Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 24

Kada Ka Zama Barawo!

Kada Ka Zama Barawo!

WANI ya taɓa sace wani abin ka?— Yaya ka ji?— Ko waye da ya saci abin ɓarawo ne, kuma babu wanda yake son ɓarawo. Ta yaya kake tsammanin mutum yake zama ɓarawo? Ana haifansa ne haka?—

Bai jima ba da muka koyi cewa ana haifan mutane da zunubi. Saboda haka, dukanmu ajizai ne. Babu mutumin da aka haife shi ɓarawo. Ɓarawo zai iya kasancewa daga iyali nagari. Iyayensa, ’yan’uwansa maza da mata za su kasance masu gaskiya. Amma idan mutum yana son kuɗi ko kuma abin da kuɗi yake saya zai iya sa shi ya zama ɓarawo.

Waye kake ji ya fara sata?— Ka yi tunani. Babban Malami ya san mutumin sa’ad da yake sama. Wannan ɓarawon mala’ika ne. Amma tun da Allah ya yi dukan mala’iku kamilai, ta yaya mala’ikan ya zama ɓarawo?— Kamar yadda muka koya a Babi na 8 na wannan littafin, yana son wani abu da ba na shi ba. Ka tuna ko menene wannan?—

Bayan da Allah ya halicci namiji da tamace na farko, wannan mala’ikan yana son su bauta masa. Ba shi da ikon ya karɓi wannan bautar. Bautarsu ta Allah ce. Amma ya sace ta! Ta wajen saka Adamu da Hauwa’u su bauta masa, mala’ikan ya zama ɓarawo. Ya zama Shaiɗan Iblis.

Menene yake sa mutum ya zama ɓarawo?— Son abin da ba na shi ba. Wannan muradin yana da ƙarfi sosai da zai sa mutanen kirki su yi miyagun abubuwa. Wani lokaci waɗannan mutane da  suka zama ɓarayi ba sa juyawa su yi abin da yake da kyau kuma. Ɗaya cikin waɗannan manzon Yesu ne. Sunansa Yahuda Iskariyoti.

Yahuda ya sani cewa ba shi da kyau a yi sata, an koya masa Dokar Allah tun lokacin da yake ƙarami. Ya sani cewa da akwai lokacin da Allah ya yi magana daga sama ya gaya wa mutanensa: ‘Kada ku yi sata.’ (Fitowa 20:15) Sa’ad da Yahuda ya yi girma, ya sadu da Babban Malami kuma ya zama almajirinsa. Daga baya, Yesu ya zaɓi Yahuda ya zama cikin manzanninsa 12.

Yesu da manzanninsa suna tafiya tare. Suna cin abinci tare. Kuma dukan kuɗin da suke da shi sun zuba cikin asusu. Yesu ya bai wa Yahuda asusun ya kula da shi. Hakika kuɗin ba na Yahuda ba ne. Amma ka san abin da Yahuda ya yi bayan ɗan lokaci?—

Me ya sa Yahuda ya yi sata?

Yahuda ya fara ɗeban kuɗi daga cikin asusu sa’ad da bai kamata ya ɗauka ba. Zai ɗebi kuɗin sa’ad da wasu ba sa gani, kuma ya yi ƙoƙari ya sami hanyar samun kuɗi da yawa. Ya fara tunanin kuɗi ko da yaushe. Bari mu ga abin da wannan muradin da ba shi da kyau ya sa ya yi kwanaki kaɗan kafin a kashe Babban Malami.

Maryamu, ’yar’uwar Li’azaru, ta kawo mai, mai kyau ta zuba a sawun Yesu. Amma Yahuda ya yi gunaguni. Ka san abin da ya sa?— Ya ce domin da ya kamata a sayar da man a bai wa matalauta kuɗin. Amma yana so ya sami kuɗi da yawa a cikin asusun ne domin ya sami na sacewa.—Yohanna 12:1-6.

Yesu ya gaya wa Yahuda kada ya dami Maryamu, wadda take da kirki. Yahuda bai ji daɗi ba sa’ad da Yesu ya gaya masa haka, saboda haka ya je wajen babban firist, waɗannan abokan gaba ne  na Yesu. Suna so su kama Yesu, amma suna so su yi haka cikin dare saboda mutanen kada su gan su.

Yahuda ya gaya wa firistocin: ‘Zan gaya muku yadda za ku sami Yesu, idan za ku ba ni kuɗi. Nawa za ku ba ni?’

