Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 3

Ka Yi Amfani da Tambayoyi

Ka Yi Amfani da Tambayoyi

Matiyu 16:​13-16

ABIN DA ZA KA YI: Ka yi tambaya da basira don ka ja hankalin masu sauraronka ko ka taimaka musu su fahimci batun da kake tattaunawa ko kuma ka nanata muhimman darussa.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka sa mutane su saurare ka har ƙarshe. Ka yi tambayar da za ta sa mutane su yi tunani ko kuma su yi sha’awar sanin amsar.

  • Ka sa su yi tunani a kan batun. Ka yi tambayoyi da za su sa masu sauraronka tunani har su kai ga fahimtar abin da kake koya musu.

  • Ka nanata muhimman darussa. Ka yi tambaya don ka ja hankalin masu sauraron ga wani batu mai muhimmanci. Sa’ad da ka kusan gama jawabin, ka yi tambayoyin da za su nanata darussan da kake so ka koyar.