Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 4

Ka Gabatar da Nassi Yadda Ya Dace

Ka Gabatar da Nassi Yadda Ya Dace

Matiyu 22:​41-45

ABIN DA ZA KA YI: Ka sa masu sauraronka su yi marmarin nassin da kake so ka karanta kafin ka karanta shi.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka yi tunani a kan dalilin da ya sa kake so ka karanta nassin. Ka gabatar da nassin a hanyar da za ta sa masu sauraronka su ga bayanin da kake so ka fitar daga nassin.

  • Ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki. Idan kana magana da mutanen da suka yi imani da Allah, ka nuna musu cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce. Ta hakan, kana nuna cewa abin da kake koyarwa ba naka ba ne, amma na Allah ne.

  • Ka ja hankalin masu sauraronka ga nassin. Ka yi wata tambayar da za a sami amsar a nassin, ka ambata wata matsala da nassin zai bayyana yadda za a warware ta ko kuma ka faɗi wata ƙa’idar da ke nassin.