Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 15

Ka Ji Dadi Cikin Dukan Aikinka

Ka Ji Dadi Cikin Dukan Aikinka

“Kowane mutum kuma . . . shi ji daɗi cikin dukan aikinsa.”—MAI-WA’AZI 3:13.

1-3. (a) Wane ra’ayi ne yawancin mutane suke da shi game da aikinsu? (b) Wane ra’ayi game da aiki ne Littafi Mai Tsarki yake ƙarfafawa, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan babin?

GA YAWANCIN mutane a duniyarmu ta yau, yin aiki ba shi da daɗi. Domin suna shan wahala a aikin da ba sa so, suna tsoron zuwa aiki kullum. Ta yaya za a iya motsa mutanen da suke da irin wannan halin su soma son aikinsu, balle ma su soma jin daɗin aikinsu?

2 Littafi Mai Tsarki yana ƙarfafa kasancewa da ra’ayi mai kyau game da yin aiki tuƙuru. Ya ce aiki da kuma amfaninsa duk albarka ce. Sulemanu ya rubuta: “Kowane mutum kuma shi ci, shi sha, shi ji daɗi cikin dukan aikinsa; wannan kyautar Allah ne.” (Mai-Wa’azi 3:13) Jehobah, wanda yake ƙaunarmu kuma wanda a kowane lokaci yana son ya ba mu abin da zai amfane mu, yana son mu ji daɗin aikinmu kuma mu sami amfanin aikin da muka yi. Idan muna son mu tsare kanmu a cikin ƙaunarsa, muna bukatar mu yi rayuwar da ta jitu da ra’ayinsa da kuma mizanansa game da aiki.—Karanta Mai-Wa’azi 2:24; 5:18.

3 A cikin wannan babin, za mu tattauna tambayoyi guda huɗu: Ta yaya za mu ji daɗi cikin dukan aikinmu? Waɗanne irin ayyuka ne ba su dace da Kiristoci na gaskiya ba? Ta yaya za mu iya daidaita aikinmu da kuma ayyukanmu na ruhaniya? Kuma wane aiki mafi muhimmanci ne za mu iya yi? Na farko, bari mu tattauna misalin manyan  ma’aikata guda biyu a sararin samaniya, wato, Jehobah Allah da Yesu Kristi.

MAI AIKI MAFI GIRMA DA GWANIN MAI AIKI

4, 5. Ta yaya ne Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah mai himma ne wajen aiki?

4 Jehobah ne Mai aiki Mafi Girma. Farawa 1:1 ta ce: “A cikin farko Allah ya halitta sama da ƙasa.” Sa’ad da Allah ya gama aikinsa na halitta a duniya, ya ce sakamakon “yana da kyau ƙwarai.” (Farawa 1:31) Hakan yana nufin cewa, ya gamsu sosai da dukan ayyukan da ya yi a duniya. Jehobah, “Allah mai farin ciki,” babu shakka ya yi farin ciki sosai domin aikin da ya yi.—1 Timothawus 1:11NW.

5 Allahnmu mai himma wajen aiki bai taɓa daina aiki ba. Da daɗewa bayan an kammala halittan duk wani abu a duniya, Yesu ya ce: “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki.” (Yohanna 5:17) Menene Uban yake yi? Daga mazauninsa a sama, ya ci gaba da kāre da kuma kula da ’yan adam. Ya riga ya haifar da “sabon halitta,” wato, Kiristoci haifaffu daga ruhu waɗanda za su yi sarauta da Yesu a sama. (2 Korintiyawa 5:17) Ya kuma ci gaba da yin aiki don ya cika nufinsa ga ’yan adam, wato, waɗanda suke ƙaunarsa su sami rai madawwami a sabuwar duniya. (Romawa 6:23) Babu shakka, Jehobah ya yi farin ciki sosai da sakamakon wannan aikin. Miliyoyin mutane sun saurari saƙon Mulki, kuma Allah ya jawo su sun kuma daidaita rayuwarsu don su ci gaba da tsare kansu cikin ƙaunarsa.—Yohanna 6:44.

6, 7. Wane irin suna na yin aiki tuƙuru ne Yesu ya yi tun da daɗewa?

