Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 11

“Aure Shi Zama Abin Darajantuwa”

“Aure Shi Zama Abin Darajantuwa”

“Ka yi murna da matar kuruciyarka.”—MISALAI 5:18.

1, 2. Wace tambaya ce za mu amsa, kuma me ya sa?

KANA da aure? Aurenka abin farin ciki ne, ko kuma kana fuskantar matsaloli masu tsanani a aure? Kai da matarka kun raba gari ne? Kana jimre rayuwar aure ne kawai amma ba ka jin daɗinsa? Idan haka ne, to wataƙila kana baƙin ciki domin ba ka samun irin farin cikin da a dā kake morewa a aure. Hakika da yake kai Kirista ne, kana so aurenka ya daraja Jehobah, Allah da kake ƙauna. Saboda haka, yanayinka na yanzu zai kasance abin damuwa ne da ɓacin rai a gareka. Ko ma haka ne, kada ka ga cewa yanayinka ba shi da wata makawa.

2 A yau, da ma’aurata Kiristoci da a dā suna zama ne tare kawai babu farin ciki. Duk da haka, sun sami hanyar ƙarfafa dangantakarsu. Kai ma za ka sami gamsuwa a aurenka. Ta yaya?

KUSANTAR ALLAH DA KUMA ABOKIYAR AURENKA

3, 4. Me ya sa mata da miji za su kusaci juna idan suka yi ƙoƙari su kusaci Allah? Ka kwatanta.

3 Kai da abokiyar aurenka za ku kusaci juna idan kuka kusaci Allah. Me ya sa? Ka yi la’akari da wannan kwatanci: Ka yi tunanin dutsen da kansa yake da tsini, gindinsa kuma yake da faɗi. Miji yana tsaye a gindin  dutse a gefen arewa matar kuma tana tsaye a gindin dutsen a gefen kudu. Sai suka fara hawa. Sa’ad da dukansu suke kusa da gindin dutse, da akwai rata babba a tsakaninsu. Duk da haka, sa’ad da suka ci gaba da hawa zuwa kan dutsen, ratar da ke tsakaninsu za ta ci gaba da raguwa. Ka fahimci darassi mai ƙarfafawa a wannan kwatanci?

4 Za a iya kwatanta ƙoƙari da kuke yi wajen bauta wa Jehobah sosai da ƙoƙarin hawan dutse. Tun da kuna ƙaunar Jehobah, za a ce kuna ƙoƙarin hawa. Idan kai da abokiyar aurenka kun raba gari, zai kasance kuna hawa ne daga ɓangarori biyu na dutsen. Menene zai faru idan kuka ci gaba da hawa? Hakika, da farko  ɗan rata za ta kasance a tsakaninku. Duk da haka, yayin da kuke ƙara ƙoƙartawa ku kusaci Jehobah, wato, ta wajen hawan sama a alamance, hakan zai sa kai da matarka ku kusaci juna. Hakika, kusantar Allah shi ne mabuɗin kusantar juna. Amma ta yaya za ku iya yin hakan?

Idan ka yi amfani da ita, hikimar Littafi Mai Tsarki tana da ikon ƙarfafa aurenka

5. (a) Wace hanya ɗaya ce za a kusanci Jehobah da kuma abokiyar aure? (b) Yaya Jehobah yake ɗaukan aure?

5 Wata hanya ɗaya mai muhimmanci na hawan sama a alamance, ita ce, kai da matarka ku bi shawarar da ke cikin Kalmar Allah game da aure. (Zabura 25:4; Ishaya 48:17, 18) Saboda haka, ga wani takamaiman gargaɗi da manzo Bulus ya bayar. Ya ce: “Aure shi zama abin darajantuwa a wajen dukan mutane.” (Ibraniyawa 13:4) Menene wannan yake nufi? Kalmar nan ‘daraja’ tana nufin girmama wani abu, kuma abin yana da tamani. Haka Jehobah yake ɗaukan aure, yana da tamani a gare shi.

