Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 12

Ku Fadi “Abin da ke Mai Kyau Garin Ginawa”

Ku Fadi “Abin da ke Mai Kyau Garin Ginawa”

“Kada kowanne ruɓaɓen zance shi fita daga cikin bakinku, sai irin abin da ke mai-kyau garin ginawa.”—AFISAWA 4:29.

1-3. (a) Wace kyauta ce Jehobah ya ba mu, kuma ta yaya za a iya wulakanta ta? (b) Domin mu kasance cikin ƙaunar Allah, ta yaya muke bukatar mu yi amfani da kyautar magana?

IDAN ka ba wanda kake ƙauna kyauta amma kuma da gangan ya wulakanta kyautar, ya za ka ji? A ce ka ba shi mota, daga baya ka sami labari cewa yana tuƙin hauka har ya ji wa wasu mutane ciwo. Za ka ji daɗi?

2 Iya magana da za a fahimta kyauta ce daga Jehobah Allah, Mai bayar da “kowace cikakkiyar kyauta.” (Yaƙub 1:17) Wannan kyautar da ta bambanta ’yan adam daga dabba, tana ba mu damar faɗin tunaninmu da kuma yadda muke ji ga wasu. Amma kamar mota ana iya wulakanta wannan kyautar magana. Jehobah ba zai ji daɗi ba idan muka yi magana babu tsari muna cutar da wasu.

3 Domin mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah, muna bukatar mu yi amfani da kyautar magana yadda Mai bayarwa yake so. Jehobah ya bayyana dala-dala irin maganar da take faranta masa rai. Kalmarsa ta ce: “Kada kowanne ruɓaɓen zance shi fita daga cikin bakinku, sai irin abin da ke mai-kyau garin ginawa yayinda a ke bukata, domin shi bada alheri ga waɗanda su ke ji.” (Afisawa 4:29) Bari mu tattauna abin da ya sa ya kamata mu  mai da hankali wajen magana, irin maganar da ya kamata mu guje wa, da kuma yadda za mu furta magana “mai-kyau garin ginawa.”

DALILIN DA YA SA ZA MU KULA DA YADDA MUKE MAGANA

4, 5. Ta yaya wasu Misalai na Littafi Mai Tsarki suka kwatanta ƙarfin da kalmomi suke da su?

4 Wani dalili mai muhimmanci na kula da yadda muke magana shi ne cewa kalmomi suna da ƙarfi. Misalai 15:4 ya ce: “Harshe mai-lafiya itacen rai ne: Amma shiririta a ciki karyewar ruhu ne.” * Kamar yadda ruwa yake farfaɗo da itacen da ya bushe, haka ma magana mai daɗi tana iya wartsake waɗanda suke sauraronta. Akasin haka, baƙar magana tana iya wulakanta masu jin ta. Hakika, kalmominmu suna da ƙarfin cutarwa ko kuma warkarwa.—Misalai 18:21.

5 Da yake kwatanta ikon abin da muke furtawa, wani karin magana ya ce: “Akwai wanda ya kan yi magana da garaje kamar sussukan takobi.” (Misalai 12:18) Yin magana  da garaje tana iya cutarwa ƙwarai kuma ta ɓata dangantaka. An taɓa huɗa maka zuciya da kalma mai kama da takobi? Wannan karin magana kuma ya ce: “Harshen mai-hikima lafiya ne.” Kalamai masu tsari daga mutum mai hikima ta Allah zai iya warkar da zuciya mai ciwo kuma ya gyara dangantaka. Za ka iya tuna lokacin da ka ji kalmomi masu warkarwa? (Karanta Misalai 16:24) Da yake mun fahimci cewa kalmomi suna da iko, muna so mu yi amfani da kalamanmu mu warkar, ba don mu cuci wasu ba.

Maganar kirki tana wartsakarwa

6. Me ya sa kokawa ce sosai mu kame harshenmu?

6 Ko yaya ƙoƙarinmu ba za mu iya kame harshenmu gaba ɗaya ba. Wannan shi ne dalili na biyu da ya sa ya kamata mu kula da kalamanmu: Zunubi da ajizanci suna sa mu yi baƙaƙen maganganu. Kalamai daga zuciya suke fitowa, kuma “tunanin zuciyar mutum mugunta ne.” (Farawa 8:21; Luka 6:45) Yi wa harshenmu linzami baban aiki ne. (Karanta Yaƙub 3:2-4) Ko da yake ba zai yiwu mu kame harshenmu gabaki ɗaya ba, za mu iya ci gaba da aiki don mu kyautata yadda muke amfani da shi. Kamar yadda mai iyo da yake fuskantar taguwar ruwa zai ci gaba da ƙoƙari, haka kuma dole mu ci gaba da kokawa da ajizancinmu da ke sa mu yi maganganu marasa kyau.

