Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 7

Rai Yana da Muhimmanci a Gare Ka Kamar Yadda Yake ga Allah?

Rai Yana da Muhimmanci a Gare Ka Kamar Yadda Yake ga Allah?

“A wurinka maɓulɓular rai ta ke.”—ZABURA 36:9.

1, 2. Wace kyauta ce daga Allah musamman take da muhimmanci a yau, kuma me ya sa?

UBANMU na samaniya ya ba mu wani kyauta mai tamani ƙwarai, kyautar rai ga mutane masu hankali waɗanda za su iya nuna irin halayensa. (Farawa 1:27) Domin wannan kyauta mai tamani, muna iya tunani bisa Littafi Mai Tsarki. Idan muka yi amfani da su, za mu zama mutane waɗanda suka manyanta a ruhaniya waɗanda suke ƙaunar Jehobah kuma waɗanda “hankulansu wasassu bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.”—Ibraniyawa 5:14.

2 Yin tunani a kan mizanan Littafi Mai Tsarki yana da muhimmanci musamman a yau, domin duniya ta zama da wuya da babu adadin dokoki da za su ja-goranci dukan yanayi da za su taso a rayuwa. Hanyar magani kwatanci ce mai kyau na wannan yanayi, musamman ma magunguna da kuma hanyar magani da ta ƙunshi jini. Wannan wuri ne da dukan waɗanda suke so su yi wa Jehobah biyayya ya kamata su mai da hankali kuma su damu da shi. Duk da haka, idan muka fahimci mizanai da suka shafi wannan, za mu iya mu yanke shawarar da za ta gamsar da lamirinmu kuma ta sa mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah. (Misalai 2:6-11) Ka yi la’akari da waɗannan mizanan.

RAI DA JINI SUNA DA TSARKI

3, 4. Yaushe aka nuna cewa jini yana da tsarki a cikin Nassosi, kuma bisa wane mizani yake?

3 Ba da daɗewa ba bayan da Kayinu ya kashe Habila, Jehobah ya nuna dangantaka da take tsakanin rai da jini da kuma tsarkinsu. Allah ya ce wa Kayinu. “Muryar jinin ƙaninka ta yi ƙara a wurina daga ƙasa.” (Farawa 4:10) A gaban Jehobah, jinin Habila yana nufin ransa, wanda aka kashe. Saboda haka, jinin Habila yana ƙara yana bukatar fansa.—Ibraniyawa 12:24.

4 Bayan Ruwan Tufana, Allah ya ba wa mutane izini su ci nama na dabbobi amma ba jininsu ba. Allah ya ce: “Sai dai nama tare da ransa, watau jininsa ke nan, wannan ba za ku ci ba. Lallai kuwa zan ja jininku, jini na rayukanku.” (Farawa 9:4, 5) Wannan umurnin ya shafi dukan zuriyar Nuhu har zuwa yanzu a zamaninmu. Ya tabbata da abin da aka faɗa wa Kayinu da farko cewa ran dukan wata halitta a jininsa take. Wannan doka kuma ta tabbatar da cewa Jehobah, tushen rai, zai hukunta dukan mutane da suka ƙi daraja rai da kuma jini.—Zabura 36:9.

5, 6. Ta yaya Dokar Musa ta nuna cewa jini yana da tamani kuma yana da tsarki? (Dubi kuma akwati da ke  shafi na 78.)

5 Waɗannan abubuwa biyu masu muhimmanci sun bayyana a cikin Dokar Musa. Leviticus 17:10, 11 suka ce: “Kowane mutum kuma . . . wanda ya ci kowane irin jini; sai in yi gāba da wannan mai-rai wanda ya ci jini, in datse shi daga cikin jama’assa. Gama ran nama yana cikin jini: na kuwa ba ku shi bisa bagadi domin a yi kafarar rayukanku: gama jini ne ke yin kafara sabada rai.” *—Dubi akwatin nan “ Ikon Kafara ta Jini,” da ke shafi na 76.

 6 Idan ba a yi amfani da jinin dabba a kan bagadi ba, za a zubar ne a ƙasa. Ta haka, a hanya ta alama, an mai da rai ga Mai shi. (Kubawar Shari’a 12:16; Ezekiel 18:4) Amma ka lura, ba a bukaci Isra’ilawa su cire dukan wani alamar jini daga tsokar dabba ba. Idan an yanka dabban da kyau kuma jini ya zuba, Ba’isra’ile zai iya ci da lamiri mai kyau, domin an riga an daraja Mai ba da Rai.

