Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 14

Muhimman Bayanan Su Fita Dalla-Dalla

Muhimman Bayanan Su Fita Dalla-Dalla

Ibraniyawa 8:1

ABIN DA ZA KA YI: Ka taimaka wa masu sauraronka su riƙa bin jawabin, kuma ka nuna musu yadda muhimman bayanan suka jitu da jigon da kuma darasin.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka kasance da manufa. Ka bincika ka ga ko manufar jawabin shi ne a sanar da su ko tabbatar musu da wani batu, ko kuma ƙarfafa su su yi wani abu. Ka tabbata cewa abin da za ka tattauna zai taimaka maka ka cim ma manufar jawabin.

  • Ka riƙa nanata jigon jawabinka. Sa’ad da kake tattaunawar, ka riƙa nanata jigon jawabinka. Kana iya sake maimaita kalamai ko furucin da suka jitu da jigon.

  • Ka sa bayanan su fita sarai da kuma sauƙin fahimta. Ka zaɓi batutuwan da suka jitu da jigon jawabinka don ka iya gama aikin daidai kan lokaci. Kada bayanan su yi yawa, amma su fita sarai. Ka riƙa dakatawa sa’ad da kake magana don masu sauraron su fahimce su da kyau. Ka gama bayanin kafin ka shiga na gaba.