ƘAUNARKA GA JEHOBAH CE TAKE MOTSA KA

6. Menene mahalli na gargaɗin Bulus game da aure ya nuna, kuma me ya sa yake da muhimmanci a tuna hakan?

6 Hakika da yake kai bawan Allah ne, kai da matarka kun riga kun sani cewa aure yana da tamani, har ma da tsarki. Jehobah ne da kansa ya kafa tsarin aure. (Karanta Matta 19:4-6) Amma, idan a yanzu kuna fuskantar matsala a aure, sanin cewa aure yana da tamani kawai ba zai motsa kai da abokiyar aurenka ku nuna daraja da ƙauna ga juna ba. To, menene, zai motsa ku ku yi haka? Ka lura da yadda Bulus ya tunkari wannan batu na ba da daraja. Bai ce, ‘aure yana da daraja ba’; maimakon haka, ya ce, ‘aure shi zama abin darajantuwa.’ Ba abin da Bulus ya gani ba ne ba kawai yake faɗa; amma yana ba da gargaɗi  ne. * Tuna wannan bambanci zai taimaka wajen ba da ƙarin dalili na sake daraja abokiyar aurenka. Me ya sa ya kasance haka?

7. (a) Waɗanne dokoki ne na Nassi muke bi, kuma me ya sa? (b) Menene sakamakon biyayya?

7 Ka ɗan yi tunanin yadda kake ɗaukan wasu dokoki na Nassi, kamar su dokar almajirantarwa ko kuma ta mu riƙa zuwa taro don mu bauta wa Allah. (Matta 28:19; Ibraniyawa 10:24, 25) Hakika, cika waɗannan dokoki wani lokaci zai iya zama ƙalubale. Mutane da kake yi musu wa’azi wataƙila su amsa da baƙar magana, ko kuma aikin da kake yi zai sa ka gaji har ma halartar taron Kirista ya kasance kokawa. Duk da hakan, ka ci gaba da wa’azin saƙon Mulki, kuma ka ci gaba da halartar taron Kirista. Babu wanda zai iya hana ka yin haka, har Shaiɗan da kansa! Me ya sa? Domin ƙaunarka ga Jehobah ya motsa ka ka yi biyayya ga dokokinsa. (1 Yohanna 5:3) Menene sakamakon haka? Yin wa’azi da halartan taro yana ba ka kwanciyar rai da farin ciki domin ka sani kana yin nufin Allah. Kuma hakan yana ƙarfafa ka. (Nehemiah 8:10) Wane darassi ne muka koya a nan?

8, 9. (a) Menene zai motsa mu mu yi biyayya ga gargaɗi mu daraja aure, kuma me ya sa? (b) Waɗanne abubuwa biyu ne za mu bincika yanzu?

8 Kamar yadda ƙaunarka mai zurfi ga Allah take motsa ka ka yi biyayya ga dokar yin wa’azi kuma ka halarci taro duk da matsaloli, haka nan ƙaunarka ga Jehobah ya kamata ta motsa ka ka yi biyayya ga gargaɗin Nassosi na sa “aure [naka] shi zama abin darajantuwa,” har a lokacin da haka ya kasance da wuya. (Ibraniyawa 13:4; Zabura 18:29; Mai-Wa’azi 5:4) Ƙari ga haka, kamar yadda ƙoƙarinka na fita wa’azi da kuma halartan taro yake kawo  albarka masu yawa daga Allah, hakan kuma Jehobah zai gan ƙoƙarinka na daraja aurenka kuma ya albarkace ka.—1 Tassalunikawa 1:3; Ibraniyawa 6:10.

9 To, ta yaya za ka sa aurenka ya kasance da daraja? Kana bukatar ka guje wa halaye da za su iya ɓata wannan shiri na aure. Ƙari ga haka, kana bukatar ka ɗauki matakai da za su ƙarfafa gamin auren.

KA GUJI FURCI DA KUMA HALI DA BA ZA SU DARAJA AURE BA

10, 11. (a) Wane hali ne ba ya daraja aure? (b) Wace tambaya ce ya kamata a yi tsakanin mata da miji?

10 Wata mace Kirista ta faɗi haka: “Na yi wa Jehobah addu’a domin ƙarfi ya taimake ni in jimre.” Jimre menene? Ta yi bayani: “Mijina yana mini baƙar magana. Ko da yake ba ni da tabo a jikina, amma kalmominsa masu ciwo, kamar su ‘Kin cika matsi!’ da kuma ‘Ba ki da amfani!’ suna sa ni baƙin ciki.” Wannan matar ta ambata wani batu mai muhimmanci a cikin aure, wato, baƙar magana.