7. Ta yaya Dauda ya nuna daraja ga jini?

 7 Dauda “mutum gwargwadon zuciyata [Allah],” ya fahimci mizanin Allah game da jini. (Ayukan Manzanni 13:22) A wani lokaci sa’ad da yake jin ƙishirwa, uku cikin mutanensa suka ratsa cikin zangon abokan gaba, suka ja ruwa daga rijiya, suka kawo masa. Me Dauda ya yi? “zan sha jinin mutane waɗanda suka kasaida ransu?” ya yi tambaya. A wajen Dauda, ruwan kamar jinin waɗannan mutanen ne. Duk da ƙishin da yake ji, “ya zubas ma Ubangiji.”—2 Samuila 23:15-17.

8, 9. Shin ra’ayin Allah game da rai da jini ya canja ne sa’ad da aka kafa ikilisiyar Kirista? Ka yi bayani.

8 Bayan shekaru 2,400 da aka ba wa Nuhu doka, kuma bayan shekara 1,500 da aka kafa doka ta alkawari, Jehobah ya hure Hukumar da Ke Kula Ayyukanmu na ƙarni na farko su rubuta: “Ruhu Mai-tsarki, da mu kuma, kada mu nawaita maku wani abu gaba da waɗannan wajibai; ku hanu daga abin da aka miƙa ma gumaka, da jini kuma, da abin da aka maƙare, da fasikanci.”—Ayukan Manzanni 15:28, 29.

9 A bayyane yake cewa Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu na dā sun fahimci cewa jini yana da tsarki kuma wasa da shi ba daidai ba ne kamar bautar gumaka ko kuma fasikanci. Kiristoci na gaskiya a yau sun yarda da wannan. Ƙari ga haka, domin suna tunani bisa mizanai na Littafi Mai Tsarki, suna faranta wa Jehobah rai sa’ad da suke yanke shawara game da amfani da jini.

AMFANI DA JINI WAJEN MAGANI

Ta yaya zan yi wa likita bayani game da shawarata ta karɓan ɓangarorin jini?

10, 11. (a) Ta yaya Shaidun Jehobah suke ɗaukan ƙarin jini da kuma ɓangarori huɗu na jini? (b) A waɗanne wurare game da jini ne Kiristoci suna iya kasancewa da ra’ayi da ya bambanta?

10 Shaidun Jehobah sun fahimci cewa “hanu daga . . . jini” yana nufin ƙin karɓan ƙarin jini da kuma ƙin ba da jini ko kuma ajiye jininsu domin a yi wa wasu ƙarin jini. Kuma domin daraja dokar Allah ba sa karɓan ainihin  ɓangarori huɗu na jini: wato, jajaye da fararen ƙwayoyin halitta na jini, kamewar jini, da kuma ruwan jini.

11 A yau, ta wajen ƙarin rarrabawa, waɗannan ɓangarori ana iya ƙara raba su kuma a yi amfani da su a hanyoyi dabam dabam. Shin Kirista yana iya yin amfani da waɗannan ne? Yana ɗaukansu a matsayin “jini” ne? Kowane Kirista zai yanke shawararsa game da wannan. Haka kuma ya kasance ga wasu hanyoyin magani kamar su hemodialysis, hemodilution, da cell salvage da ya ƙunshi amfani da jinin mutum, idan ba a ajiye shi ba.—Dubi Rataye, shafuffuka na 215-218.

12. Yaya za mu ɗauki kuma mu magance batu da ya kasance na lamiri?

12 Shin shawarar da mutum zai yanke wa kansa ba shi da muhimmanci ne sosai ga Jehobah? Suna da muhimmanci, domin ya damu da tunaninmu da kuma abin da yake motsa  mu. (Karanta Misalai 17:3; 24:12) Saboda haka, bayan mun yi addu’a kuma mun yi bincike game da wata hanyar magani ko kuma wani magani, sai mu bi lamirinmu da aka koyar da Littafi Mai Tsarki. (Romawa 14:2, 22, 23) Hakika, kada wasu su cusa nasu lamiri a kanmu, kuma kada mu yi tambaya, “Me za ka yi da a ce kai ne kake da wannan matsalar?” A wannan batu, kowane Kirista ya kamata ya “ɗauki kayan kansa.” *Galatiyawa 6:5; Romawa 14:12; Dubi akwatin nan “ Ina Ɗaukan Jini da Tsarki Kuwa?” da ke shafi na 81.

