Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 30

Taimako Domin Mu Kawar da Tsoratarmu

Taimako Domin Mu Kawar da Tsoratarmu

BAUTA wa Jehovah yana da sauƙi ne?— Babban Malami bai ce zai kasance da sauƙi ba. A daren da za a kashe Yesu, ya gaya wa manzanninsa: “Idan duniya ta ƙi ku, kun sani ta rigaya ta ƙi ni tun ba ta ƙi ku ba.”—Yohanna 15:18.

Bitrus ya yi fahariyar cewa ba zai taɓa barin Yesu ba, amma Yesu ya ce Bitrus zai yi musunsa sau uku a wannan daren. Kuma haka Bitrus ya yi! (Matta 26:31-35, 69-75) Ta yaya irin wannan abin zai faru?— Ya faru domin Bitrus ya tsorata ne, sauran manzannin ma sun tsorata.

Ka san abin da ya sa manzannin suka tsorata— Ba su yi wani abu ba ne mai muhimmanci. Koyon wannan zai taimaka mana mu bauta wa Jehovah ko da menene mutane za su ce game da mu ko kuma su yi mana. Amma da farko, muna bukatar mu sake maimaita abin da ya faru a daren ƙarshe da Yesu ya yi da manzanninsa.

Da farko, sun yi bikin Ƙetarewa. Wannan dina ce ta musamman da ake yi kowacce shekara domin a tunasar da mutanen Allah ceton da Allah ya yi wa mutanensa a bauta daga ƙasar Masar. Sai Yesu ya kafa wata dina ta musamman. Za mu tattauna wannan a babi na gaba kuma za mu yi bayani game da yadda wannan dina take taimaka mana mu tuna da Yesu. Bayan wannan dina da kuma kalmomi na ƙarfafa ga manzanninsa, Yesu ya je da su lambun Jathsaimani. Wannan waje ne da suke yawan ziyarta.

 Yesu ya ɗan matsa gaba kaɗan a cikin lambun domin ya yi addu’a. Ya kuma gaya wa Bitrus, Yaƙub, da kuma Yohanna su yi addu’a. Amma barci ya kwashe su. Sau uku Yesu ya je ya yi addu’a shi kaɗai, kuma sau uku ya dawo wajensu ya ga Bitrus da sauran suna barci! (Matta 26:36-47) Ka san abin da ya sa ya kamata su kasance a faɗake domin su yi addu’a?— Bari mu tattauna game da wannan?

Me ya hana Bitrus, Yaƙub, da Yohanna kasancewa a faɗake?

Yahuda Iskariyoti yana wajen bikin Ƙetarewa tare da Yesu da wasu manzannin da yamma a ranar. Kamar yadda ka tuna, Yahuda ya zama ɓarawo. Yanzu ya zama maci amana. Ya san wajen da Yesu da manzanninsa suke taruwa domin addu’a a lambun Jathsaimani. Saboda haka, Yahuda ya kai sojoji wurin domin su kama Yesu. Sa’ad da suka isa, Yesu ya tambaye su: “Wa ku ke nema?”

Sojojin suka amsa: “Yesu.” Yesu bai ji tsoro ba, saboda haka ya amsa musu: “Ni ne.” Sojojin suka yi mamakin gaba gaɗinsa suka ja da baya suka faɗi a ƙasa. Yesu ya ce musu: ‘Idan ni kuke nema, ku ƙyale manzannina su yi tafiyarsu.’—Yohanna 18:1-9.

Sa’ad da sojojin suka kama Yesu suka ɗaure shi, mazannin suka tsorata suka watse. Amma Bitrus da Yohanna suna so su san abin da zai faru, saboda haka suka bi su daga nesa. Sai aka kai Yesu gidan Kayafa, babban firist. Tun da babban firist ɗin ya san Yohanna, masu gadi suka ƙyale shi da Bitrus suka shiga cikin gidan.

Firistocin sun riga sun taru a gidan Kayafa domin su yi hukunci. Suna so a kashe Yesu. Saboda haka, suka kawo shaidu suka zo suka yi shaidar zur. Mutane suka naushi Yesu kuma suka mare shi. Sa’ad da dukan waɗannan suna faruwa Bitrus yana kusa.

