Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 19

Maganarka ta Ratsa Zuciya

Maganarka ta Ratsa Zuciya

Karin Magana 3:1

ABIN DA ZA KA YI: Ka taimaka wa masu sauraronka su ga amfanin maganarka kuma su yi amfani da abin da suka koya.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka taimaka wa masu sauraronka su bincika kansu. Ka yi tambayoyi don masu sauraro su bincika ra’ayinsu a kan batun.

  • Ka sa su kasance da manufa mai kyau. Ka ƙarfafa masu sauraronka su yi tunani a kan dalilin da ya sa suke yin ayyuka masu kyau. Ka taimaka musu su ga cewa abu mafi kyau da ya kamata su sa a gaba shi ne, su ƙaunaci Jehobah da mutane kuma su so koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ka taimaka musu su ga hikimar da ke cikin Littafi Mai Tsarki; kada ka cika su da surutu. Maimakon ka sa masu sauraronka su ji kunya bayan ka gama jawabin, ka ƙarfafa su don su yi abubuwan da suka dace.

  • Ka sa su san Jehobah. Ka nuna yadda koyarwa da ƙa’idodi da kuma dokokin da ke cikin Kalmar Allah suke nuna halayen Allah masu kyau da kuma yadda yake ƙaunar mu. Ka taimaka musu su san yadda Allah yake ji da kuma yadda za su faranta masa rai.