Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 10

Aure, Kyauta ne Daga Allah Mai Kauna

Aure, Kyauta ne Daga Allah Mai Kauna

“Igiya riɓi uku kuma ba shi tsunkuwa da sauri ba.”—MAI-WA’AZI 4:12.

1, 2. (a) Game da sabon aure, menene wani lokaci muke tunani a kai kuma me ya sa? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan babin?

KANA son zuwa bikin aure? Mutane da yawa suna so, domin irin wannan biki yana iya ba da farin ciki. Za ka ga ma’auratan sun yi ado da kyau. Fiye da haka ma, fuskokinsu suna cike da farin ciki! A wannan rana, su kam sai murmushi, kuma rayuwarsu ta nan gaba tana cike da bege.

2 Duk da haka, dole ne a yarda cewa a hanyoyi da yawa aure a yau cike yake da matsaloli. Ko da yake muna fatan sababbin ma’aurata su sami farin ciki, amma wani lokaci sai mu yi tunani: ‘Za su sami farin ciki kuwa a wannan auren? Zai daɗe kuwa?’ Amsoshin waɗannan tambayoyin sun dangana ne ga mata da mijin ko za su dogara ga gargaɗin Allah kuma su yi amfani da shi a aurensu. (Karanta Misalai 3:5, 6) Suna bukatar su yi haka idan suna so su tsare kansu cikin ƙaunar Allah. Bari yanzu mu mai da hankali ga amsoshin Littafi Mai Tsarki ga waɗannan tambayoyi huɗu: Me ya sa za ka yi aure? Idan za ka yi aure, wa za ka zaɓa ka aura? Ta yaya za ka yi shirin aure? Kuma menene zai taimaki ma’aurata su kasance da farin ciki a aurensu?

ME YA SA ZA KA YI AURE?

3. Me ya sa ba zai kasance hikima ba a yi aure domin dalilai marar muhimmanci?

3 Wasu sun gaskata cewa aure yana da muhimmanci  don samun farin ciki, sun ce ba za ka gamsu ba ko kuma ka sami farin ciki idan ba ka yi aure ba. Hakika hakan ba gaskiya ba ne! Yesu da ba shi da aure ya yi maganar rashin aure cewa kyauta ce kuma ya aririci waɗanda za su iya, kada su yi aure. (Matta 19:11, 12) Manzo Bulus ya faɗi muhimmancin rashin aure. (1 Korintiyawa 7:32-38) Yesu da Bulus ba su kafa doka ba game da wannan; hakika, an lissafa “hana aure” cikin “koyarwar aljannu.” (1 Timothawus 4:1-3) Duk da haka, rashin aure zai ba wa waɗanda suke so su bauta wa Jehobah ba tare da raba hankali ba damar yin haka. Saboda haka, ba hikima ba ce, a yi aure domin wasu dalilai marar muhimmanci, ko kuma domin matsi na tsara.

4. Aure mai kyau yana kafa wane harsashi ne domin renon yara?

4 A wani ɓangare kuma, da dalilai masu muhimmanci na yin aure? E. Aure ma kyauta ne daga Allah. (Karanta Farawa 2:18) Saboda haka yana iya ba da farin ciki da kuma albarkatai. Alal misali, aure mai kyau shi ne harsashi mai kyau domin rayuwar iyali. Yara suna bukatar yanayi mai kyau da kuma iyaye domin su yi renonsu, su nuna musu ƙauna, su yi horonsu kuma su yi musu ja-gora. (Zabura 127:3; Afisawa 6:1-4) Amma kuma, ba renon yara ba ne kawai dalilin yin aure.

5, 6. (a) In ji Mai-Wa’azi 4:9-12, menene wasu albarkatai na abota ta kusa? (b) Ta yaya aure zai kasance kamar igiya riɓi uku?

5 Ka duba nassin jigon wannan babi da abin da ke cikinsa: “Gwamma biyu da ɗaya; domin suna da arziki cikin aikinsu. Gama idan sun fāɗi, ɗaya za ya ɗaga ɗan’uwansa: amma kaiton wanda shi ke shi kaɗai sa’anda ya fāɗi, ba shi da wanda za ya tashe shi. Kuma idan biyu sun kwanta wuri ɗaya, za su ji ɗumi; amma ƙaƙa mutum shi ɗaya za ya ji ɗumi? Kuma idan mutum ya rinjayi wanda shi ke shi kaɗai, biyu za su iya tsaya masa; igiya riɓi uku kuma ba shi tsunkuwa da sauri ba.”—Mai-Wa’azi 4:9-12.