7, 8. Ta yaya za mu ba Jehobah lissafi a kan kalaman da muke furtawa?

7 Dalili na uku da ya sa ya kamata mu kula da kalamanmu shi ne cewa za mu ba da lissafi ga Jehobah a kan abin da muke furtawa. Yadda muka yi amfani da harshenmu zai shafi dangantakarmu da mutane da kuma matsayinmu a gaban Jehobah. Yaƙub 1:26 ta ce: “Idan kowane mutum yana aza kansa mai-addini ne, shi kuwa ba ya kame harshensa ba amma yana yaudara  zuciyatasa, addinin wannan banza ne.” * Kamar yadda muka tattauna a babi da ya gabata, furcinmu na shafan bautarmu.

8 A bayyane yake cewa muna da ƙwararen dalilai na kula da kalamanmu domin kada mu yi baƙar magana. Kafin mu yi la’akari da kalamai masu kyau domin ƙarfafawa, bari mu tattauna irin kalaman da ba su dace da rayuwar Kirista ba.

KALAMAI DA BA SU DA KYAU

9, 10. (a) Wane irin salon magana ne ya zama furci na yau da kullum? (b) Me ya sa za mu ƙi irin wannan maganganun batsa? (Dubi hasiya.)

9 Furcin batsa. Zagi, ashar, da kuma wasu maganganun batsa furci ne da ake amfani da su kowace rana a duniya ta yau. Mutane da yawa suna rantse-rantse don su nanata abin da suke faɗi ko kuma don ba su san kalamai da suka dace ba. Masu wasan ba da dariya sau da yawa suna ɗanyen magana domin su ba mutane dariya. Amma maganganun batsa, ba abin dariya ba ne. Shekaru dubu biyu da suka shige, manzo Bulus da aka hure ya gargaɗi ikilisiyar Kolosiyawa su bar yin “alfasha.” (Kolossiyawa 3:8) Bulus ya gaya wa ikilisiyar Afisawa cewa “alfasha” tana cikin abubuwa da bai kamata a “ambata a cikin” Kiristoci na gaskiya ba.—Afisawa 5:3, 4.

10 Maganar batsa tana ɓata wa Jehobah rai. Kuma tana ɓata wa waɗanda suke ƙaunarsa rai. Hakika, ƙaunarmu ga Jehobah tana motsa mu mu guji maganganun batsa. Sa’ad da yake lissafa “ayyukan jiki,” Bulus ya ambaci “ƙazanta” wanda ya haɗa da rashin tsabta wajen  magana. (Galatiyawa 5:19-21) Wannan batu ne mai tsanani. Ana iya yanke wa mutum zumunci daga ikilisiya idan ya zame masa hali ya riƙa maganganun rashin ɗabi’a mai lalatarwa kuma ya ƙi ji duk da gargaɗi da aka yi masa. *

11, 12. (a) Menene tsegumi, kuma ta yaya zai kasance da lahani? (b) Me ya sa ya kamata masu bauta wa Jehobah su guji ɓata sunan wasu?

11 Tsegumi, ɓata suna. Tsegumi yin maganar mutane ne da kuma rayuwarsu a bayansu. Kowane irin tsegumi ne bai da kyau? Babu laifi idan magana ce kawai game da abubuwa masu kyau game da wanda bai jima ba da yin baftisma ko kuma wanda yake bukatar a ƙarfafa shi. Kiristoci na ƙarni na farko sun damu da lafiyar juna kuma sun yi magana game da ’yan’uwa masu bi. (Afisawa 6:21, 22; Kolossiyawa 4:8, 9) Tsegumi zai kasance da lahani idan ba gaskiya ake faɗa ba kuma yana tona asirin wasu. Kuma mafi muni ma, yana iya kai ga ɓata suna, wanda kuma yana da lahani. Ɓata suna ‘zargin ƙarya ne . . . wanda yake ɓata mutum a idanun wasu.’ Alal misali, Farisawa suka fara ɓata sunan Yesu domin su ɓata shi a idanun wasu. (Matta 9:32-34; 12:22-24) Ɓata suna sau da yawa yana kawo saɓani.—Misalai 26:20.

