’ila ta dā, kuma ta yaya wannan bambanci ya bayyana?
Matta 28:19; 1 Bitrus 2:9) Saboda haka, idan muka manne wa wata jam’iyyar siyasa, hakan zai shafi damarmu na magana game da saƙonmu na Mulki da kuma haɗin kanmu na Kirista. (1 Korintiyawa 1:10) Bugu da ƙari, a lokacin yaƙi, za mu yaƙi ’yan’uwanmu Kiristoci, waɗanda aka umurce mu mu ƙaunace su. (Yohanna 13:34, 35; 1 Yohanna 3:10-12) Da kyakkyawar dalili Yesu ya gaya wa mabiyansa kada su yi yaƙi. Ya kuma gaya musu su ƙaunaci abokan gabansu.—Matta 5:44; 26:52; 26:52; dubi akwatin nan “ Ina Saka Hannu a Siyasa Ne?” a shafi na 55.
5 Aminci ga Kristi ba shi ba ne kawai dalilin da ya sa Kiristoci ba sa saka hannu a siyasa ba. Ba kamar Isra’ila ta dā ba da Allah ya raba mata ƙasa, mu muna cikin ’yan’uwantaka ne na dukan duniya. (6. Ta yaya keɓe kanka ga Allah ya shafi dangantakarka da Kaisar?
6 Mu Kiristoci na gaskiya mun keɓe kanmu ga Allah, ba ga wani mutum ba, ko kuma wata ƙungiyar mutane, ko ta al’umma ba. 1 Korantiyawa 6:19, 20 ta ce: “Ku kuwa ba na kanku ba ne; gama aka saye ku da tamani.” Saboda haka, sa’ad da muke ba wa “Kaisar” abin da ke na shi, wato, girmamawa, haraji, da kuma biyayya da ta dace, mabiyan Yesu suna bai wa Allah, “abin da ke na Allah.” (Markus 12:17; Romawa 13:1-7) Wannan ya haɗa da bautarsu, ƙaunar su a gare shi, da kuma biyayyarsu cikin aminci. Idan ma ya zama dole, suna shirye su ba da ransu ga Allah.—Luka 4:8; 10:27; karanta Ayukan Manzanni 5:29; Romawa 14:8.
TSAYAYYA WA “RUHUN DUNIYA”
7, 8. Menene “ruhun duniya,” kuma ta yaya yake ‘aikatawa’ a cikin mutane?
7 Wata hanya kuma da Kiristoci suke ware kansu daga 1 Korintiyawa 2:12) Ya gaya wa Afisawa, kun taɓa “tafiya a dā bisa ga . . . wannan duniya, ƙarƙashin sarkin ikon sararin sama, ruhun da ke aikawa yanzu a cikin ’ya’yan kangara.”—Afisawa 2:2, 3.
duniya ita ce ta wajen tsayayya wa mugun ruhunta. Bulus ya rubuta: “Ba ruhun duniya muka karɓa ba, amma ruhun da ke daga wurin Allah.” (8 Kalmar nan “ruhu” tana nufin abu ne da ba a gani da ke zuga mutane su yi rashin biyayya ga Allah kuma yana ta da “kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu.” (1 Yohanna 2:16; 1 Timothawus 6:9, 10) “Ikon” wannan ruhu ya dangana ne ga yadda yake ba da sha’awa ga jiki, kissa, nacewarsa, kuma kamar iska, yana mamayewa. Bugu da ƙari, yana ‘aikatawa’ a cikin mutum ta wajen saka masa a hankali halaye na rashin ibada, irin su son kai, fahariya, haɗama, buri, da kuma halayen neman ’yanci da tawaye. * Wato hakan yana nufin, ruhun duniya a hankali yana saka halayen Iblis a zuciyar mutane.—Yohanna 8:44; Ayukan Manzanni 13:10; 1 Yohanna 3:8, 10.
9. Ta waɗanne hanyoyi ne ruhun duniya zai shiga zuciyarmu da kuma tunaninmu?
9 Shin ruhun duniya zai iya yin jijiya ne a zuciyarmu? Hakika, yana iya yin hakan idan ba mu kula ba. (Karanta Misalai 4:23) Rinjayarsa sau da yawa da hankali ne, wataƙila ta wajen abokane da suka kasance kamar mutanen kirki ne, amma kuma ba su da ƙaunar Jehobah. (Misalai 13:20; 1 Korintiyawa 15:33) Za ka kuma iya samun ruhun duniya ta wajen karanta littattafai da ba su dace ba, hotunan batsa ko kuma dandalin ’yan ridda a Intane, nishaɗi marar kyau, da kuma wasanni na gasa, kowane cikin waɗannan da aka ambata suna gabatar da tunanin Shaiɗan ko kuma duniyarsa.
10. Ta yaya za mu tsayayya wa ruhun duniya?
1 Yohanna 4:4) Saboda haka, yana da muhimmanci mu kusaci Jehobah cikin addu’a!
10 Ta yaya za mu tsayayya wa wannan mugun ruhu na duniya kuma mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah? Ta wajen yin amfani da tanadi na ruhaniya sosai da Jehobah ya ba da da kuma yin addu’a a kullum domin ruhunsa mai tsarki. Ba za a gwada Jehobah da Shaiɗan ba ko kuma duniyar da take ƙarƙashin ikonsa ba. (KASANCEWA DA FILAKO A ADONMU
11. Ta yaya ruhun duniya yake rinjayar mizanin ado?
11 Abin da zai nuna a zahiri irin ruhun da yake rinjayar mutum shi ne adonsa da kuma tsabtarsa. A ƙasashe da yawa, mizanin ado ya zube har wani kalamai a talabijin ya ce ba da daɗewa ba ba za a ga bambancin masu yin irin wannan ado da karuwai ba. Har yara mata da ba su balaga ba sun faɗa cikin irin wannan yayi na “nuna gaɓoɓin jiki, da rashin filako,” in ji wata jarida. Wani yayi kuma shi ne a yi ado da ke nuna ruhun tawaye da kuma rashin daraja kai.
12, 13. Waɗanne mizanai ne za su ja-goranci adonmu?
12 Mu bayin Jehobah, ya kamata mu yi ado da kyau, wato, sa kaya masu tsabta, masu tsari kuma waɗanda suka dace da yanayi da ake ciki. A dukan lokaci, adonmu ya kamata ya nuna muna da “tsantseni da hankali,” waɗanda tare da “aiki nagari” suna da kyau ga kowa, mace ko namiji, da suke da “ibada.” Hakika, dalilin yin ado da kyau ba don mu jawo hankalin mutane a gare mu ba ne, amma mu ‘tsare kanmu cikin ƙaunar Allah.’ (1 Timothawus 2:9, 10; Yahuda 21) Babu shakka, muna son adonmu mafi kyau ya kasance “ɓoyayyen mutum na zuciya . . . , da ke da tamani mai-girma a gaban Allah.”—1 Bitrus 3:3, 4.
13 Ka tuna kuma cewa salon tufafinmu na iya rinjayar yadda wasu za su ɗauki bauta ta gaskiya. Kalmar Helenanci da aka fassara “tsantseni,” idan aka yi amfani da ita a fannin ɗabi’a, tana nufin ibada, daraja, da kuma girmama ra’ayin wasu. Makasudinmu shi ne mu ɗauki lamirin wasu da muhimmanci fiye da damar da muke da ita. Fiye da kome, muna so mu daraja Jehobah da kuma mutanensa kuma mu tabbatar da cewa mu bayin Allah ne, masu yin dukan abu domin “girmama Allah.”—1 Korintiyawa 4:9; 10:31; 2 Korintiyawa 6:3, 4; 7:1.
14. Game da adonmu da kuma tsabtarmu, me ya kamata mu tambayi kanmu?
14 Adonmu da tsabtarmu sun fi ma muhimmanci sa’ad da muka fita hidimar fage ko kuma muke halartar taron Kirista. Ka tambayi kanka: ‘Shin adona da kuma tsabta na yana jawo hankali a gare ni da bai dace ba? Suna kunyatar da wasu ne? Shin ina ɗaukan dama da nake da shi a wannan wurare da muhimmanci fiye da ƙwarewa don in sami gata a ikilisiya?’—Zabura 68:6; Filibbiyawa 4:5; 1 Bitrus 5:6.
15. Me ya sa Kalmar Allah ba ta ba da jerin dokoki game da ado da kuma tsabta?
15 Littafi Mai Tsarki bai ba Kiristoci jerin dokoki game da ado da kuma tsabta ba. Jehobah ba ya son ya hana mu dama da muke da ita na zaɓe da kuma amfani da tunaninmu. Maimakon haka, yana so mu zama Kiristoci da suka manyanta waɗanda suke amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki waɗanda kuma “suna da hankulansu wasassu bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.” (Ibraniyawa 5:14) Fiye da kome, yana son ƙauna ta ja-gorance mu, wato, ƙaunar Allah da ta maƙwabta. (Karanta Markus 12:30, 31) Cikin waɗannan iyaka, akwai damar yin ado iri iri. Ana ganin tabbacin haka a tufafi kyawawa, da mutanen Jehobah suke sakawa a duk inda suka taru a duniya.