DOKOKIN JEHOBAH SUN NUNA ƘAUNARS

13. Menene dokokin Jehobah da kuma mizanansa suka nuna game da shi? Ka kwatanta.

13 Dokoki da kuma mizanai da muka gani cikin Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa Jehobah mai ba da doka ne mai hikima kuma Uba ne mai ƙauna ƙwarai mai kula da bukatun ’ya’yansa. (Zabura 19:7-11) Ko da yake dokar nan “hanu daga . . . jini” ba a ba da shi ba domin kiyaye lafiya, ya kāre mu daga matsaloli da suke tasowa daga ƙarin jini. (Ayukan Manzanni 15:20) Hakika, mutane da yawa a tsakanin malaman kiwon lafiya sun ce yin fiɗa ba tare da ƙarin jini ba shi ne “mizani mafi kyau” a hanyar magani na zamani. Ga Kiristoci na gaskiya kuma irin wannan yana tabbatar da hikima marar iyaka ta Jehobah Ubanmu mai ƙauna.—Karanta Ishaya 55:9; Yohanna 14:21, 23.

14, 15. (a) Ƙaunar Allah ga mutanensa ta bayyana ne cikin waɗanne dokoki? (b) Ta yaya za ka yi amfani da mizanai da ya sa aka fito da wannan doka?

14 Damuwa da Allah yake yi game da mutanensa ta bayyana cikin dokokinsa masu yawa. Alal misali, ya bukaci a ja wa rufi na gidan Isra’ilawa dangarama domin ya hana mutane faɗuwa, tun da ana yawan ayyuka a wajen. (Kubawar  Shari’a 22:8; 1 Samuila 9:25, 26; Nehemiah 8:16; Ayukan Manzanni 10:9) Allah kuma ya ba da doka cewa a kula da bijimai masu faɗa. (Fitowa 21:28, 29) Ƙin bin wannan doka zai nuna rashin damuwa da lafiyar wasu kuma hakan zai iya jawo alhakin jini.

15 Ta yaya za ka yi amfani da mizanai da aka fito da wannan doka daga cikinsu? Me ya sa ba za ka yi tunanin motarka ba, yadda kake tuƙi, dabbobinka, gidanka, wurin aikinka, da kuma irin nishaɗi da kake so? A wasu ƙasashe, haɗarin mota su suka fi kashe matasa, sau da yawa domin suna yin ganganci. Amma, matasa da suke so su kasance cikin ƙaunar Allah suna ɗaukan rayuwarsu da tamani kuma ba sa neman farin ciki cikin ayyuka masu haɗari. Ba sa tunanin wauta cewa babu abin da zai sami matasa. Maimakon haka, suna morar ƙuruciyarsu ta wajen guje wa bala’i.—Mai-Wa’azi 11:9, 10.

16. Wane mizanin Littafi Mai Tsarki ne ya shafi zubar da ciki? (Dubi hasiya.)

16 Har ran wanda ba a haifa ba yana da muhimmanci a gaban Allah. A Isra’ila ta dā, idan wani ya ji wa mace mai ciki rauni idan ta mutu ko kuma ta yi ɓari domin wannan, Allah zai riƙe wannan mutumin da hakkin kisa, kuma zai ba da fansa “rai don rai.” * (Karanta Fitowa 21:22, 23) To, ka yi tunanin yadda Jehobah zai ji sa’ad da ya ga ana zubar da ciki da gangan kowace shekara, ana hadaya da su don a gamsar da sha’awar jiki da kuma ’yancin jima’i.

17. Ta yaya za ka ƙarfafa wadda ta zubar da ciki kafin ta koyi game da mizanan Allah?

17 To, mai zai faru da mace da ta zubar da ciki kafin ta zo  ga sanin gaskiyar Littafi Mai Tsarki? Ta riga ta wuci Allah ya yi mata jin ƙai ne? A’a! Hakika, mutumin da ya tuba da gaske zai iya samun gafarar Jehobah bisa ga jinin Yesu. (Zabura 103:8-14; Afisawa 1:7) Hakika, Kristi da kansa ya ce: “Ni  ban zo domin in kira masu-adalci ba, amma masu zunubi zuwa tuba.”—Luka 5:32.

KA GUJI MUGUN TUNANI!

18. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna dalilin yawan zubar da jini?

18 Ban da ji wa wasu rauni, Jehobah yana so mu kawar da tushin zubar da jini daga zuciyarmu, wato ƙiyayya. Manzo Yohanna ya rubuta: “Dukan wanda ya ƙi ɗan’uwansa mai-kisankai ne.” (1 Yohanna 3:15) Irin wannan mutumin ba ya son ɗan’uwansa kuma yana fata ya mutu. Irin wannan ƙiyayya tana iya bayyana ta wajen yi wa mutum tsegumi ko kuma sharri da idan gaskiya ne zai jawo hukuncin Allah. (Leviticus 19:16; Kubawar Shari’a 19:18-21; Matta 5:22) Saboda haka, ya kamata mu yi aiki wajen kawar da duk wani irin ƙiyayya da ke zuciyarmu!—Yaƙub 1:14, 15; 4:1-3.

