Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RATAYE

Abubuwan da Suka Zama Jini da Kuma Hanyoyin Fida

Abubuwan da Suka Zama Jini da Kuma Hanyoyin Fida

Abubuwa da suka zama jini. Waɗannan abubuwa ana samunsu ne daga abubuwa huɗu da suka haɗu suka zama jini, jajayen ƙwan halitta, farare, kamewar jini, da kuma ruwan jini. Alal misali, jajayen ƙwan halitta sun ƙunshi furotin da ake kira himoglobin. Ana amfani da magunguna da aka yi daga wannan himoglobin na mutane ko kuma na dabbobi wajen yi wa majiyyata da suke fama da rashin jini magani.

Ruwan jini, wanda kashi 90 ɗinsa ruwa ne, yana ɗauke da wasu sinadarai, gishiri, kayan gina jiki, sukari, da dai sauransu. Ruwan jini kuma ya ƙunshi abubuwa da suke sa jini ya daskare, ƙwayoyi masu yaƙi da cututtuka, irinsu furotin da ake kira albumin. Idan mutum yana da wani irin cuta, likita zai iya cewa a ba shi allurar da ake kira gamma-globulin wadda aka samo daga ruwan jinin mutanen da suke da kāriya ga wannan cutar. Ƙila an samo fararen ƙwan halitta daga interferons da kuma interleukins da ake amfani da su wajen magance wasu cututtuka masu tsanani da kuma ciwon daji.

Ya kamata Kiristoci su karɓi maganin da ya ƙunshi iri waɗannan abubuwa ne? Littafi Mai Tsarki bai ba da cikakken bayani ba, dole ne kowa ya yanke shawararsa a gaban Allah. Wasu za su ƙi dukan wani abu da ya fito daga jini, suna tunanin cewa Dokar Allah ga Isra’ila ta bukaci cewa a zubar  da jini da ya fita daga jikin halitta a “ƙasa.” (Kubawar Shari’a 12:22-24) Ko da yake wasu za su ƙi karin jini ko kuma karɓan waɗannan abubuwa huɗu da suka haɗu suka zama jini, suna iya amincewa da magani da ya ƙunshi sinadarai daga waɗannan abubuwa huɗu. Za su yi tunanin cewa irin waɗannan ba sa kuma wakiltan ran halitta da aka ɗauki jini daga jikinsa.

Sa’ad da za ka yanke shawara game da sinadari da aka samu daga abubuwa huɗu na jini, ka yi tunani a kan waɗannan tambayoyi: Na sani cewa ƙin dukan waɗannan sinadarai da aka samu daga jini yana nufin ba zan karɓi magunguna da suka ƙunshi waɗannan sinadarai domin magance wata cuta ko kuma domin hana jini zuba ta wajen sa jinin ya daskare ba? Zan iya yi wa likita bayanin dalilin da ya sa na ƙi ko na amince da amfani da ɗaya ko fiye da haka na abubuwa da suka zama jini?

Hanyoyin fiɗa. Wannan ya haɗa da hemodilution da cell salvage. Hemodilution yana nufin karkata hanyar jini daga jikin mutum, a sake shi da ruwan magani, sai daga baya a mai da hanyar jinin cikin jikin mutum. Cell salvage yana tare jini kuma ya mayar da shi cikin jikin mutum a lokacin fiɗa. Ana samun jini daga ciwo ko kuma wani rami na jiki, a wanke ko kuma a tace shi, sai kuma a mayar da shi cikin jikin mutum. Domin wannan tsarin ya bambanta daga likita  zuwa likita, ya kamata Kirista ya tambayi likitansa abin da yake nufi.

Sa’ad da kake yanke shawara game da wannan ka tambayi kanka: ‘Idan za a karkata hanyar jini daga jikina kuma a dakatar da tafiyar jinina na ɗan lokaci, lamiri na zai ƙyale ni in ɗauki wannan jinin a kan matsayin ɓangaren jiki na ne, saboda haka ba a bukatar a zubar da shi a “ƙasa”? (Kubawar  Shari’a 12:23, 24) Lamiri na da aka koyar da Littafi Mai Tsarki zai dame ni ne idan a lokacin fiɗa aka ja jinina aka haɗa da magani aka sake mayar a jikina? Na sani cewa idan na ƙi dukan wata hanyar magani da ta ƙunshi amfani da jinina, hakan yana nufin cewa ba zan yarda a gwada jinina ba, da kuma wasu hanyoyin yin magani?’

Dole ne Kirista ya yanke shawara wa kansa game da yadda za a bi da jininsa a lokacin fiɗa. Hakan kuma ya shafi gwaji da kuma wasu hanyoyin magani da za a ja jinin mutum, bayan an haɗa da wasu magunguna sai a mayar cikin jikin mutum.