Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 3

Ka Kaunaci Wadanda Allah Yake Kauna

Ka Kaunaci Wadanda Allah Yake Kauna

“Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima.”—MISALAI 13:20.

1-3. (a) Wace gaskiya ce Littafi Mai Tsarki ya faɗa? (b) Ta yaya za mu zaɓi abokan da za su rinjaye mu a hanya mai kyau?

MUTANE kamar soso suke a wata hali, suna tsotse dukan wani abin da ke inda suke. Ba shi da wuya mu koyi halaye, mizanai, da kuma mutumtakar waɗanda muke cuɗanya da su, ba da sanin mu ba.

2 Littafi Mai Tsarki ya faɗi gaskiya sa’ad da ya ce: “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima: Amma abokin tafiyar wawaye za ya ciwutu dominsa.” (Misalai 13:20) Wannan karin maganar ba akan saduwa da mutane kawai yake magana ba. Furcin nan “ka yi tafiya” yana nufin yin tarayya na kud da kud. * Da yake bayani a kan wannan ayar, wani littafin bincike na Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yin tafiya da mutum tana nufin ƙauna da kuma shaƙuwa.” Ba za ka yarda ba ne cewa muna yawan kwaikwayon waɗanda muke ƙauna? Hakika, domin mun shaƙu da waɗanda muke ƙauna, za su iya mulmula mu a hanya mai kyau ko marar kyau.

3 Domin mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah, yana da muhimmanci mu nemi abokan da za su rinjaye mu a hanya mai kyau. Ta yaya za mu yi haka? A taƙaice, ta wajen ƙaunar waɗanda Allah yake ƙauna, da kuma mai  da abokansa abokanmu. Ka yi tunani a kan wannan. Waɗanne abokai ne za mu zaɓa da za su fi waɗanda suke da halayen da Jehobah yake so? Saboda haka, bari mu bincika mu ga irin mutanen da Allah yake ƙauna. Da ra’ayin Jehobah a zukatanmu, za mu kasance a shirye mu zaɓi abokan kirki.

WAƊANDA ALLAH YAKE ƘAUNA

4. Me ya sa Jehobah yana da daman ya zaɓi abokansa, kuma me ya sa Jehobah ya kira Ibrahim “aminina”?

4 Idan ya zo ga abota, Allah yana da zaɓi. Kuma yana da damar zaɓe. Ban da haka ma, shi ne Ubangijin dukan halitta, kuma yin abota da shi gata ne da ya fi kome. To, su waye ne yake zaɓa su zama abokansa? Jehobah yana kusantar waɗanda suka dogara a gare shi kuma suka ba da gaskiya a gare shi. Ka yi la’akari da Ibrahim, shi mutum ne mai bangaskiya sosai. Babu gwaji na bangaskiya da za a yi wa mahaifi da zai kai na gaya masa ya yi hadaya da ɗansa. * Duk da haka, Ibrahim “ya miƙa Ishaku” domin yana da cikakken bangaskiya cewa “Allah yana da iko ya tada mutum, ko daga matattu.” (Ibraniyawa 11:17-19) Domin Ibrahim ya nuna irin wannan bangaskiyar da kuma biyayya, Jehobah ya kira shi “aminina.”—Ishaya 41:8; Yaƙub 2:21-23.

5. Yaya Jehobah yake ɗaukan waɗanda suke yi masa biyayya cikin aminci?

5 Jehobah yana ɗaukan biyayya ta aminci da muhimmanci. Yana ƙaunar waɗanda suka nuna amincinsu a gare shi fiye da dukan wani abu. (Karanta 2 Samuila 22:26) Kamar yadda muka gani a Babi na 1 na wannan littafin,  Yesu yana farin ciki da waɗanda suka yi masa biyayya domin suna ƙaunarsa. “Asirinsa yana tare da masu-adalci,” in ji Misalai 3:32. Waɗanda suke cika bukatun Allah da aminci suna samun gayyata mai kyau daga wajen Jehobah, wato: Suna iya sauka cikin ‘tantinsa,’ su bauta masa kuma su yi addu’a ga Allah a kowane lokaci.—Zabura 15:1-5.

6. Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Yesu, kuma yaya Jehobah yake ji game da waɗanda suke ƙaunar Ɗansa?

