Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 8

Misalai Masu Amfani

Misalai Masu Amfani

Matiyu 13:​34, 35

ABIN DA ZA KA YI: Ka inganta koyarwarka da misalai masu sauƙi da za su ratsa zuciyar masu sauraro. Misalan su koyar da darussa masu muhimmanci.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka yi amfani da misalai masu sauƙi. Kamar Yesu, ka yi amfani da misalan da mutane suka saba da su don ka bayyana musu gaskiya. Kar ka yi bayani mai yawa don kada misalin ya yi wuyar fahimta. Ka tabbata cewa misalin ya yi daidai da darasin da kake so su fahimta don kada ka raba hankalin masu sauraronka.

  • Ka yi tunani a kan abin da zai amfane masu sauraronka. Ka yi amfani da misalin da masu sauraronka suka saba da shi. Kada ka yi amfani da misalin da zai ɓata musu rai ko ya sa su ji kunya.

  • Ka koya musu ainihin darasin. Ka yi amfani da misalai don fitar da muhimman darussan da kake koyarwa. Ka tabbata cewa masu sauraro sun tuna darasin da suka koya daga misalin ba misalin kawai ba.