12 Jehobah ba ya son waɗanda suke amfani da kyautar magana su ɓata mutane ko kuma su haɗa mutane. Ya ƙi waɗanda suke “mai-shukan annamimanci tsakanin ’yan’uwa.” (Misalai 6:16-19) Kalmar Helenanci da aka fassara ‘matsegunci’ di·aʹbo·los ce, ita ce kuma aka yi  amfani da ita wajen yi wa Shaiɗan laƙabi. Shi ne “Iblis” wanda ya yi ƙarya ya ɓata wa Allah suna. (Ru’ya ta Yohanna 12:9, 10) Hakika muna so mu guji kalaman da za su sa mu zama iblis. Babu wuri a ikilisiya domin ɓata suna da yake ta da ayyukan jiki irin su “hasala” da kuma “tsatsaguwa.” (Galatiyawa 5:19-21) Saboda haka kafin ka faɗi wani abu game da wani, ka tambayi kanka: ‘Gaskiya ne kuwa? Zai yi kyau kuwa a maimaita wannan? Dole ne ko kuma yana da kyau a faɗi wannan magana?’—Karanta 1 Tassalunikawa 4:11.

13, 14. (a) Yaya zage-zage za su shafi waɗanda suke jinsa? (b) Mecece maganar ɓatanci, kuma ta yaya mai irin wannan maganar yake sa kansa cikin haɗari?

13 Zage-zage. Kamar yadda muka fahimta, kalmomi suna da ƙarfin cutarwa. Domin ajizancinmu, dukanmu muna faɗin abin da zai sa mu yi nadama daga baya. Amma, Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi game da salon magana da ba shi da wuri a cikin gidajen Kiristoci ko kuma cikin ikilisiya. Bulus ya gargaɗi Kiristoci: “Bari dukan ɗacin zuciya, da hasala, da fushi, da hargowa, da zage-zage, su kawu daga gareku.” (Afisawa 4:31) Wasu sun fassara kalmar nan “zage-zage” cewa “muguwar magana,” ce kuma “magana mai cutarwa.” Zage-zage, ya haɗa da kiran mutum da sunan tsiya, da kuma sūka kullum, hakan za su iya zubar da mutuncin wasu ya sa su ji ba su da wani amfani. Musamman zage-zage ya fi wa yara ciwo.—Kolossiyawa 3:21.

14 Littafi Mai Tsarki ya la’anci maganar ɓatanci, wato, wulakanta wasu da kalamai ko kuma zagi. Mutumin da ya zama masa jiki ya yi irin waɗannan maganganu yana saka kansa cikin haɗari, domin ana iya cire mai zage-zage daga cikin ikilisiya idan bai canja halinsa ba bayan an yi ƙoƙari a taimake shi. Idan bai canja halinsa ba, ba zai sami albarkar Mulki ba. (1 Korintiyawa 5:11-13; 6: 9, 10) A bayyane yake cewa ba za mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah ba idan ya zama mana hali mu furta kalaman da ba su da kyau, ba su da gaskiya, kuma ba na kirki ba. Irin waɗannan suna rushewa.

KALMOMI DA SUKE “MAI-KYAU GARIN GINAWA”

15. Waɗanne irin kalamai ne ‘masu kyau domin ginawa’?

15 Ta yaya za mu yi amfani da kyautar magana kamar yadda Mai bayarwa yake so? Ka tuna cewa Kalmar Allah ta aririce mu mu faɗi “abin da ke mai-kyau garin ginawa.” (Afisawa 4:29) Jehobah yana farin ciki sa’ad da muka furta kalamai masu ginawa, da kuma ƙarfafa wasu. Furta irin waɗannan kalamai yana bukatar tunani. Littafi Mai Tsarki bai ba da dokoki da za a bi ba; kuma bai ƙunshi jerin “zancen kirki” ba. (Titus 2:8) Domin mu furta kalamai da suke “mai-kyau garin ginawa,” ya kamata mu tuna da abubuwa uku da kalamai masu ƙarfafawa suka ƙunsa; yana da kyau, gaskiya ce, kuma na kirki ne. Da waɗannan bari mu bincika wasu ’yan takamammun misalai na kalamai masu ƙarfafawa.—Dubi akwatin nan “ Kalamai na Suna Ƙarfafawa Kuwa?” a shafi na 140.