SAUƘAƘA SALON RAYUWARMU
16. Ta yaya ruhun duniya ya saɓa wa koyarwar Yesu, kuma waɗanne tambayoyi za mu yi wa kanmu?
16 Ruhun duniya yana yaudara kuma ya sa miliyoyin mutane su juya ga neman kuɗi da abin duniya domin farin ciki. Amma kuma Yesu ya ce: “Ba da yalwar dukiya da mutum ya ke da ita ransa ke tsayawa ba.” (Luka 12:15) Ko da yake ba ƙarfafa rayuwa marar farin ciki yake yi ba, ko kuma rayuwar hana kai, Yesu ya koyar da cewa “waɗanda suka san talaucinsu na ruhu” da kuma waɗanda suka kasance da ‘lafiyayyen’ ido wanda ya kasance mai gaskiya, mai mai da hankali ga ruhaniya shi ne yake yin rayuwa da kuma farin ciki ta gaskiya. (Matta 5:3; 6:22, 23) Ka tambayi kanka: ‘Da gaskiya na gaskata da abin da Yesu ya koyar, ko kuma dai “uban ƙarya” yana rinjaya na? (Yohanna 8:44) Menene kalamai na, makasudi na, da kuma salon rayuwa ta suka nuna?—Luka 6:45; 21:34-36; 2 Yohanna 6.
17. Ka faɗi wasu amfani da waɗanda suka sauƙaƙa salon rayuwarsu suke samu.
17 Yesu ya ce: “Hikima ta barata bisa ga ayyukanta.” (Matta 11:19) Ka yi la’akari da wasu amfanin da waɗanda suka sauƙaƙa rayuwarsu suka samu. Suna samun wartsakewa ta gaske a hidimar Mulki. (Matta 11:29, 30) Sun rage wa kansu yawan damuwa saboda haka sun kāre kansu daga azaba ta tunani. (Karanta 1 Timothawus 6:9, 10) Da yake sun gamsu da wajibi na rayuwa, sun sami ƙarin lokaci domin iyalansu da kuma abokanansu Kiristoci. Za su yi barci mai kyau domin wannan. (Mai-Wa’azi 5:12) Suna samun farin cikin bayarwa, suna yin haka a dukan hanyar da za su iya yi. (Ayukan Manzanni 20:35) Suna “yalwata cikin bege,” kuma suna da kwanciyar hankali da gamsuwa. (Romawa 15:13; Matta 6:31, 32) Tamanin waɗannan albarkatai ba su da iyaka!
KA ƊAUKI “DUKAN MAKAMAI NA ALLAH”
18. Yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta abokin gabanmu, dabarunsa, da kuma irin kokawa da muke yi?
18 Waɗanda suka tsare kansu cikin ƙaunar Allah suna more kāriya ta ruhaniya don kada Shaiɗan wanda ba ya son Kiristoci su yi farin ciki kuma su sami rai madawwami ya hana su bauta wa Allah. (1 Bitrus 5:8) Bulus ya ce, “kokuwarmu ba da nama da jini ta ke ba, amma da mulkoki, da ikoki, da mahukuntan wannan zamani mai-duhu, da rundunai masu-ruhaniya na mugunta cikin sammai.” (Afisawa 6:12) Kalmar nan “kokuwa” ta nuna cewa faɗan da muke yi ba wanda ake jifan juna ba ne a ɓoye, amma na gaba da gaba ne. Ƙari ga haka, kalmomin nan “mulkoki,” “ikoki,” “mahukunta wannan zamani” sun nuna cewa farmaki daga ruhohi ne masu tsari kuma da gangan.
19. Ka kwatanta kayan yaƙin Kiristoci na ruhaniya.
19 Duk da raunanarmu na ’yan adam da kasawarsu, za mu iya samun nasara. Ta yaya? Ta wajen ɗaukan “dukan makamai na Allah.” (Afisawa 6:13) Da yake kwatanta waɗannan makamai, Afisawa 6:14-18 ya ce: “Ku tsaya fa, kun rigaya kun ɗaure gindinku da gaskiya, kun yafa sulke na adalci, kun ɗaura ma sawayenku shirin bishara ta salama; musamman kuma, ku ɗauki garkuwa ta bangaskiya, wadda za ku iya ɓice dukan jefejefe masu-wuta na Mugun da ita. Ku ɗauki kwalkwali na ceto kuma, da takobin Ruhu, watau maganar Allah: kuna addu’a kowane loto cikin Ruhu.”—Afisawa 6:14-18.