‘Za mu baka sulalla talatin,’ firistocin suka amsa.—Matta 26:14-16.

Yahuda ya karɓi kuɗin. Kamar yana sayar da Babban Malami ga waɗannan mutane ne! Ka taɓa ganin mutum yana irin wannan mugun abu?— To, irin abin da yake faruwa ke nan sa’ad da mutum ya zama ɓarawo kuma yakan saci kuɗi. Yana son kuɗi fiye da yadda yake ƙaunar mutane har da Allah.

Wataƙila za ka ce, ‘Ba zan taɓa ƙaunar wani abu ba fiye da yadda nake ƙaunar Jehovah Allah.’ Yana da kyau da ka ji haka. Sa’ad da Yesu ya zaɓi Yahuda ya zama manzo, wataƙila haka Yahuda ya ji. Wasu da suka zama ɓarayi wataƙila su ma sun ji haka. Bari mu yi magana game da wasu cikinsu.

Waɗanne abubuwa ne marasa kyau Akan da Dauda suke tunaninsa?

Wani bawan Allah ne mai suna Akan, ya rayu da daɗewa kafin a haifi Babban Malami. Akan  ya ga riga mai kyau, da sanda na zinariya, da kuma wasu sulalla. Ba na shi ba ne. Littafi Mai Tsarki ya ce na Jehovah ne domin an kwato su daga wurin abokan gaban mutanen Allah. Amma Akan yana son su sosai sai ya sace su.—Joshua 6:19; 7:11, 20-22.

Ga wani misali kuma. Da daɗewa, Jehovah ya zaɓi Dauda ya zama sarkin mutanensa Isra’ila. Wata rana, Dauda ya fara kallon wata kyakkyawar mace mai suna Bath-sheba. Ya yi ta kallon Bath-sheba yana tunanin ɗaukanta zuwa gidansa. Amma kuma matar Uriya ce. Da menene ya kamata Dauda ya yi?—

Da ya kamata Dauda ya daina tunanin Bath-sheba. Amma bai daina ba. Sai Dauda  ya ɗauke ta zuwa gida. Kuma ya kashe Uriya. Me ya sa Dauda ya yi wannan mugun abu?— Domin ya ci gaba da son matar wani.—2 Samu’ila 11:2-27.

A wace hanya ce Absalom ya kasance ɓarawo?

Domin Dauda ya tuba, Jehovah ya ƙyale shi. Amma daga lokacin zuwa gaba Dauda ya fuskanci masifu da yawa. Ɗansa Absalom yana son ya ƙwaci sarauta a hannun Dauda. Saboda haka, idan mutane suka zo su ga Dauda, Absalom zai rungume su kuma ya sumbace su. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Absalom ya sace zukatan mazaje na Isra’ila.” Ya sa waɗannan mutane su so ya zama sarki a maimakon Dauda.—Tafiyar tsutsa tamu ce; 2 Samu’ila 15:1-12.

Ka taɓa son wani abu sosai, kamar yadda Akan, Dauda, da kuma Absalom suka yi?— Idan wannan abin na wani ne, in ka ɗauka babu tambaya to, sata ne. Ka tuna abin da ɓarawo na farko, Shaiɗan, yake so?—Yana son mutane su bauta masa maimakon Allah. Saboda haka, Shaiɗan yana sata sa’ad da ya sa Adamu da Hauwa’u su yi masa biyayya.

Idan mutum yana da wani abu, yana da iko ya ce ga wanda zai yi amfani da shi. Alal misali, za ka je ka yi wasa da wasu yara a gidansu. Daidai ne ka ɗauki wani abu daga can ka kawo gidanku?— A’a, sai dai baban ko mamar ta ce ka ɗauka. Idan ka ɗauki wani abu zuwa gidanku ba tare da izni ba, wannan sata ne.

Me ya sa za ka ji kamar ka yi sata?— Domin kana son abin da ba naka ba. Ko ma idan babu mutumin da ya ga lokacin da ka ɗauki abin, wa yake gani?— Jehovah Allah. Kuma muna so mu tuna cewa Allah ba ya son sata. Saboda haka, ƙaunar Allah da maƙwabcinka zai taimake ka ba za ka zama ɓarawo ba.

Littafi Mai Tsarki ya bayyana sarai cewa ba daidai ba ne ka yi sata. Ka karanta Markus 10:17-19; Romawa 13:9 da kuma Afisawa 4:28.