6 Tun da daɗewa, Yesu ya yi suna wajen yin aiki tuƙuru. Kafin ya zo duniya, shi ne “gwanin mai-aiki” na Allah a wajen halittar dukan abubuwa “cikin sammai da bisa duniya.” (Misalai 8:22-31; Kolossiyawa 1:15-17) Sa’ad da yake duniya, Yesu ya ci gaba da yin aiki tuƙuru. Tun yana yaro,  ya koyi aikin gini, kuma an san cewa shi “masassaƙi” ne. * (Markus 6:3) Wannan ya ƙunshi yin aiki tuƙuru da kuma ƙwarewa, musamman a zamanin da babu ma’aikatar yanka katakai, wajen sayen kayan aiki, da kuma kayan aiki masu amfani da wutar lantarki. Ka yi tunanin yadda Yesu yake zuwa ya samo katakansa, wataƙila ta wajen kada itatuwa kuma ya ja icen zuwa inda yake aiki. Ka yi tunanin kana ganinsa sa’ad da yake gina gidaje, yana shirya kuma yana buga ginshiƙai na rufin kwano, yana haɗa ƙofofi, yana kuma haɗa kayan ɗaki. Babu shakka, Yesu da kansa ya san daɗin da ake samu daga aiki tuƙuru mai kyau da aka yi.

7 Yesu ya nuna himma sosai a aikinsa na hidima. A cikin shekara uku da rabi, ya shagala sosai da wannan aiki mai muhimmanci. Domin yana son ya kai ga mutane masu yawa, ba ya ɓata lokaci, kuma yana tashi tun da safe ya ci gaba da aiki har dare. (Luka 21:37, 38; Yohanna 3:2) Ya yi tafiya “a cikin birane da ƙauyuka, yana wa’azi, yana kawo bishara ta mulkin Allah.” (Luka 8:1) Yesu ya yi tafiya har na tsawon ɗarurruwan mil, ya yi tafiyar ne da kafa a kan hanya mai ƙura don ya kai bishara ga mutane.

8, 9. Ta yaya ne Yesu ya sami farin ciki a aiki tuƙuru da ya yi?

8 Yesu ya sami gamsuwa sosai a aiki tuƙuru da ya yi a hidima kuwa? Ƙwarai kuwa! Ya shuka iri na gaskiyar Mulki, ya kuma bar gonakin da suka nuna don girbi. Yin aikin Allah ya sa Yesu ya sami ƙarfi da gamsuwa har ya ƙyale abinci don cika aikin. (Yohanna 4:31-38) Ka yi tunanin irin gamsuwar da ya samu wadda hakan ta sa a ƙarshen hidimarsa ya sami dalilin gaya wa Ubansa: “Na ɗaukaka ka a duniya, yayinda na cika aikin da ka ba ni in yi.”—Yohanna 17:4.

9 Babu shakka, Jehobah da Yesu su ne misalai da ke kan  gaba na waɗanda suka ji daɗin aiki tuƙuru da suka yi. Ƙaunar da muke yi wa Jehobah tana motsa mu mu “zama fa masu-koyi da Allah.” (Afisawa 5:1) Ƙaunar da muke yi wa Yesu tana motsa mu mu “bi sawunsa” sawu da kafa. (1 Bitrus 2:21) Bari yanzu mu bincika yadda mu ma za mu iya jin daɗin aiki tuƙuru da muke yi.

YADDA ZA MU JI DAƊI CIKIN DUKAN AIKINMU

Yin amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka sami farin ciki a aikin da kake yi

10, 11. Menene zai iya taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da aikinmu?

10 Aiki yana iya zama sashen rayuwar Kiristoci na gaskiya. Muna son mu sami gamsuwa da wadatar zuciya a aikinmu, amma hakan zai iya zama ƙalubale idan muna yin aikin da ba ma so. Ta yaya za mu iya jin daɗin aikinmu a irin wannan yanayin?

11 Ta wajen kasancewa da ra’ayin da ya dace. Ba a kowane lokaci ba ne za mu iya canja yanayinmu ba, amma za mu iya canja halinmu. Yin bimbini a kan ra’ayin Allah zai iya taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da aiki. Alal misali, idan kai shugaban iyali ne, ka tuna cewa aikinka, ko yaya ƙanƙantarsa, yana sa ka yi wa iyalinka tanadin ainihin abubuwan da suke bukata. Saboda haka, kula da ƙaunatattunka ba ƙaramin abu ba ne a gaban Allah. Kalmarsa ta ce wanda ya ƙi yi wa iyalinsa tanadi “gwamma mara-bangaskiya da shi.” (1 Timothawus 5:8) Sanin cewa aikinka wata hanya ce ta cim ma muradinka, wato, cika hakkin da Allah ya ba ka, hakan zai iya taimaka maka ka sami gamsuwa da manufa wadda abokan aikinka ba su da shi.

