Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 18

Mutane Su Koyi Darasi Daga Jawabin

Mutane Su Koyi Darasi Daga Jawabin

1 Korintiyawa 9:​19-23

ABIN DA ZA KA YI: Ka sa masu sauraronka su yi tunani a kan batun da kake gaya musu kuma su ji sun koyi darussa masu muhimmanci.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka yi la’akari da abin da masu sauraronka suka sani. Maimakon ka gaya musu abin da suka sani a dā, ka taimaka musu su fahimci batun a wata hanya dabam.

  • Ka yi bincike kuma ka yi tunani. Idan zai yiwu, ka ba da labarin da mutane ba su sani sosai ba don ka bayyana darussa masu muhimmanci. Ka yi tunani sosai game da batun da kake tattaunawa da kuma yadda binciken da ka yi ya jitu da batun.

  • Ka nuna musu muhimmancin maganarka. Ka bayyana yadda bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka wa masu sauraronka a rayuwarsu. Ka faɗi yanayi da halaye da kuma abubuwan da suka shafi masu sauraronka.