20. Ta yaya yanayinmu ya bambanta da na soja na zahiri?
20 Tun da tanadi ne na Allah, waɗannan kayan yaƙi na ruhaniya za su kāre mu, idan muna sanye da su a kowane lokaci. Ba kamar sojoji na zahiri ba, waɗanda wani lokaci za su jima ba tare da sun yi yaƙi ba, Kiristoci suna yaƙi wanda ba zai ƙare ba har sai Allah ya halaka duniyar Shaiɗan ya kuma ɗaure dukan miyagun ruhohi. (Ru’ya ta Yohanna 12:17; 20:1-3) Kada ka kasala idan kana kokawa da wani raunana ko kuma wata muguwar sha’awa, domin dole ne dukanmu mu “dandaƙi” kanmu domin mu kasance da aminci ga Jehobah. (1 Korintiyawa 9:27) Hakika, sa’ad da ba ma kokawa ne ya kamata mu damu!
21. Ta wace hanya ce kawai za mu iya yin nasara a wannan yaƙi na ruhaniya?
21 Bugu da ƙari, ba za mu iya cin nasara a wannan yaƙin da ƙarfinmu ba. Saboda haka, Bulus ya tuna mana mu yi Filimon 2; Ibraniyawa 10:24, 25) Waɗanda suka kasance da aminci a dukan waɗannan wurare za su yi nasara kuma su kāre bangaskiyarsu da kyau sa’ad da aka ƙalubalance ta.
“addu’a kowane loto cikin ruhu.” Kuma ya kamata mu saurari Jehobah ta wajen nazarin Kalmarsa da kuma hulɗa da ’yan’uwa “sojoji” a dukan wani zarafi da muka samu, domin ba mu kaɗai ba ne muke wannan kokawa ba! (KA KASANCE A SHIRYE KA KĀRE BANGASKIYARKA
22, 23. (a) Me ya sa za mu kasance a shirye a kowane lokaci mu kāre bangaskiyarmu, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu yi wa kanmu? (b) Menene za a tattauna a babi na gaba?
22 Yesu ya ce: “Domin ku ba na duniya ba ne, . . . duniya tana ƙinku.” (Yohanna 15:19) Saboda haka, dole ne Kiristoci ko da yaushe su kasance a shirye su kāre bangaskiyarsu kuma su yi haka a hanya mai daraja, mai tawali’u. (Karanta 1 Bitrus 3:15) Ka tambayi kanka: ‘Na fahimci kuwa abin da ya sa Shaidun Jehobah a wani lokaci suke kasancewa da ra’ayin da yawancin mutane ba sa so? Sa’ad da aka ƙalubalance ni game da wannan, da gaske na tabbata cewa abin da Littafi Mai Tsarki da kuma bawan nan mai aminci ya faɗa gaskiya ne? (Matta 24:45; Yohanna 17:17) Sa’ad da ya zo ga yin abin da ke daidai a gaban Jehobah, ina shirye kuwa in kasance dabam kuma ina alfaharin yin haka?’—Zabura 34:2; Matta 10:32, 33.
23 Amma, sau da yawa, ana gwada muradinmu na kasancewa a ware daga duniya a cikin dabara. Alal misali, kamar yadda aka ambata a baya, Shaiɗan yana ƙoƙari ya rinjayi bayin Jehobah su bi duniya ta wurin nishaɗi irin na duniya. Ta yaya za mu zaɓi nishaɗi mai kyau da zai wartsake mu kuma mu kasance da lamiri mai kyau? Za a tattauna wannan batun a babi na gaba.
^ sakin layi na 3 Tun daga Fentikos na shekara ta 33 A.Z., Kristi ya kasance Sarki bisa ikilisiyar mabiyansa naɗaɗɗu a duniya. (Kolossiyawa 1:13) A shekara ta 1914, Yesu ya karɓi ikon sarauta bisa “Mulkin duniya.” Saboda haka, Kiristoci shafaffu sun kasance manzannin Mulkin Almasihu.—Ru’ya ta Yohanna 11:15.
^ sakin layi na 8 Dubi Reasoning From the Scriptures, shafuffuka na 389-393, Shaidun Jehobah ne suka buga.
^ sakin layi na 65 Dubi Rataye, shafuffuka na 212-215.