12. A waɗanne hanyoyi ne kasancewa masu ƙwazo da gaskiya a aikinmu yake da kyau?

12 Ta wajen kasancewa mai ƙwazo da kuma mai faɗin gaskiya. Yin aiki tuƙuru da kuma koyan yadda za mu yi aikinmu sosai zai iya kawo albarka. Shugabannin aiki suna son  ƙwararrun ma’aikata kuma masu ƙwazo. (Misalai 12:24; 22:29) Mu Kiristoci na gaskiya, dole ne mu kasance masu gaskiya a wajen aikinmu, kada mu saci kuɗi, kayan aiki, ko kuwa lokaci daga shugaban aikinmu. (Afisawa 4:28) Kamar yadda muka gani a babin da ya gabata, gaskiya tana da amfani sosai. Za a iya gaskatawa da ma’aikaci mai gaskiya. Ko da shugaban aikinmu ya lura cewa muna aiki tuƙuru ko bai lura ba, za mu iya samun farin cikin da ke tattare da samun “kyakkyawan lamiri” da kuma sanin cewa muna faranta ran Allah da muke ƙauna.—Ibraniyawa 13:18; Kolossiyawa 3:22-24.

13. Wane irin sakamako ne halinmu mai kyau a wurin aiki zai iya kawowa?

 13 Ta sanin cewa halinmu zai iya ɗaukaka Allah. Sa’ad da muka ci gaba da nuna halin da ya dace da Kirista a wajen aikinmu, mutane za su lura da hakan. Menene zai kasance sakamakon hakan? Za mu “zama ado ga koyaswa ta Allah Mai-cetonmu.” (Titus 2:9, 10) Hakika, halinmu mai kyau zai iya sa wasu su ga kyaun bautarmu, kuma su so ta sosai. Ka yi tunanin yadda za ka ji idan abokin aikinka ya soma bin gaskiya domin misalinka mai kyau a wurin aiki! Mafi muhimmanci, yi la’akari da wannan: Wane sakamako ya fi sanin cewa halinka mai kyau yana ɗaukaka Jehobah kuma yana faranta zuciyarsa?—Karanta Misalai 27:11; 1 Bitrus 2:12.

YIN AMFANI DA FAHIMI A WAJEN ZAƁAN AIKIN DA ZA MU YI

14-16. Sa’ad da muka fuskanci yin shawarwari game da aiki, waɗanne tambayoyi masu muhimmanci ne muke bukatar mu yi?

14 Littafi Mai Tsarki bai faɗi dalla-dalla irin aikin da za mu yi da wanda ba za mu yi ba. Hakan ba ya nufin cewa za mu iya karɓan kowane irin aiki ko da menene hakan ya ƙunsa. Nassosi za su iya taimaka mana mu zaɓi aiki mai kyau da zai faranta wa Allah rai yayin da muke guje wa aikin da zai ɓata masa rai. (Misalai 2:6) Sa’ad da muke fuskantar yanke shawarwari game da aiki, akwai tambayoyi masu muhimmanci guda biyu da za mu tattauna.

15 Yin ainihin wannan aikin zai ƙunshi yin abin da Littafi Mai Tsarki ya hana ne? Kalmar Allah dalla-dalla ta haramta sata, ƙarya, da kuma ƙera gumaka. (Fitowa 20:4; Ayukan Manzanni 15:29; Afisawa 4:28; Ru’ya ta Yohanna 21:8) Za mu ƙi duk wani irin aikin da zai sa mu yi waɗannan abubuwan. Ƙaunar da muke yi wa Jehobah ba za ta taɓa ƙyale mu mu karɓi aikin da ya ƙunshi yin ayyukan da suka saɓa wa dokokin Allah ba.—Karanta 1 Yohanna 5:3.

 16 Yin wannan aikin zai sa mu saka hannu ko kuwa mu ƙarfafa wasu su yi abin da bai dace ba? Ga misali. Yin aiki a matsayin mai yi wa baƙi maraba ba laifi ba ne. To, idan aka ba Kirista irin wannan aikin a asibitin da ake zubar da ciki fa? Hakika, aikinsa ba zai ƙunshi saka hannu kai tsaye wajen zubar da cikin ba. Duk da haka, aikin da yake yi a wurin a kowane lokaci ba zai taimaka ba ne wajen ci gaban asibitin da aka buɗe don zubar da ciki ba, aikin da ya saɓa  wa Kalmar Allah? (Fitowa 21:22-24) A matsayin masu ƙaunar Jehobah, ba ma son wani abu ya haɗa mu da ayyukan da suka saɓa wa Nassosi.