6 Jehobah yana ƙaunar waɗanda suke ƙaunar Ɗansa makaɗaici, Yesu. Yesu ya ce: “Idan mutum yana ƙaunata, za shi kiyaye maganata; Ubana kuwa za ya ƙaunace shi, mu zo wurinsa, mu yi zamanmu tare da shi.” (Yohanna 14:23) Ta yaya za mu nuna ƙaunarmu ga Yesu? Hakika, ta wajen kiyaye dokokinsa, wannan ya haɗa da umurnin da ya ba mu na yin wa’azin bishara da kuma almajirantarwa. (Matta 28:19, 20; Yohanna 14:15, 21) Muna kuma nuna ƙauna ga Yesu sa’ad da muka “bi sawunsa,” ta wajen yin koyi da kalmominsa da kuma ayyukansa daidai yadda mu ajizai za mu iya. (1 Bitrus 2:21) Jehobah yana yin farin ciki domin ƙoƙarin waɗanda ƙaunarsu ga Ɗansa tana motsa su su bi tafarkin Kristi.

7. Me ya sa hikima ce mu yi abota da abokan Jehobah?

7 Bangaskiya, aminci, biyayya, da kuma ƙauna ga Yesu da hanyoyinsa, suna cikin halayen da Jehobah yake bukata daga abokansa. Ya kamata kowannenmu ya tambayi kansa: ‘Abokai na na kud da kud suna da irin waɗannan halayen kuwa? Ina abota da abokan Jehobah kuwa?’ Yana da kyau mu yi hakan. Mutane da suka koyi waɗannan halaye kuma suka yi wa’azin bishara da ƙwazo za su iya rinjayarmu a hanya mai kyau, kuma za su rinjaye mu mu ƙuduri aniyar faranta wa Allah rai.—Dubi akwatin nan “ Wenene Abokin Kirki?” da ke shafi na 29.

 KOYA DAGA MISALIN DA KE LITTAFI MAI TSARKI

8. Menene ya burge ka game da dangantar da ke tsakanin (a) Na’omi da Ruth? (b) Matasa uku Ibraniyawa? (c) Bulus da Timothawus?

8 Nassosi suna ɗauke da misalan waɗanda suka amfana domin sun zaɓi abokan kirki. Za ka iya karanta dangantakar da ke tsakanin Na’omi da surkuwarta Ruth, tsakanin matasa uku Ibraniyawa waɗanda suka manne wa Jehobah a ƙasar Babila, da kuma tsakanin Bulus da Timothawus. (Ruth 1:16; Daniel 3:17, 18; 1 Korintiyawa 4:17; Filibiyawa 2:20-22) Amma, bari mu mai da hankali ga wani misalin da ya yi fice: abota da ke tsakanin Dauda da Jonathan.

9, 10. Menene ainihin dalilin da ya sa Dauda da Jonathan suka zama abokai?

9 Littafi Mai Tsarki ya ce bayan da Dauda ya kashe Goliath, “Sai ran Jonathan ya saje da ran Dauda, Jonathan kuma ya ƙaunace shi kamar ransa.” (1 Samuila 18:1) Wannan shi ne mafarin abota na kud da kud da ko da yake da bambancin shekaru, ta ci gaba har mutuwar Jonathan a bakin daga. * (2 Samuila 1:26) Menene ainihin tushen wannan abota da waɗannan mutane biyu suka ƙulla?

10 Ƙaunar Allah ce ta ɗaure Dauda da Jonathan tare, da kuma muradinsu mai ƙarfi na kasancewa da aminci a gare shi. Waɗannan mutanen biyu sun kasance masu ruhaniya. Kowannensu ya nuna halayen da ya sa ɗayan yake ƙaunarsa. Babu shakka, gaba gaɗi da ƙwazon wannan saurayin da ya kāre sunan Jehobah babu tsoro ya burge Jonathan. Dauda babu shakka ya daraja wannan tsohon da ya kasance da aminci ga tsarin Jehobah, kuma ba tare da son  kai ba ya saka bukatun Dauda a gaba da nasa. Ka yi la’akari da abin da ya faru sa’ad da Dauda ya yi sanyin gwiwa a rayuwarsa, yana zaune a daji don ya guje wa fushin da mugun Sarki Saul, uban Jonathan yake yi da shi. Ta wajen nuna zurfin amincinsa, Jonathan ya “tafi wurin Dauda cikin kurmin, ya ƙarfafa hannunsa cikin Allah.” (1 Samuila 23:16) Ka yi tunanin yadda Dauda ya ji sa’ad da  abokinsa abin ƙaunarsa ya zo ya tallafa masa kuma ya ƙarfafa shi! *