16, 17. (a) Me ya sa za mu yaba wa wasu? (b) Waɗanne zarafi ne muke da su na yaba wa wasu a ikilisiya? da kuma iyali?

16 Yabo. Jehobah da Yesu sun fahimci bukatar furta kalamai na yabo da kuma karɓuwa. (Matta 3:17; 25:19-23; Yohanna 1:47) Mu Kiristoci ma, muna bukatar mu yabi wasu. Me ya sa? Misalai 15:23 ya ce: “Magana a kan kari, ina misalin kyaunta!” Ka tambayi kanka: ‘Yaya nake ji sa’ad da aka yabe ni? Yana faranta mini rai kuma ya ƙarfafa ni?’ Hakika, kalmomin yabo suna sa ka ji wani ya lura da kai, cewa wani ya damu da kai, da kuma cewa ƙoƙarin da ka yi ba na banza ba ne. Irin wannan tabbaci  yana ƙarfafa gaba gaɗinka ya kuma motsa ka ka ƙara ƙoƙari a nan gaba. Tun da kana jin daɗi idan aka yabe ka, bai kamata ba ne ka yi iya ƙoƙarinka ka yabi wasu?—Karanta Matta 7:12.

17 Ka koyar da kanka ka nemi abin kirki da wasu suke yi, kuma ka yaba musu. A cikin ikilisiya, wataƙila ka saurari jawabi da aka bayar da kyau a taro, ka lura da wani saurayi da yake ƙoƙarin ya cim ma makasudi na ruhaniya, ko kuma ka lura da dattijo wanda yake da aminci wajen halartan taro duk da cewa ya tsufa. Kalmomin yabo za su iya taɓa zukatan irin waɗannan kuma ya ƙarfafa su. A iyali, mata da miji suna bukatar su ji kalaman yabo da ƙauna daga juna. (Misalai 31:10, 28) Musamman yara suna son su sani ana lura da su kuma ana ƙaunarsu. Yabo da kuma amincewa ga yaro sun yi daidai da yadda ruwa da hasken rana suke yi wa shuki. Iyaye ku nemi zarafin yaba wa yaranku domin kyawawan halinsu da kuma ƙoƙarinsu. Irin wannan yabo zai sa yaran su kasance da gaba gaɗi kuma ya sa su yi ƙoƙari sosai don su yi abin kirki.

18, 19. Me ya sa za mu yi iyaka ƙoƙarinmu mu kwantar da hankalin ’yan’uwanmu masu bi, kuma ta yaya za mu yi hakan?

18 Kwantar da hankali. Jehobah yana son “masu-tawali’u” ƙwarai kuma “masu-karyayyen zuciya.” (Ishaya 57:15) Kalmarsa ta aririce mu mu “ƙarfafa wa juna zuciya” kuma mu “ƙarfafa masu-raunanan zukata.” (1 Tassalunikawa 5:11, 14) Mu tabbata cewa Allah yana gani kuma yana amince da ƙoƙari da muke yi domin mu ƙarfafa ’yan’uwanmu da zukatansu ke cike da baƙin ciki.

Jehobah yana farin ciki sa’ad da muka furta magana mai ƙarfafa wasu

19 To, menene za mu faɗa domin mu ƙarfafa ɗan’uwa Kirista wanda ya raunana ko kuma ya karaya? Kada ka ga kamar dole ne ka magance matsalar. Sau da yawa, kalamai masu daɗi sun fi taimako. Ka tabbata wa mutumin  cewa ka damu da shi. Ka yi addu’a da wanda ko wadda ta ko ya raunana; za ka iya roƙon Jehobah ya taimake shi ya ko ta sani cewa wasu suna ƙaunarsa ko ƙaunarta kuma Allah ma yana haka. (Yaƙub 5:14, 15) Ka tabbatar masa cewa ana bukatarsa kuma yana da tamani a cikin ikilisiya. (1 Korintiyawa 12:12-26) Ka karanta aya daga Littafi Mai Tsarki da za ta tabbatar masa cewa Jehobah yana ƙaunarsa da gaske. (Zabura 34:18; Matta 10:29-31) Babu shakka idan ka ba da isashen lokaci ka faɗi “maganar alheri” daga zuciyarka ga mai sanyin gwiwa, zai ji ana ƙaunarsa.—Karanta Misalai 12:25.