19. Yaya mutumin da mizanan Littafi Mai Tsarki suke yi masa ja-gora yake ɗaukan abin da ke Zabura 11:5 da kuma Filibbiyawa 4:8, 9?

19 Dukan waɗanda suka ɗauki rai kamar yadda Jehobah ya yi da kuma waɗanda suka tsare kansu cikin ƙaunar Allah suna guje wa dukan wani irin nuna ƙarfi. Zabura 11:5 ta ce: “Mai-mugunta da mai-son zalunci ransa [Jehobah] yana ƙinsu.” Wannan furcin ba kwatanta halayen Allah kawai yake yi ba; amma mizani ne na ja-gora a rayuwa. Yana motsa waɗanda suke ƙaunar Allah su guje wa dukan wani nishaɗi da yake ɗaukaka nuna ƙarfi. Hakazalika, furcin da ya ce Jehobah ‘Allah ne na salama’ ya motsa bayinsa su cika zukatansu da abubuwa masu jawo ƙauna, masu tsabta, masu jawo yabo, waɗanda suke kawo salama.—Karanta Filibbiyawa 4:8, 9.

KA GUJI ƘUNGIYOYIN DA SUKE DA ALHAKIN JINI

20-22. Menene matsayin Kiristoci game da duniya, kuma me ya sa?

20 A gaban Allah, dukan duniyar Shaiɗan tana da alhakin jini. Tsarinsa na siyasa, da aka kwatanta a Nassosi a matsayin  mugun bisa, ya kashe miliyoyin mutane, har da bayin Jehobah masu yawa. (Daniel 8:3, 4, 20-22; Ru’ya ta Yohanna 13:1, 2, 7, 8) Ba da haɗin kai ga wannan iko mai kama da bisa, ’yan kasuwa da kuma masanan kimiyya sun ƙirƙiro miyagun makamai, kuma suna samun riba masu yawa. Hakika, “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.”—1 Yohanna 5:19.

21 Domin mabiyan Yesu “ba na duniya ba ne” kuma ba su saka hannu a cikin siyasa ba da kuma yaƙe-yaƙe, sun guje wa kasancewa da alhakin jini a kowace hanya. * (Yohanna 15:19; 17:16) Kuma ta wajen yin koyi da Kristi, ba sa faɗa sa’ad da ake tsananta musu. Maimakon haka, suna nuna ƙauna ga abokan gabansu, har suna yin addu’a dominsu.—Matta 5:44; Romawa 12:17-21.

22 Fiye da kome, Kiristoci na gaskiya suna guje wa yin sha’ani da “Babila Babba,” wato, daular duniya ta addinan  ƙarya kuma wadda ta fi kowa ɗaukan alhakin jini. Kalmar Allah ta ce: “A cikinta aka samu jinin annabawa da na tsarkaka, da na dukan waɗanda aka kashe a duniya.” Saboda haka, ana yi mana gargaɗi: “Ku fito daga cikinta, ya al’ummata.”—Ru’ya ta Yohanna 17:6; 18:2, 4, 24.

23. Menene fita daga cikin Babila Babba yake nufi?

23 Fita daga cikin Babila Babba ya ƙunshi fiye da cire sunan mutum daga littafin sunan waɗanda suke cikinta. Ya kuma ƙunshi ƙin miyagun ayyuka da addinin ƙarya ya ƙyale ko kuma waɗanda suke yaɗawa, irinsu lalata, saka hannu cikin siyasa, da kuma haɗama wajen neman arziki. (Karanta Zabura 97:10; Ru’ya ta Yohanna 18:7, 9, 11-17) Sau da yawa waɗannan ayyuka suna kai ga zubar da jini!

24, 25. (a) Bisa ga menene Allah zai nuna jin ƙai ga mutumin da ya tuba wanda yake da alhakin jini? (b) Kuma hakan ya tuna mana da wane tsari da mutanen Allah suke bi a dā?

24 Kafin mu fara bin addini na gaskiya, kowannenmu, a wata hanya, ya tallafa wa tsarin Shaiɗan kuma saboda haka yana da ɗan alhakin jini. Amma, domin mun canja halayenmu, mun ba da gaskiya bisa hadayar fansa ta Kristi, mun kuma keɓe kanmu ga Allah, mun sami jin ƙan Allah da kuma kāriya ta ruhaniya. (Ayukan Manzanni 3:19) Irin wannan kāriya sun tuna mana da biranen mafaka a zamanin dā.—Litafin Lissafi 35:11-15; Kubawar Shari’a 21:1-9.