11 Abin baƙin ciki ne ƙwarai sa’ad da ma’aurata a iyalin Kirista suka jefi juna da baƙaƙen maganganu, suna ji wa juna ciwo a zuciya da ba sa warkewa da wuri! A bayyane yake cewa, aure da ya cika da baƙaƙen maganganu ba shi da daraja. Yaya aurenka yake a wannan batun? Hanya ɗaya na sanin hakan shi ne ka tambayi matarka ko mijinki, “Yaya kalmomi na suke shafanki ko suke shafanka?” Idan abokiyar aurenka ko na ki ya ko ta ga cewa sau da yawa kalmominka ko na ki suna kawo baƙin ciki, dole ne a yi gyara.—Galatiyawa 5:15; karanta Afisawa 4:31.

12. Ta yaya bautar mutum za ta kasance banza a gaban Allah?

12 Ka tuna cewa yadda ka yi amfani da harshenka a cikin aure zai shafi dangantakarka da Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan kowane mutum yana aza kansa  mai-addini ne, shi kuwa ba ya kame harshensa ba amma yana yaudara zuciyatasa, addinin wannan banza ne.” (Yaƙub 1:26) Kalamanka suna shafan bautarka. Littafi Mai Tsarki bai yarda da ra’ayin cewa dukan abin da ya faru a gida ba shi da wani muhimmanci, muddin wani ya yi da’awar cewa yana bauta wa Allah. Don Allah kada ka yaudari kanka. Wannan batu ne mai tsanani. (Karanta 1 Bitrus 3:7) Kana iya kasancewa da kuzari da kuma iyawa, amma idan da gangan kana zaluntar matarka da kalmomi, ba ka daraja tsarin aure kuma bautarka za ta kasance banza a gaban Allah.

13. Ta yaya abokin aure zai iya jawo baƙin ciki?

13 Ya kamata ma’aurata su kasance a faɗake domin kada su jawo baƙin ciki a kaikaice. Ga wasu misalai biyu: Wata gwauruwa tana yawan kiran wani ɗan’uwa a ikilisiya domin ta nemi shawara a wurinsa, kuma sai su yi doguwar hira; wani ɗan’uwa marar aure yana fitan wa’azi na dogon lokaci kowane mako da ’yar’uwa da take da aure. Wataƙila waɗannan ma’aurata da aka ambata a waɗannan misalan suna da kyakkyawar niyya; duk da haka, yaya abin da suke yi yake shafan abokan aurensu? Wata mata da ta fuskanci irin wannan yanayi ta ce: “Sanin cewa mijina yana ba da lokaci mai yawa ga wata ’yar’uwa a cikin ikilisiya yana damu na. Yana sa na ji ba ni da muhimmanci.”

14. (a) Wane hakkin aure ne aka nuna a Farawa 2:24? (b) Menene ya kamata mu tambayi kanmu?

14 Dalilin da ya sa wannan matar da wasu da suke fuskantar irin wannan yanayi suke baƙin ciki a bayyane yake. Mazansu sun yi watsi da ainihin umurnin da Allah ya ba da na aure: ‘Mutum za ya rabu da ubansa da uwatasa, ya manne ma matatasa: za su zama nama ɗaya kuma.’ (Farawa 2:24) Hakika, waɗanda suka yi aure za  su daraja iyayensu; amma, tsarin Allah ne cewa ainihin hakkinsu ga matansu ne. Hakika, Kiristoci suna ƙaunar ’yan’uwansu masu bi ƙwarai; amma hakkinsu na farko yana ga matansu ne. Saboda haka, idan Kirista da yake da aure yana ba da lokaci mai yawa ga wata ko kuma ya shaƙu da wata ’yar’uwa, zai jawo damuwa cikin aure.  Shin hakan ne ke jawo tashin hankali a aurenka? Ka tambayi kanka, ‘Ina ba matata lokaci da ƙauna da take bukata kuwa?’