20, 21. Waɗanne abubuwa ne suke sa gargaɗi ya kasance mai kyau?

20 Gargaɗi mai kyau. Da yake mu ajizai ne muna bukatar gargaɗi lokaci lokaci. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu: “Ka ji shawara, ka karɓi koyaswa, Domin ka yi hikima a ƙarshen kwanakinka.” (Misalai 19:20) Ba da gargaɗi ga wasu ba aikin dattawa ba ne kawai. Iyaye suna yi wa yara gargaɗi. (Afisawa 6:4) ’Yan’uwa mata da suka manyanta za su yi wa mata matasa gargaɗi. (Titus 2:3-5) Ƙaunar da muke yi wa wasu zai motsa mu mu yi musu gargaɗi da za su karɓa ba tare da suna ji kamar an ci musu fuska ba. Menene zai taimake mu ba da irin wannan gargaɗin? Yi la’akari da abubuwa uku da za su sa gargaɗi ya kasance  da kyau: hali da kuma dalilin mai gargaɗin, abin da ya sa za a yi gargaɗin, da kuma yadda aka yi gargaɗin.

21 Gargaɗi mai kyau yana farawa ne da mai ba da gargaɗin. Ka tambayi kanka, ‘Yaushe ne zan iya karɓan gargaɗi da sauƙi?’ Idan ka sani cewa wanda yake yi maka gargaɗi yana ƙaunarka, ba magana ba ne kawai yake yi domin baƙin cikinsa, kuma ba shi da wani ƙulli a cikinsa, gargaɗin zai kasance da sauƙin karɓa. Saboda haka, sa’ad da ka yi wa wasu gargaɗi, bai kamata ba ne halinka da kuma dalilinka na yin gargaɗin su kasance hakan? Gargaɗi mai kyau kuma yana kasancewa bisa Kalmar Allah. (2 Timothawus 3:16) Ko mun yi ƙauli kai tsaye daga Littafi Mai Tsarki ko kuma a’a, ya kamata gargaɗi da za mu bayar ya kasance yana da tushe cikin Nassosi. Saboda haka, ya kamata dattawa su mai da hankali domin kada su cusa ra’ayinsu a kan wasu kuma su juya Nassosi, ya zama kamar dai Littafi Mai Tsarki ya yarda da ra’ayinsu. Gargaɗi kuma yana kasancewa da kyau idan aka ba da shi a hanyar da ta dace. Idan aka ba da gargaɗi tare da kalamai masu daɗi yana kasancewa da sauƙin karɓa kuma wanda yake karɓa yana kasancewa da darajarsa.—Kolossiyawa 4:6.

22. Menene aniyarka game da yin amfani da kyautar magana?

22 Hakika, magana kyauta ce mai kyau daga Allah. Ƙaunarmu ga Allah ya kamata ta motsa mu mu yi amfani da kyautar da kyau. Ya kamata mu tuna cewa kalmomin da muke furtawa suna iya ƙarfafawa ko kuma su sa mutum ya yi sanyin gwiwa. Saboda haka, bari mu yi ƙoƙari mu yi amfani da wannan kyauta kamar yadda Mai bayarwa ya shirya, wato, domin “ginawa.” Da haka, maganarmu za ta kasance albarka ce ga waɗanda suke tare da mu kuma za ta taimake mu mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah.

^ sakin layi na 4 Kalmar Ibraniyawa da aka fassara “shiririta” a Misalai 15:4 tana kuma nufin “karkatacce, lalatace.”

^ sakin layi na 7 Idan harshenmu ba shi da linzami, yana fitar da baƙaƙen maganganu masu guba, dukan ayyukanmu na Kiristanci za su kasance banza ne a gaban Allah. Ya kamata mu mai da hankali a kan yadda muke magana?—Yaƙub 3:8-10.

^ sakin layi na 10 Kamar yadda aka yi amfani da ita a Nassosi, “ƙazamta” ya ƙunshi zunubai masu yawa. Ko da yake ba dukan ƙazamta suke bukatar shari’a ba, ana iya korar mutum daga ikilisiya idan ya ƙi tuɓa wajen yin ƙazamta mai tsanani.—2 Korintiyawa 12:21; Afisawa 4:19; Dubi “Tambayoyi Daga Masu Karatu” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2006, a Turanci.