Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 13

Ka Nuna Yadda Za Su Amfana

Ka Nuna Yadda Za Su Amfana

Karin Magana 3:21

ABIN DA ZA KA YI: Ka taimaka wa masu sauraronka su fahimci yadda batun da kake tattaunawa ya shafe su kuma ka nuna abin da ya kamata su yi.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka yi tunani game da masu sauraronka. Ka yi tunani a kan dalilin da ya sa masu sauraronka suke bukatar su ji saƙon kuma ka zaɓi batutuwa da za su amfane kowannensu.

  • Ka nuna wa masu sauraronka abin da ya kamata su yi yayin da kake jawabi. Tun daga farko, ka taimaka wa masu sauraronka su ga cewa batun zai amfane kowannensu. A lokacin da kake bayyana muhimman darussa, ka nuna yadda za su yi amfani da darussan. Kuma ka bayyana darussan dalla-dalla.