15. In ji Matta 5:28, me ya sa ya kamata Kiristoci da suke da aure su guji ba da lokaci mai yawa ga wasu maza ko mata?

15 Bugu da ƙari, Kiristoci ma’aurata da suka ba da lokaci da bai dace ba ga wasu maza ko mata waɗanda ba matansu ko mazansu ba ne, suna saka kansu ne cikin haɗari. Abin baƙin ciki, wasu Kiristoci da suke da aure suna soma soyayya da wasu da suka shaƙu sosai. (Matta 5:28) Irin wannan, kuma yana kai ga halaye da ba sa daraja aure. Ka yi la’akari da abin da Bulus ya ce game da wannan batu.

“GADO KUMA SHI KASANCE MARA-ƘAZANTA”

16. Wane umurni ne Bulus ya bayar game da aure?

16 Bayan da Bulus ya ba da gargaɗi na “aure shi zama abin darajantuwa,” nan da nan ya daɗa wannan gargaɗin: “Gado kuma shi kasance mara-ƙazanta: gama da fasikai da mazinata Allah za shi shar’anta.” (Ibraniyawa 13:4) Bulus ya yi amfani da “gado” a madadin jima’i. Irin waɗannan saduwa ba su da “ƙazanta,” idan ta kasance a cikin tsarin aure ne kawai. Saboda haka, Kiristoci suna bin kalmomin da aka hure: “Ka yi murna da matar kuruciyarka.”—Misalai 5:18.

17. (a) Me ya sa Kiristoci ba sa yarda ra’ayin duniya game da zina ta rinjaye su? (b) Ta yaya za mu bi misalin da Ayuba ya kafa?

17 Waɗanda suke yin jima’i da wadda ba su aura ba suna ƙeta dokar Allah ta ɗabi’a. Hakika, mutane da yawa a yau suna ɗaukan zina abu ne da za a ɗan amince da shi. Duk da haka, ko yaya wasu mutane suke ɗaukan zina kada hakan ya rinjayi yadda Kirista yake ɗaukanta. Sun fahimci cewa a ƙarshe, ba mutum ba ne  amma ‘Allah ne za shi shar’anta mazinata.’ (Ibraniyawa 10:31; 12:29) Saboda haka, Kiristoci na gaskiya suna manne wa ra’ayin Jehobah a kan wannan batu. (Karanta Romawa 12:9) Ka tuna cewa Ayuba ya ce: “Na yi wa’adi da idanuna.” (Ayuba 31:1) Hakika, domin su guje wa takun farko da zai iya kai ga zina, Kiristoci na gaskiya suna kame idanunsu kuma ba sa yi wa wata da ba matarsu ko kuma mijinsu kallon sha’awa ba.—Dubi Rataye, shafi na 219-221.

18. (a) A gaban Allah, yaya tsananin zina? (b) Wane kamani ne ke tsakanin zina da bautar gumaka?

18 Yaya tsananin zina yake a gaban Jehobah? Dokar Musa ta taimake mu mu ga yadda Jehobah yake ji game da wannan? A Isra’ila, sakamakon zina da kuma bautar gumaka mutuwa ce. (Leviticus 20:2, 10) Ka ga kamannin da ke tsakanin abubuwan biyu? Ba’isra’ile da yake bauta wa gunki ya karya alkawarinsa da Jehobah. Hakazalika, Ba’isra’ile da ya yi zina ya karya alkawarinsa da matarsa. Dukansu sun ci amana. (Fitowa 19:5, 6; Kubawar Shari’a 5:9; karanta Malachi 2:14.) Saboda haka, dukansu suna da hakki a gaban Jehobah, Allah mai aminci abin dogara.—Zabura 33:4.

19. Menene zai ƙarfafa mutum ya ƙi zina, kuma me ya sa?

19 Hakika, Kiristoci ba sa ƙarƙashin Dokar Musa. Duk da haka, tuna cewa a Isra’ila ta dā, zina zunubi ne mai tsanani zai iya ƙarfafa Kiristoci kada su yi hakan. Me ya sa? Ka yi la’akari da wannan gwadi: Za ka taɓa shiga coci, ka sunkuya, ka yi addu’a a gaban gunki? Za ka ce, “Allah ya sawwaƙe!” Amma za ka so ka yi haka idan aka ba da kuɗi mai yawa? Za ka amsa, ‘ba zan taɓa ba yin haka ba!’ Hakika, tunanin cin amanar Jehobah ta wajen bauta wa gunki tana da ban ƙyama ga Kiristoci na gaskiya. Hakazalika, ya kamata Kiristoci su yi ƙyamar tunanin  cin amanar Allahnsu, Jehobah, da kuma matansu ta wajen yin zina, ko da menene dalilin yin zunubin. (Zabura 51:1, 4; Kolossiyawa 3:5) Kuma ba ma so mu yi aikin da zai sa Shaiɗan ya yi farin ciki kuma mu rena Jehobah da kuma tsarin aure.

YADDA ZA A ƘARFAFA GAMIN AURE

20. Menene ya faru a wasu aure? Ka kwatanta.

20 Ƙari ga guje wa halin da ba zai daraja aure ba, wane mataki za ka ɗauka domin ka sabonta daraja ga matarka ko mijinki? Domin mu amsa, ka yi tunanin cewa tsarin aure gida ne. Sai kuma, ka yi tunanin kalmomi masu daɗi, ayyukan kirki, da kuma wasu hanyar ba da daraja ga juna kamar yadda kayayyakin adon suke ƙara wa gida kyau. Idan kuka kusaci juna, aurenku zai yi kama da gida mai ado mai kyau. Idan ƙaunarku ta ragu, waɗannan kayan ado a hankali za su ɓace, su bar aurenku kamar gida da ba shi da kayan ado. Tun da kana so ka bi dokar Allah ka sa “aure shi zama abin darajantuwa,” za ka yi ƙoƙari ka yi gyara. Ban da haka ma, ya dace a gyara abin da ke da daraja da tamani. Ta yaya za ka yi hakan? Kalmar Allah ta ce: “An gina gidaje a kan harsashin hikima da fahimi. Ta wurin ilimi a kan ƙawata ɗakuna da kyawawan kayayyaki masu tamani.” (Misalai 24:3, 4, Littafi Mai Tsarki) Ka yi la’akari da yadda za ka yi amfani da waɗannan kalmomi a aurenka.

21. Ta yaya za mu ƙarfafa aurenmu a hankali? (Dubi akwatin da ke  shafi na 131.)

21 “Kayayyaki masu tamani” da suka cika iyali mai farin ciki sun haɗa da ƙauna ta gaskiya, tsoron Allah, da kuma bangaskiya mai ƙarfi. (Misalai 15:16, 17; 1 Bitrus  1:7) Suna ƙarfafa aure. Amma ka lura da yadda ɗakuna da aka yi ƙaulinsa a littafin misalai na baya suke cike da abubuwa masu tamani? “Ta wurin hikima.” Hakika, idan aka yi amfani da ita, hikimar Littafi Mai Tsarki tana da ikon canja tunanin mutane kuma ta motsa su su sabonta ƙaunarsu ga juna. (Romawa 12:2; Filibbiyawa 1:9) Saboda haka, duk lokacin da kai da matarka kuka zauna tare kuna bincika ayar Littafi Mai Tsarki, kamar su nassosin yini, ko kuma wani talifi na Hasumiyar Tsaro ko kuma Awake! game da aure, zai zama kamar kuna duba wani ado ne mai kyau da zai iya kyawanta gidanku. Sa’ad da ƙaunar Jehobah ta motsa ku ku yi amfani da gargaɗi da kuka tattauna, kamar dai kuna kai wannan kayan ado cikin ɗakinku ne. Domin wannan, farin ciki da kwanciyar hankali da kuke da su a aurenku a dā zai komo.

22. Wace gamsuwa ce za mu samu idan muka yi ƙoƙari muka yi namu ɓangare wajen ƙarfafa aurenmu?

22 Hakika, zai ɗauki ɗan lokaci da ƙoƙari a jera waɗannan kayan ado a wuraren da suke a dā. Duk da haka, idan ka yi ƙoƙari ka yi naka ɓangaren, za ka sami gamsuwa ta sanin cewa kana yin biyayya ga dokar Allah da ta ce: ‘Ku gabatar da juna cikin bangirma.’ (Romawa 12:10; Zabura 147:11) Fiye da kome, ƙoƙarin da kake yi na daraja aurenka zai tsare ka cikin ƙaunar Allah.

^ sakin layi na 6 Mahallin ya nuna cewa gargaɗin Bulus game da aure ɓangare ne na gargaɗi masu yawa.—Ibraniyawa 13:1-5.