Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 16

Ka Yi Jawabi Mai Karfafawa

Ka Yi Jawabi Mai Karfafawa

Ayuba 16:5

ABIN DA ZA KA YI: Ka mai da hankali ga yadda za a magance matsala kuma ka faɗi abubuwa masu ƙarfafawa.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka kasance da ra’ayin da ya dace game da masu sauraronka. Ka gaskata cewa masu sauraronka suna son su faranta wa Jehobah rai. Ka riƙa yaba musu kafin ka ba su shawara.

  • Ka yi amfani da misalai masu kyau. Kada ka ambata munanan abubuwa sai dai idan za su taimaka wajen koyar da muhimman darussa. Ka tattauna abubuwan da za su ƙarfafa su.

  • Ka yi amfani da Kalmar Allah sosai. Ka riƙa ambata abubuwan da Jehobah ya yi da waɗanda yake yi da kuma waɗanda zai yi wa ’yan Adam a nan gaba. Ka sa masu sauraronka su kasance da bege da kuma ƙarfin zuciya.