 6 Ainihin ma’anar wannan nassi don abokantaka ne. Aure kuma, shi ne abota da ya fi kusa. Kamar yadda wannan nassin ya nuna, wannan gami zai ba da taimako, kwanciyar hankali, da kāriya. Aure zai fi ƙarfi idan ba gami ba ne kawai tsakanin mutane biyu. Kamar yadda wannan ayar ta nuna za a iya tsinka igiya riɓi biyu. Amma idan aka tuƙa igiya uku zai yi wuyan tsinkewa. Idan faranta wa Jehobah rai shi ne ainihin abin da ya dami mata da miji, aurensu zai kasance kamar wannan igiya riɓi uku. Jehobah zai kasance yana cikin aure saboda haka gamin zai kasance da ƙarfi sosai.

7, 8. (a) Wane gargaɗi ne Bulus ya rubuta wa Kiristoci marasa aure da suke kokawa da sha’awa ta jima’i? (b)Wace gaskiya ce Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da aure?

7 Cikin aure ne kawai za a iya gamsar da sha’awa ta jima’i daidai. Za a iya ɗaukan jima’i abin da ke kawo farin ciki a wannan yanayin. (Misalai 5:18) Idan mutum marar aure ya wuce abin da Littafi Mai Tsarki ya kira “wuce lokaci,” wato, lokacin da sha’awar jima’i da fari take yin ƙarfi sosai, shi ko ita har ila zai ko za ta riƙa kokawa da sha’awa ta jima’i. Idan ba a kame kai ba, irin wannan sha’awa za ta iya kai wa ga hali marar tsabta ko wanda bai dace ba. An huri Bulus ya rubuta wannan gargaɗi ga marasa aure: “Idan ba su da daurewa, su yi aure; gama da a ƙuna gwamma a yi aure.”—1 Korintiyawa 7:9, 36; Yaƙub 1:15.

8 Ko da wane dalili ne ya motsa mutum ya yi aure, yana da kyau ya san ainihin abin da zai fuskanta. Kamar yadda Bulus ya faɗa, waɗanda suka yi aure “za su sha wahala a cikin jiki.” (1 Korintiyawa 7:28) Mutane da suka yi aure za su fuskanci ƙalubale da waɗanda ba su yi aure ba ba za su fuskanta ba. Idan ka zaɓi ka yi aure, ta yaya za ka rage ƙalubalan kuma ka ƙara albarkar? Hanya ɗaya ita ce ka zaɓi wadda za ka aura cikin hikima.

 WANENE ZAI KASANCE ABOKI MAI KYAU NA AURE?

9, 10. (a) Ta yaya Bulus ya kwatanta haɗari na ƙulla abota na kud da kud da marasa bangaskiya? (b) Menene sau da yawa sakamakon ƙin bin gargaɗin Allah game da auren marasa bangaskiya?

9 An huri manzo Bulus ya rubuta wani mizani mai muhimmanci da za a yi amfani da shi sa’ad da ake zaɓan abokin aure: “Kada ku yi karkiya marar-dacewa tare da marasa-bangaskiya.” (2 Korintiyawa 6:14) Wannan kwatanci yana bisa rayuwa ce ta manoma. Idan aka yi wa dabbobi biyu da suka bambanta a girmansu ko kuma a ƙarfinsu karkiya tare, dukansu za su wahala. Hakazalika, idan aka haɗa, mai bi da marar bi a aure, babu wata shakka za su sami rashin jituwa. Idan ɗaya yana so ya tsare kansa cikin ƙaunar Jehobah kuma ɗayan hakan bai dame ta ba, abin da ya fi muhimmanci a rayuwarsu zai bambanta, kuma hakan zai jawo rashin jin daɗi. Saboda haka Bulus ya aririci Kiristoci su yi aure “sai dai cikin Ubangiji.”—1 Korinthiyawa 7:39.

10 A wasu yanayi, Kiristoci marasa aure sukan kammala cewa karkiya marar dacewa ta fi irin kewa da suke ji a yau. Wasu sukan ƙeta gargaɗin Littafi Mai Tsarki, kuma su auri mutumin da ba ya bauta wa Jehobah. Sau da yawa, sakamakon haka abin baƙin ciki ne. Irin waɗannan sukan auri mutumin da ba za su iya taɗi game da abubuwa mafi muhimmanci a rayuwa ba. Kewar da za su fuskanta zai fi wanda suka ji kafin su yi auren. Abin farin ciki, da akwai dubban Kiristoci marasa aure da suka dogara ga gargaɗin Allah kuma suna manne masa cikin aminci game da wannan. (Karanta Zabura 32:8) Ko da yake suna da begen yin aure wata rana, suna kasance marasa aure har sai sun sami abokin aure tsakanin waɗanda suke bauta wa Jehobah Allah.

11. Menene zai taimake ka ka zaɓi abokiyar aure cikin hikima? (Dubi akwatin da ke  shafi na 114.)

11 Hakika, ba kowanne bawan Jehobah ba ne zai kasance  abokin aure da ya dace ba. Idan kana da niyyar aure, ka nemi wadda mutumtakarta, makasudinta na ruhaniya, da kuma ƙaunarta ga Allah sun dace da na ka. Bawan nan mai aminci ya yi tanadin abubuwa da yawa game da wannan batun, kuma ya kamata ka bi wannan gargaɗi na Nassosi da addu’a, kuma ka ƙyale wannan ya yi maka ja-gora wajen yanke wannan shawarar mai muhimmanci. *Karanta Zabura 119:105.

12. Wace al’ada ce game da aure har yanzu ake bi a wasu ƙasashe, kuma wane misali ne Littafi Mai Tsarki ya ba da ja-gora?

12 A ƙasashe da yawa, al’ada ce iyaye su zaɓa wa ’yarsu miji. A irin waɗannan al’adun ana ganin cewa iyaye sun fi hikima kuma sun san abubuwa da ake bukata domin yin irin wannan zaɓe mai muhimmanci. Irin wannan aure yakan yi nasara kamar yadda ya kasance a lokacin dā. Misalin Ibrahim da ya aiki bawansa ya nemi wa Ishaku mata, darassi ne mai kyau ga iyayen da suke cikin irin wannan yanayi a yau. Kuɗi da kuma martaba ba su dami Ibrahim ba. Maimakon haka, ya je ya nemi mata wa Ishaku tsakanin mutanen da suke bauta wa Jehobah. *Farawa 24:3, 67.

TA YAYA ZA KA YI SHIRI DOMIN AURE DA ZAI YI NASARA?

13-15. (a) Ta yaya mizani da aka samu a Misalai 24:27 zai taimaki samari da suke tunanin aure? (b) Menene budurwa za ta yi don ta yi shirin aure?

13 Idan kana tunanin aure sosai, ya kamata ka tambayi  kanka, ‘Na shirya kuwa?’ Amsar ba ta dangana game da yadda kake ji game da soyayya, jima’i, abota, ko kuma renon yara ba. Maimakon haka, da wasu makasudai da kowane namiji ko mace da suke so su yi aure ya kamata su yi tunani a kai.

14 Saurayi da yake neman matar da zai aure ya kamata ya yi tunani wannan mizani da kyau: “Ka shirya aikinka a waje, Ka shirya ma kanka kuma cikin gona; Daga baya kuma ka gina gidanka.” (Misalai 24:27) Menene ake nufi a nan? A zamanin dā, idan mutum yana so ya ‘gina gidansa,’ ko kuma ya kafa iyali ta wajen yin aure, yana bukatar ya tambayi kansa, ‘Ina shirye in kula kuma in taimaki matata da kuma yara da za mu haifa?’ Yana bukatar ya yi aiki tukuna, ya kula da gonarsa, ko kuma shuki. Haka mizanin yake a yau. Mutumin da yake so ya yi aure yana bukatar ya shirya domin wannan hakkin. Idan yana iya aiki, dole ne ya yi aiki. Kalmar Allah ta nuna cewa mutumin da bai kula da bukatun zahiri, motsin rai, da kuma na ruhaniyar iyalinsa ba gwamma marar bangaskiya da shi!—Karanta 1 Timothawus 5:8.

15 Mace da ta tsai da shawara za ta yi aure ma za ta cika wasu hakki masu nauyi. Littafi Mai Tsarki ya ambata wasu halaye da mace za ta bukaci domin taimakon mijinta wajen kula da gidansu. (Misalai 31:10-31) Maza da mata da suka shiga aure ba tare da shirin ɗaukan waɗannan hakkin da aure ya ƙunsa ba suna nuna son kai ne, ba sa tunani game da abin da za su bai wa wanda za su aura ba. Mafi muhimmanci ma, ya kamata waɗanda suke shirin aure su bi ka’idodin Littafi Mai Tsarki a rayuwarsu.

