Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 7

Ka Koyar da Gaskiya

Ka Koyar da Gaskiya

Luka 1:3

ABIN DA ZA KA YI: Ka yi amfani da bayanai na gaskiya da za su taimaka wa masu sauraronka su fahimci batun.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka nemi bayanai na gaskiya. Bayaninka ya yi daidai da abin da ke Littafi Mai Tsarki, idan zai yiwu ka karanta wurin. Idan za ka yi magana a kan wani abu daga littafin kimiyya ko jarida ko labarin wani, ka tabbata cewa abin da kake so ka faɗa gaskiya ne.

  • Ka yi amfani da bayanan yadda ya dace. Don mu bayyana darassin da ke nassin da za mu karanta, muna bukatar mu fahimci abin da Jehobah yake so mu koya a ayar. Bayaninmu ya jitu da dukan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, da kuma littattafan “bawan nan mai aminci, mai hikima.” (Mat. 24:45) Idan ka ɗauko bayani daga wasu littattafan da ba na ƙungiyarmu ba, ka faɗi ainihin abin da suka ce.

  • Ka taimaka wa masu sauraronka su fahimci batun. Bayan ka karanta wani nassi ko kuma wani littafi, ka yi wa masu sauraronka tambaya ko kuma ka gaya musu wani kwatanci don ka taimaka musu su fahimci batun.