11. Menene ka koya game da abokantaka daga misalin Jonathan da Dauda?

11 Menene muka koya daga misalin Jonathan da Dauda? Fiye da dukan wani abu, mun ga cewa abu mafi muhimmanci da ya kamata abokai su kasance da shi a tsakaninsu shi ne, mizanai na ruhaniya. Sa’ad da muka kusaci  waɗanda suke da irin imaninmu, irin mizanan ɗabi’armu, da kuma muradinmu na kasancewa da aminci ga Allah, za mu iya ƙarfafa juna kuma mu gina juna. (Karanta Romawa 1:11, 12) Muna samun irin waɗannan abokane da suke da ruhaniya a tsakanin ’yan’uwanmu da muke bauta tare. Wannan yana nufin cewa dukan wanda yake zuwa taro a Majami’ar Mulki ne zai kasance abokin kirki? Ba dole ba ne.

ZAƁAN ABOKANMU NA KUD DA KUD

12, 13. (a) Me ya sa har a tsakanin ’yan’uwanmu Kiristoci ma dole ne mu zaɓi abokananmu? (b) Wane ƙalubale ne Kiristoci na ƙarni na farko suka fuskanta, kuma wane gargaɗi ne Bulus ya bayar?

12 Har a cikin ikilisiya ma, dole ne mu yi zaɓe idan muna son abokanmu su kasance masu ƙarfafawa a ruhaniya. Ya kamata hakan ya ba mu mamaki ne? A’a. Yakan ɗauki wasu Kiristoci a ikilisiya dogon lokaci kafin su manyanta a ruhaniya, kamar yadda yakan ɗauki wasu ’ya’yan itace lokaci kafin su ƙosa. Saboda haka, a kowace ikilisiya, muna samun Kiristocin da suka bambanta a manyantarsu ta ruhaniya. (Ibraniyawa 5:12–6:3) Hakika, muna haƙuri kuma mu nuna ƙauna ga sababbi da kuma waɗanda suka raunana, domin muna so mu taimake su su girma a ruhaniya.—Romawa 14:1; 15:1.

13 Jifa jifa, yanayi a ikilisiya zai bukaci mu mai da hankali da abokanmu. Wasu za su yi halayen da ba daidai ba. Wasu za su zama masu ƙiyayya ko kuma masu sūka. Ikilisiyoyi ma a ƙarni na farko A.Z. sun fuskanci irin wannan ƙalubalen. Sa’ad da yawanci suke da aminci, wasu mutane sun ƙi su nuna halayen kirki. Domin wasu cikin ikilisiyar Koranti sun ƙi bin wasu koyarwar Kiristoci, manzo Bulus ya yi wa ikilisiyar gargaɗi: “Kada ku yaudaru: zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.” (1 Korintiyawa 15:12, 33) Bulus ya gargaɗi Timothawus cewa har a tsakanin  Kiristoci ma, da waɗanda ba su da halin kirki. Ya gaya wa Timothawus ya guji waɗannan kada ya mai da su abokanansa na kud da kud.—Karanta 2 Timotawus 2:20-22.

14. Ta yaya za mu yi amfani da mizanin da ke gargaɗin da Bulus ya bayar game da abokantaka?

14 Ta yaya za mu yi amfani da mizanin da ke cikin gargaɗin da Bulus ya bayar? Ta wajen guje wa abota da kowane mutum a ciki da wajen ikilisiya, da zai iya rinjayarmu mu bi muguwar hanya. (2 Tassalunikawa 3:6, 7, 14) Dole ne mu kāre ruhaniyarmu. Ka tuna cewa kamar soso, muna tsotse halaye da kuma hanyoyin abokananmu. Kamar yadda ba zai yiwu mu tsoma soso cikin giya kuma mu yi tsammanin cewa zai tsotse ruwa ba, hakazalika, ba zai yiwu mu yi abota da waɗanda za su rinjaye mu a muguwar hanya kuma mu yi tsammanin cewa za mu koyi abin da yake da kyau ba.—1 Korintiyawa 5:6.