16, 17. Waɗanne mizanai na Nassi ne ya kamata waɗanda suke shirin aure su yi bimbini a kai?

16 Shirin aure ya ƙunshi bimbini bisa aikin da Allah ya  ba wa mata da miji. Namiji yana bukatar ya san abin da shugabancin iyali na Kirista yake nufi. Wannan matsayi ba izini ba ne domin cin zali. Maimakon haka, dole ne ya yi koyi da yadda Yesu ya nuna shugabancinsa. (Afisawa 5:23) Haka ma, mace Kirista tana bukatar ta fahimci matsayinta mai martaba. Za ta kasance a shirye ta miƙa kanta ga “shari’ar mijin”? (Romawa 7:2) Tana ƙarƙashin dokar Jehobah da kuma ta Kristi. (Galatiyawa 6:2) Ikon mijinta a cikin iyali ya kasance wata shari’a ce. Za ta kasance mai tallafawa kuma mai miƙa kai idan ya zo ga ikon mutum ajizi? Idan ba ta son wannan, to, ya fi kyau kada ta yi aure.

17 Bugu da ƙari, kowane abokin aure ya kamata ya kasance a shirye domin ya biya bukatu na musamman na abokin aure. (Karanta Filibbiyawa 2:4) Bulus ya rubuta: “Kowane ɗayanku shi yi ƙaunar matatasa kamar kansa; matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.” Da yake Allah ne ya huri Bulus, ya fahimci cewa namiji yana da bukata ta musamman ya ga cewa matarsa tana girmama shi sosai. Ita kuma matar tana da bukata ta musamman ta ga cewa mijinta yana ƙaunarta.—Afisawa 5:21-33.

18. Me ya sa ya kamata masu zawarci su kame kansu?

18 Zawarci, ba lokaci ba ne kawai na nishaɗi da jin daɗi ba. Lokaci ne da mace da na miji za su koyi su yi cuɗanya da juna yadda ya dace, su ga ko aure zai yiwu. Kuma lokaci ne na kame kai! Son su kasance kusa da juna zai yi ƙarfi sosai, saboda haka, ba laifi ba ne su nuna wa juna soyayya. Duk da haka, waɗanda suke ƙaunar juna da gaske za su guji dukan wani abun da zai cutar da wanda suke ƙauna a ruhaniya. (1 Tassalunikawa 4:6) Saboda haka, idan kana zawarci, ka kame kai; za ka amfana daga wannan hali a dukan rayuwarka, ko ka yi aure ko ba ka yi ba.

Sa’ad da suke zawarci ma’aurata da yawa cikin hikima suna tafiya da ’ya ko ɗan rakiya

 TA YAYA ZA KA SA AURENKA YA DAWWAMA?

19, 20. Ta yaya ra’ayin Kirista game da aure ya kamata ya bambanta da na yawancin mutane a duniyar yau? Ka kwatanta.

19 Idan ma’aurata za su sa aurensu ya dawwama, suna bukatar su fahimci muhimmancin alkawari. A littattafai da kuma fina finai, aure yana ba da rayuwar farin ciki da mutane suke bukata. A rayuwa ta zahiri, aure ba shi ne ƙarshe ba; somawar abin da Jehobah ya tsara ne domin ya dawwama. (Farawa 2:24) Abin baƙin ciki, ba haka ake ɗaukansa ba a duniya ta yau. A wasu al’adu, mutane suna maganar aure “kamar igiya biyu ne da za a ɗaure.” Ba su fahimci yadda wannan ya kwatanta yadda mutane suke ɗaukan aure ba. Kamar yaya? Ko da yake ɗauri mai kyau ya kamata ya daɗe kamar yadda ake bukata, wani abu kuma da ake bukatar a sani shi ne, za a iya ɗaure da kuma kwance igiya cikin sauƙi.

20 Mutane da yawa a yau suna ɗaukan aure abu ne na ɗan lokaci. Suna yinsa ne domin suna gani zai biya bukatunsu, amma kuma suna shirin su kashe da zarar sun ga zai kawo musu ƙalubale. Amma ka tuna kwatanci da Littafi Mai Tsarki ya yi game da irin wannan gami na aure, cewa igiya ne. Igiya da aka yi domin fila-filan jirgin ruwa ana yinsu ne domin su jure, ba kawai su tsinke har a lokacin hadari mai ƙarfi ba. Hakazalika, an shirya aure ne domin ya jure. Ka tuna Yesu ya ce: “Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.” (Matta 19:6) Idan ka yi aure, kana bukatar ka kasance da irin wannan ra’ayin game da aure. Shin irin wannan alkawari yana mai da aure ya kasance kaya mai nauyi ne kawai? A’a.

