Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 2

Ka Yi Kamar Kuna Tattaunawa

Ka Yi Kamar Kuna Tattaunawa

2 Korintiyawa 2:17

ABIN DA ZA KA YI: Ka yi magana a sake yadda zai nuna cewa kana son batun da kake tattaunawa kuma ka damu da masu sauraronka.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka yi shiri da kyau kuma ka yi addu’a. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka don ka mai da hankali ga saƙon ba kanka ba. Ka yi ƙoƙari ka fahimci ainihin muhimman darussan da kake so ka koyar. Kada ka karanta abin da kake so ka faɗa, amma ka riƙa magana kamar kuna tattaunawa.

  • Ka yi magana daga cikin zuciyarka. Ka yi tunani a kan dalilan da suka sa masu sauraronka suke bukatar saƙon. Ka mai da hankali a kansu. Tsayawarka da motsin hannayenka da jikinka da kuma yadda fuskarka take su nuna cewa abin da kake faɗa gaskiya ne.

  • Ka kalli masu sauraronka. Ka kalli idanun masu sauraronka idan ana yin hakan a yankin. Yayin da kake tattaunawar, ka riƙa kallon mutane ɗaya bayan ɗaya maimakon ka riƙa jujjuyawa kana kallon kowa da kowa.