17. (a) Waɗanne abubuwa ne ya kamata mu yi tunani a kai sa’ad da muke yanke shawarwari game da aiki? (Duba akwatin nan da ke  shafi na 177.) (b) Ta yaya ne lamirinmu zai iya taimaka mana mu yanke shawarwarin da za su faranta wa Allah rai?

17 Za a iya samun yawancin amsoshin tambayoyin da suka shafi aiki, ta wajen bincika amsoshin tambayoyi biyu masu muhimmanci da aka yi a babi na 15 da 16. Ƙari ga haka, akwai wasu abubuwa da muke bukatar mu yi tunani sosai a kansu sa’ad da muke yanke shawara game da aiki. * Ba za mu yi zaton cewa rukunin bawan nan mai aminci zai  kafa dokokin da za su yi mana ja-gora a dukan wani yanayin da zai iya tasowa ba. A nan ne muke bukatar fahimi. Kamar yadda muka koya a Babi na 2, muna bukatar mu koyar da lamirinmu ta wajen yin nazarin yadda za mu yi amfani da Kalmar Allah a rayuwarmu ta yau da kullum. Da ‘hankulanmu wasassu’ da muke horarwa yau da kullum, lamirinmu zai iya taimaka mana mu yanke shawarwarin da suke faranta wa Allah rai kuma su sa mu tsare kanmu a cikin ƙaunarsa.—Ibraniyawa 5:14.

KASANCEWA DA DAIDAITACCEN RA’AYI GAME DA AIKI

18. Me ya sa bai da sauƙi a ci gaba da kasancewa da daidaituwa a ruhaniya?

18 Ci gaba da kasancewa cikin ƙaunar Allah ba shi da sauƙi a waɗannan “kwanaki na ƙarshe” da ke cike da “miyagun” abubuwa. (2 Timothawus 3:1) Samun aiki da kuma riƙe shi zai iya zama ƙalubale. A matsayinmu na Kiristoci na gaskiya, mun fahimci muhimmancin yin aiki tuƙuru don mu yi wa iyalinmu tanadi. Amma idan ba mu mai da hankali ba, matsi a wurin aiki ko kuwa tunanin son abin duniya zai iya shafar ayyukanmu na ruhaniya. (1 Timothawus 6:9, 10) Bari mu tattauna yadda za mu kasance da daidaituwa, kuma mu tabbata da “mafifitan al’amura.”—Filibbiyawa 1:10.

19. Me ya sa Jehobah ya cancanci mu dogara da shi gabaki ɗaya, kuma menene irin wannan dogarar za ta sa mu guje wa?

19 Ka dogara gabaki ɗaya ga Jehobah. (Karanta Misalai 3:5, 6.) Ya cancanci mu dogara a gare shi. Ban da haka ma, yana kula da mu. (1 Bitrus 5:7) Ya san bukatunmu fiye da mu, kuma zai biya bukatunmu. (Zabura 37:25) Saboda haka, ya kamata mu saurara sa’ad da Kalmarsa ta tuna mana cewa: “Ku kawarda hankalinku daga ƙaunar kuɗi; ku haƙura da abin da ku ke da shi: gama shi [Allah] da kansa ya ce, Daɗai ba  ni tauye maka ba, daɗai kuwa ba ni yashe ka ba.” (Ibraniyawa 13:5) Yawancin waɗanda suke hidima na cikakken lokaci za su gaya maka iyawar Allah na yin tanadin abubuwan da ake bukata a rayuwa. Idan muka gaskata sosai cewa Jehobah zai kula da mu, za mu daina nuna yawan damuwa game da yi wa iyalinmu tanadi. (Matta 6:25-32) Ba za mu ƙyale aiki ya sa mu yi watsi da ayyukanmu na ruhaniya ba,  kamar su yin wa’azin bishara da kuma halartar taro.—Matta 24:14; Ibraniyawa 10:24, 25.

20. Menene kasancewa mai sauƙin ido yake nufi, kuma ta yaya za ka iya kasancewa da irin wannan ra’ayin?

20 Bari idonka ya kasance lafiyayye. (Karanta Matta 6:22, 23.) Kasancewa marar rawan ido yana daidaita rayuwarmu. Kirista marar rawan ido yana mai da hankali ga manufa ɗaya, wato, yin nufin Allah. Idan muka mai da idonmu wuri guda, ba za mu damu da neman aikin da ake biyan kuɗi ba sosai, kuma ba za mu biɗi salon rayuwa marar sauƙi ba. Kuma ba za mu dawwama cikin neman abin duniya da suka fito da masu talla za su sa mu gaskata cewa muna bukatarsu don mu yi farin ciki. Ta yaya za ka iya kasancewa marar rawan ido? Ka guji cin bashi da bai dace ba. Kada ka kewaye rayuwarka da abubuwan da za su janye lokacinka da hankalinka. Ka bi shawarar Littafi Mai Tsarki na samun gamsuwa “da abinci da sutura.” (1 Timothawus 6:8) Ka nemi sauƙaƙa rayuwarka yadda ya kamata.