21. Mata da miji suna bukatar su kasance da wane irin hali game da juna, kuma menene zai taimake su su yi haka?

21 Ya kamata mata da miji su kasance da ra’ayin da ya dace game da juna. Idan mata da miji suka mai da hankali ga halayensu na kirki da kuma ƙoƙarin da suke yi, aurensu  zai kasance abin farin ciki da wartsakewa. Yaudarar kai ne mata da miji su kasance da irin wannan ra’ayi game da kansu duk da cewa su ajizai ne? Jehobah a kullum ya san abin da ke daidai, shi ya sa muke dogara a gare shi ya ga halayenmu na kirki. Mai zabura ya yi tambaya: “Idan kai, ya Ubangiji, za ka ƙididdiga laifofi, wa za ya tsaya, ya Ubangiji?” (Zabura 130:3) Mata da miji ya kamata su kasance da irin wannan ra’ayi na gafarta wa juna.—Karanta Kolossiyawa 3:13.

22, 23. Ta yaya Ibrahim da Saratu suka kasance misali mai kyau ga ma’aurata a yau?

 22 Aure zai kasance albarka yayin da ya jure na shekaru masu yawa. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da auren Ibrahim da Saratu sa’ad da suka tsufa. Rayuwarsu ta ƙunshi ƙalubale da kuma wahala. Ka yi tunanin yadda ya kasance wa Saratu, matar da wataƙila ta wuce shekara 60, ta bar daɗin da take ji a gidanta a birnin Ur mai arziki kuma ta fara zama a cikin tanti. Duk da haka, ta miƙa kai ga shugabancin mijinta. Ta kasance mataimakiya ce ta gaske ga Ibrahim, cikin daraja ta taimaka domin mataki da ya ɗauka ya yi nasara. Kuma miƙa kanta ba na baki ba ne kawai. Har a “cikin ranta,” ta kira mijinta ubangijina. (Farawa 18:12; 1 Bitrus 3:6) Darajar da take ba Ibrahim ya fito ne daga cikin zuciyarta.

23 Hakika, wannan ba ya nufin cewa ko da yaushe ra’ayin Ibrahim da Saratu ɗaya ne. Ta taɓa ba da shawara da ya yi wa Ibrahim “ciwo ƙwarai.” Duk da haka, da Allah ya ba da umurni, cikin tawali’u, Ibrahim ya saurari abin da matarsa ta ce, kuma hakan ya kasance albarka ga iyalin. (Farawa 21:9-13) Mata da miji a yau, har waɗanda suka yi shekaru da aure, za su iya koyon wani abu daga waɗannan ma’aurata masu tsoron Allah.

24. Wane irin aure ne yake daraja Jehobah Allah, kuma me ya sa?

24 A ikilisiya ta Kirista, da akwai masu aure dubbai da suke farin ciki, wato, aure da mata suna daraja mazansu ƙwarai, mazan kuma suna ƙaunar matansu suna nuna musu bangirma, kuma duka suna aiki tare su saka yin nufin Jehobah farko a rayuwarsu. Idan ka yi niyyar aure, za ka iya zaɓan wadda za ka aure cikin hikima, ka yi shiri da kyau domin aure, kuma ka yi aiki domin auren ya zama mai ƙauna mai zaman lafiya da zai daraja Jehobah Allah. A wannan hanyar, aurenka babu shakka zai taimake ka ka tsare kanka cikin ƙaunar Allah.

^ sakin layi na 11 Dubi babi na 2 na littafin nan Asirin Farin cikin Iyali, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

^ sakin layi na 12 Wasu ubanni suna da fiye da mace ɗaya. Sa’ad da Jehobah ya yi sha’ani da ubanni da kuma Isra’ila ta zahiri, ya ƙyale auren fiye da mace ɗaya. Ba shi ya kafa ba, amma ya ƙyale. Amma, Kiristoci suna tuna cewa Allah bai ƙyale auren fiye da mace ɗaya tsakanin waɗanda suke bauta masa ba.—Matta 19:9; 1 Timothawus 3:2.