Wata kuyanga, da suke gadi da ta ƙyale Bitrus da Yohanna suka shiga, ta gane Bitrus. “Kai kuma dā kana tare da Yesu,” in ji ta.  Amma Bitrus ya ce shi bai san Yesu ba. Daga baya wata yarinya ta gane Bitrus kuma ta ce wa waɗanda suke tsaye a wurin: “Wannan mutumin kuma dā yana tare da Yesu.” Sai Bitrus ya sake cewa bai san shi ba. Can daga baya wasu mutane suka ga Bitrus suka ce masa: “Hakika kai kuma na cikinsu ne.” Na ukun ke nan da, Bitrus ya ce: “Ban san mutumin ba.” Bitrus ya yi rantsuwa cewa yana faɗan gaskiya, sai Yesu ya waiga ya kalle shi.—Matta 26:57-75; Luka 22:54-62; Yohanna 18:15-27.

Me ya sa Bitrus ya tsorata sosai da ya sa ya yi ƙarya game da sanin Yesu?

Ka san abin da ya sa Bitrus ya yi ƙarya?— I, domin ya tsorata. Amma me ya sa ya tsorata? Me ya kasa yi domin ya kasance da gaba gaɗi? Ka yi tunani game da wannan. Menene Yesu ya yi domin ya sami gaba gaɗi?— Ya yi wa Allah addu’a, kuma Allah ya taimake shi ya sami gaba gaɗi. Ka tuna kuma, Yesu sau uku ya gaya wa Bitrus ya yi addu’a kuma ya kasance a faɗake. Amma me ya faru?—

A dukan lokacin barci ya kwashi Bitrus. Bai yi addu’a ba, kuma bai ci gaba da tsaro ba. Saboda haka, kama Yesu da aka yi, ya zo  masa ba sani ba tsammani. Daga baya a lokacin shari’ar, da suka bugi Yesu kuma suka shirya su kashe shi, Bitrus ya tsorata. Amma, wasu awoyi kafin haka, menene Yesu ya gaya wa manzanninsa su yi tsammani?— Yesu ya gaya musu tun da duniya ta ƙi shi, za ta ƙi su su ma.

Ta yaya za ka shiga irin wannan yanayi da ya yi kama da na Bitrus?

Bari yanzu mu yi tunanin abin da zai iya faruwa da mu kamar wanda ya faru da Bitrus. A ce kana cikin aji sai wasu suka fara zagin mutane da ba sa sara wa tuta ko kuma waɗanda ba sa bikin Kirsimati. Me za ka yi idan wani ya juya ya tambaye ka: “Gaskiya ne ba ka sara wa tuta?” Ko kuma wasu suka ce: “Mun ji ba  kuwa ma yin Kirsimati!” Za ka ji tsoron faɗin gaskiya ne?— Ko kuma za ka yi ƙoƙarin ka yi ƙarya ne kamar yadda Bitrus ya yi?—

Daga baya, Bitrus ya yi baƙin ciki ƙwarai domin ya ce bai san Yesu ba. Sa’ad da ya fahimci abin da ya yi, ya fita waje ya yi kuka. Hakika, ya komo ga Yesu. (Luka 22:32) Ka yi tunani game da wannan. Menene zai taimake mu kada mu ji tsoro kamar yadda Bitrus ya ji?— Ka tuna, Bitrus bai yi addu’a ba kuma bai ci gaba da tsaro ba. Saboda haka, me za ka ce muke bukata domin mu zama mabiyan Babban Malami?—

Hakika muna bukatar mu yi wa Jehovah addu’a domin taimako. Sa’ad da Yesu ya yi addu’a, ka san abin da Allah ya yi masa?— Ya aiko da mala’ika ya ƙarfafa shi. (Luka 22:43) Mala’ikun Allah za su taimake mu kuwa?— Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mala’ikan Ubangiji yana kafa sansani a kewaye da masu-tsoronsa, yana tseradda su kuma.” (Zabura 34:7) Amma domin mu sami taimakon Allah, muna bukatar mu yi fiye da addu’a domin taimako. Ka san abin da kuma ya kamata mu yi?— Yesu ya gaya wa mabiyansa su kasance a faɗake kuma su yi tsaro. Ta yaya kake tsammanin za mu iya yin haka?—

Ya kamata mu saurari da kyau abin da ake faɗa a taronmu na Kirista kuma mu mai da hankali ga abin da muka karanta a Littafi Mai Tsarki. Amma kuma muna bukatar mu yi addu’a ga Jehovah a kai a kai kuma mu roƙe shi ya taimake mu mu bauta masa. Idan muka yi haka, za mu sami taimako mu kawar da tsoratarmu. Kuma za mu yi farin ciki idan muka sami zarafi muka gaya wa wasu game da Babban Malami da kuma Ubansa.

Waɗannan nassosin za su taimake mu ba za mu bar tsoron wasu mutane ya sa mu kasa yin abin da yake daidai ba: Misalai 29:25; Irmiya 26:12-15, 20-24 da kuma Yohanna 12:42, 43.