Kana iya samun abokan kirki tsakanin ’yan’uwanmu da muke bauta tare

15. Menene za ka yi domin ka sami abokai da suke mai da hankali ga ruhaniya a ikilisiya?

15 Abin godiya ne cewa za mu iya samun abokan kirki da yawa a tsakanin ’yan’uwanmu da muke bauta tare. (Zabura 133:1) Ta yaya za ka iya samun abokai masu mai da hankali ga ruhaniya a cikin ikilisiya? Sa’ad da ka koyi halaye na ibada, waɗanda suke da irin waɗannan halayen za su kusace ka. Haka nan kuma, wataƙila kana bukatar ka ɗauki wasu matakai domin ka nemi sababbin abokai. (Dubi akwatin nan “ Yadda Za Mu Sami Abokan Kirki,” a shafi na 30.) Ka nemi waɗanda suke da halayen da kake son ka koya. Ka bi shawarar Littafi Mai Tsarki da ya ce, “ku buɗe zuciyarku,” ka nemi abota da ’yan’uwa masu bi ba tare da nuna bambancin launin fata, ko ƙasa, ko al’ada ba. (2 Korintiyawa 6:13; karanta 1 Bitrus 2:17.) Kada ka yi abota da tsaranka kawai. Ka tuna cewa Jonathan ya girmi Dauda sosai. Tsofaffi da yawa za su kawo hikima da sani ga abokantaka.

 SA’AD DA MATSALOLI SUKA TASO

16, 17. Me ya sa bai kamata mu janye daga ikilisiya ba, idan ɗan’uwanmu da muke bauta tare ya ba mu haushi a wata hanya?

16 Tun da yake muna da mutane masu halaye dabam dabam kuma waɗanda suka fito daga wurare dabam dabam a cikin ikilisiya, matsala tana iya tasowa lokaci lokaci. Ɗan’uwa mai bi zai iya yin wani abu ko kuma ya faɗi wani abin da zai ba mu haushi. (Misalai 12:18) Wani lokaci matsala tana ƙaruwa domin bambancin mutumtaka, rashin fahimta, ko kuma bambancin ra’ayi. Ya kamata waɗannan ƙalubalen su sa mu yi tuntuɓe ne kuma mu bar ikilisiya? Idan muna ƙaunar Jehobah da gaske da kuma waɗanda yake ƙauna, ba za mu yi hakan ba.

17 Da yake shi ne Mahaliccinmu kuma Mai Raya mu,  Jehobah ya cancanci mu ƙaunace shi kuma mu bauta masa. (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Ƙari ga haka, ikilisiyar da yake amfani da ita ta cancanci mu tallafi mata cikin aminci. (Ibraniyawa 13:17) Saboda haka, idan ɗan’uwanmu mai bi ya ba mu haushi a wata hanya, ba za mu janye kanmu daga ikilisiya ba domin mu nuna rashin jin daɗinmu. Me ma zai sa mu yi haka? Ba Jehobah ba ne ya yi mana laifi. Ƙaunar da muke yi masa ba za ta taɓa barinmu mu juya wa shi da mutanensa baya ba!—Karanta Zabura 119:165.

18. (a) Menene za mu iya yi domin mu ci gaba da samun zaman lafiya a ikilisiya? (b) Gafartawa sa’ad da da dalilin yin haka tana kawo wace albarka?

18 Ƙaunarmu ga ’yan’uwanmu da muke bauta tare tana motsa mu mu yi zaman lafiya a cikin ikilisiya. Jehobah ba ya neman kamilta daga waɗanda yake ƙauna, ya kamata mu ma mu kasance haka. Ƙauna tana sa mu ƙyale ƙananan laifuffuka, domin dukanmu ajizai ne kuma muna yin kurakurai. (Misalai 17:9; 1 Bitrus 4:8) Ƙauna tana sa mu ci gaba da “gafarta ma juna.” (Kolossiyawa 3:13) Ba ko yaushe ba ne bin wannan shawarar yake da sauƙi ba. Idan muka ƙyale fushi ya sha kanmu, za mu iya ci gaba da nuna ƙiyayya, wataƙila ta wajen soma tunanin cewa fushinmu yana horar da wanda ya yi mana laifi. Amma gaskiyar ita ce, ci gaba da yin fushi yana cutar da mu ne. Gafartawa sa’ad da muke da dalilin yin haka tana kawo albarka. (Luka 17:3, 4) Tana ba mu kwanciyar hankali, tana kawo zaman lafiya cikin ikilisiya, fiye kuma da kome, tana kāre dangantakarmu da Jehobah.—Matta 6:14, 15; Romawa 14:19.