21. Me ya sa ya kamata mu kafa makasudai, kuma menene ya kamata ya zama farko a rayuwarmu?

21 Ka kafa makasudai na ruhaniya, kuma ka manne masu. Tun da yake ba mu da isashen lokaci a rayuwa, muna bukatar mu kafa makasudai. Idan ba haka ba, abubuwa marar muhimmanci za su iya janye lokacinmu, kuma su sha kan abubuwa mafi muhimmanci. Menene ya kamata mu sa farko a rayuwarmu? Yawancin mutane a duniya sun fi mai da hankali ga biɗar ƙarin ilimi don su sami aiki mai kyau a wannan duniyar. Amma, Yesu ya aririci mabiyansa su “fara biɗan mulki.” (Matta 6:33) Hakika, a matsayinmu na Kiristoci na gaskiya, muna saka Mulkin Allah farko a rayuwarmu. Salon rayuwarmu, zaɓen da muke yi, makasudan da muke kafawa, da kuma ayyukan da muke biɗa, ya kamata su nuna cewa al’amuran Mulki  da yin nufin Allah su ne mafi muhimmanci a gare mu fiye da abubuwan duniya.

NUNA ƘWAZO A HIDIMA

Za mu iya nuna ƙaunarmu ga Jehobah ta wajen saka aikin wa’azi farko a rayuwarmu

22, 23. (a) Menene ainihin aikin Kiristoci na gaskiya, kuma ta yaya za mu nuna cewa wannan aikin yana da muhimmanci a gare mu? (Duba akwatin nan da ke  shafi na 180.) (b) Menene ƙudurinka game da aikinka?

22 Sanin cewa muna zaune ne a lokaci na ƙarshe, muna bukatar mu mai da hankali a kan ainihin aikin Kiristoci na gaskiya, wato, wa’azi da almajirantarwa. (Matta 24:14; 28:19, 20) Kamar wanda muke bin misalinsa, Yesu, muna son mu shagala da wannan aiki na ceton rai. Ta yaya za mu nuna cewa wannan aikin yana da muhimmanci a gare mu? Yawancin mutanen Allah sun shagala sosai a aikin wa’azi da dukan zuciyarsu a matsayin masu shela a ikilisiya. Wasu sun sake tsara al’amuransu don su yi hidima a matsayin majagaba ko masu wa’azi a ƙasashen waje. Domin sun san muhimmancin makasudai na ruhaniya, iyaye da yawa sun ƙarfafa yaransu su biɗi hidima na cikakken lokaci. Masu wa’azin Mulki da ƙwazo suna jin daɗin aiki tuƙuru da suke yi a hidima kuwa? Ƙwarai kuwa! Bauta wa Jehobah da dukan zuciya ita ce kaɗai hanyar da za ta sa mu sami farin ciki a rayuwa, gamsuwa, da kuma albarka marar iyaka.—Karanta Misalai 10:22.

23 Yawancinmu muna yin awoyi a wajen aikinmu don mu yi wa iyalinmu tanadi. Ka tuna cewa Jehobah yana son mu sami farin ciki a aiki tuƙuru da muke yi. Ta wajen barin halinmu da ayyukanmu su jitu da ra’ayinsa da kuma mizanansa, za mu iya samun gamsuwa a aikinmu. Bari mu ƙudurta cewa ba za mu taɓa barin aikinmu ya janye hankalinmu daga ainihin aikinmu ba, wato, yin bisharar Mulkin Allah. Ta wajen saka wannan aikin a kan gaba a rayuwarmu, za mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah kuma za mu tsare kanmu a cikin ƙaunarsa.

^ sakin layi na 6 Kalmar Helenanci da aka fassara “masassaƙi” an ce “kalma ce da ke nufin masassaƙin da zai iya gyara gidaje ko kayan ɗaki ko kuwa duk wani irin aikin da ya shafi yin amfani da katako.”

^ sakin layi na 17 Don ƙarin bayani game da abubuwan da ya kamata a yi la’akari da su game da aiki, duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu , 1999, shafi na 28-30, da kuma 15 ga Yuli, 1982, shafi na 26.