Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wasika Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu

Wasika Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu

‘Ya kamata ku zama masu koyarwa.’ (Ibran. 5:12) Abin mamaki! Jehobah wanda ya fi kowane malami iya koyarwa ya ce mu riƙa koya wa mutane abubuwa game da shi! Koyar da mutane game da Jehobah a iyali da ikilisiya da kuma sa’ad da muke wa’azi babban gata ne kuma aiki ne mai muhimmanci sosai. Ta yaya za mu yi nasara a yin hakan?

Za a sami amsar tambayar a wasiƙar da Bulus ya rubuta wa Timoti cewa: “Ka ci gaba da karanta Rubutacciyar Maganar Allah wa jama’a, da yin wa’azi, da kuma yin koyarwa.” Bulus ya ƙara da cewa: “In ka yi haka, za ka ceci kanka da kuma masu jinka.” (1 Tim. 4:​13, 16) Saƙon da aka ba ku na ceton mutane ne. Don haka, yana da kyau ku yi iya ƙoƙarinku wajen kyautata yadda kuke karatu da kuma koyarwa. An shirya wannan ƙasidar don ta taimaka muku yin hakan. Ga wasu abubuwan da ke ciki.

Nassin da ke kowane shafi yana nuna ƙa’idar Littafi Mai Tsarki da ta yi daidai da darasin ko kuma yadda aka yi amfani da darasin a cikin nassin

Jehobah shi ne ‘Malamin’ malamai. (Isha. 30:20) Ko da yake wannan ƙasidar za ta taimaka muku ku kyautata yadda kuke karatu da koyarwa, kar ku manta cewa Jehobah ne ya ba mu saƙon kuma shi ne yake jawo mutane zuwa ƙungiyarsa. (Yoh. 6:44) Don haka, ku riƙa roƙan Jehobah ya ba ku ruhu mai tsarki don ya taimaka muku. Ku riƙa amfani da Kalmar Allah da kyau. Ku sa a ɗaukaka Jehobah, ba ku ba. Ku yi ƙoƙari ku taimaka wa masu sauraronku su ƙaunaci Jehobah sosai.

An ba ku gatan koya wa mutane Kalmar Allah. Muna da tabbaci cewa yayin da kuke dogara ga “ƙarfin da Allah ya bayar,” za ku yi nasara.​—1 Bit. 4:11.

Abokan Aikinku,

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah