DARASI NA 15
Ka Yi Magana Ba Shakka
1 Tasalonikawa 1:5
ABIN DA ZA KA YI: Ka nuna cewa maganarka gaskiya ce kuma tana da muhimmanci sosai.
YADDA ZA KA YI HAKAN:
Ka yi shiri sosai. Ka yi nazarin batun da kake son ka tattauna har sai ka ga yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa batun gaskiya ne. Ka bayyana muhimman batutuwan a hanya mai sauƙi. Ka mai da hankali ga yadda masu sauraronka za su amfana. Ka roƙi Allah ya ba ka ruhu mai tsarki.
Ka yi amfani da kalmomin da za su nuna cewa ba ka shakkar abin da kake faɗa. Maimakon ka yi amfani da kalmomi yadda suke a rubuce a cikin littafi, ka yi magana daga zuciyarka. Ka yi amfani da kalmomin da suka nuna cewa ka tabbata da abin da kake cewa.
Ka nuna cewa ka yarda da abin da kake faɗa. Ka ɗaga muryarka daidai yadda masu sauraronka za su ji ka sosai. Ka riƙa kallon masu sauraronka idan ana hakan a yankin.