25 Ta yaya tsarin yake aiki? Idan Ba’isra’ila ya kashe wani cikin tsausayi, sai ya gudu zuwa biranen mafaka. Bayan alƙalai da suka ƙware sun yanke shari’a, mutumin da ya yi kisan zai zauna a birnin mafaka har sai bayan mutuwan babban firist. Sai ya sami ’yancin zama inda ya ga dama. Wannan kyakkyawan misali ne na jin ƙan Allah da kuma yadda yake ɗaukan rai da tamani. A yau abin da ya yi kama da wannan biranen mafaka shi ne tanadi na Allah, da ke bisa hadayar fansa na Kristi, don ya kāre mu daga mutuwa don ƙeta dokar Allah game da tsarkakar rai da kuma  jini. Kana ɗaukan wannan tanadi da tamani kuwa? Ta yaya za ka nuna cewa kana yin haka? Wata hanya ita ce ta wajen gayyatar wasu su riƙa amfani da tanadodin da Allah yake yi mana don mafaka, musamman ma domin “ƙunci mai-girma” da ke zuwa da wuri.—Matta 24:21; 2 Korintiyawa 6:1, 2.

KA ƊAUKI RAI DA TAMANI TA WAJEN WA’AZIN BISHARAR MULKI

26-28. A wace hanya ce yanayinmu a yau ya yi kama da na annabi Ezekiel, kuma ta yaya za mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah?

26 Yanayin mutanen Allah a yau ya tuna mana da annabin dā Ezekiel, wanda Jehobah ya umurce shi ya kasance mai tsaro na ruhaniya a gidan Isra’ila. Allah ya ce: “Ka ji magana ga bakina ka yi masu faɗaka daga gareni.” Idan Ezekiel ya yi watsi da aikinsa, zai kasance da alhakin jinin waɗanda aka kashe sa’ad da aka yi wa Urushalima shari’a. (Ezekiel 33:7-9) Amma Ezekiel ya kasance mai biyayya ne kuma saboda haka bai jawo wa kansa alhakin jini ba.

27 A yau, muna fuskantar ƙarshen dukan duniyar Shaiɗan. Saboda haka, ga Shaidun Jehobah hakki ne kuma gata ne su sanar da “ranar sakaiya” ta Allah tare da saƙon Mulki. (Ishaya 61:2; Matta 24:14) Kana saka hannu sosai a wannan aiki mai muhimmanci kuwa? Manzo Bulus ya ɗauki aikinsa na wa’azi da muhimmanci. Domin haka ya ce: “Ni kuɓutace ne daga jinin dukan mutane. Gama ban ji nauyin bayana maku dukan shawarar Allah” ba. (Ayukan Manzanni 20:26, 27) Wannan misali ne mai kyau da ya kamata mu yi koyi da shi!

28 Hakika, domin mu tsare kanmu cikin ƙaunar Jehobah Ubanmu mai ƙauna, muna bukatar mu yi fiye da ɗaukan rai da jini kamar yadda Jehobah yake ɗaukansu. Muna bukatar mu kasance da tsabta, ko kuma da tsarki, a gabansa, kamar yadda za mu gani a babi na gaba.

^ sakin layi na 5 Game da furcin Allah, “ran nama yana cikin jini” littafin nan Scientific American ya ce: “Idan aka ƙyale muhimmancinsa na alama, wannan furci gaskiya ne: ana bukatar kowane ƙwayar rai da ke cikin jini domin rayuwa.”

^ sakin layi na 12 Dubi Awake! na Agusta 2006, shafuffuka na 3-12, Shaidun Jehobah ne suka buga.

^ sakin layi na 16 Masanan kalmomin Littafi Mai Tsarki sun ce kalmomin Ibraniyawan “sun ce ba zai yiwu mutum ya ce ai wannan yana maganar rauni kawai da aka ji wa macen ba.” Kuma ka lura cewa Littafi Mai Tsarki bai ce kome ba game da shekarun da tayin zai yi kafin ya shafi hukuncin Jehobah ba.

[Hoto a shafi na 83]

 Ta yaya zan yi wa likita bayani game da shawarata ta karɓan ɓangarorin jini?

^ sakin layi na 72  Domin ƙarin bayani dubi Rataye, shafuffuka na 215-216.