SA’AD DA YA KAMATA A JANYE ABOTA

19. Wane yanayi ne zai taso da zai sa mu janye abotarmu da wani?

19 A wani lokaci, za a aririce mu mu janye abotarmu da wani da a dā yana cikin ikilisiya. Irin wannan yanayi yana tasowa ne sa’ad da aka yi wa wani da ya ci gaba da ƙeta dokar  Allah ba tare da ya tuba ba yankan zumunci ko kuma wanda ya ƙi bangaskiya ta wajen koyar da koyarwar ƙarya ko kuma ta wajen daina tarayya da ikilisiya. Kalmar Allah kai tsaye ta gaya mana ‘kada mu yi cuɗanya’ da irin waɗannan mutanen. * (Karanta 1 Korintiyawa 5:11-13; 2 Yohanna 9-11) Zai kasance ƙalubale ne ƙwarai mu guji mutumin da wataƙila abokinmu ne a dā ko kuma danginmu ne. Za mu muna matsayinmu ne ta wajen nuna cewa mun saka aminci ga Jehobah gaba da kome? Ka tuna cewa Jehobah yana ɗaukan aminci da biyayya da muhimmanci.

20, 21. (a) Me ya sa tsarin yankan zumunci tsari ne na ƙauna? (b) Me ya sa yake da muhimmanci mu zaɓi abokanmu cikin hikima?

20 Tsarin yankan zumunci tsari ne na ƙauna daga Jehobah. Ta yaya? Ƙorar mai zunubi da ya ƙi tuba nuna ƙauna ne ga sunan Jehobah mai tsarki da kuma matsayinsa. (1 Bitrus 1:15, 16) Yankan zumunci yana kāre lafiyar ikilisiya. Ana kāre ’ya’yanta masu aminci daga mummunar rinjaya ta masu zunubi da gangan kuma za su ci gaba da bautarsu da sanin cewa ikilisiya mafaka ce daga wannan muguwar duniya. (1 Korintiyawa 5:7; Ibraniyawa 12:15, 16) Wannan horo mai tsanani yana nuna ƙauna ga mai laifin. Zai iya kasancewa abin da yake bukata ke nan domin ya dawo cikin hankalinsa kuma ya ɗauki matakan da suka dace domin ya koma ga Jehobah.—Ibraniyawa 12:11.

21 Ba za mu iya guje wa gaskiyar cewa abokanmu suna shafanmu ba. Saboda haka, yana da muhimmanci mu zaɓi abokanmu cikin hikima. Ta wajen mai da abokan Jehobah abokanmu, ta wajen ƙaunar waɗanda Allah yake ƙauna, za mu kewaye kanmu da abokan kirki. Abin da muka koya daga wajen su zai taimake mu mu ƙuduri aniyar faranta wa Jehobah rai.

^ sakin layi na 2 Kalmar Ibrananci da aka fassara “ka yi tafiya” tana nufin zama “aboki” da kuma yin “abuta.”—Alƙalawa 14:20; Misalai 22:24.

^ sakin layi na 4 Ta wajen gaya wa Ibrahim ya yi wannan, Jehobah ya ba da alamar hadayar da shi da kansa zai yi ta wajen ba da Ɗansa. (Yohanna 3:16) Ga Ibrahim, Allah ya hana shi kuma ya ba shi rago a madadin Ishaƙu.—Farawa 22:1, 2, 9-13.

^ sakin layi na 9 Dauda matashi ne, ‘saurayi,’ sa’ad da ya kashe Goliath, kuma ya kai kusan shekara 30 a lokacin da Jonathan ya mutu. (1 Samuila 17:33; 31:2; 2 Samuila 5:4) Jonathan, wanda yake kusan ɗan shekara 60 sa’ad da ya mutu, ya girmi Dauda da kusan shekara 30.

^ sakin layi na 10 Kamar yadda yake rubuce a 1 Samuila 23:17, Jonathan ya faɗi abubuwa biyar don ya ƙarfafa Dauda: (1) Ya aririci Dauda kada ya ji tsoro. (2) Ya tabbatar wa Dauda cewa ƙoƙarce-ƙoƙarcen Saul ba za su yi nasara ba. (3) Ya tuna wa Dauda cewa zai sami sarauta kamar yadda Allah ya yi alkawari. (4) Ya yi alkawari cewa zai kasance da aminci ga Dauda. (5) Ya gaya wa Dauda cewa Saul ma ya san cewa Jonathan yana da aminci ga Dauda.

^ sakin layi na 19 Domin ƙarin bayani game da yadda za mu bi da waɗanda aka yi wa yankan zumunci ko kuma waɗanda suka ware kansu, dubi Rataye, shafuffuka na 207-209.