Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 1

Abin da Ya Sa Yesu Babban Malami Ne

Abin da Ya Sa Yesu Babban Malami Ne

FIYE da shekara dubu biyu da ta gabata, an haifi yaro na musamman wanda ya yi girma ya zama mutum mafi girma da ya taɓa rayuwa. Babu wanda ya yi rayuwa a wannan lokacin da yake da jirgin sama ko kuma motoci. Babu kuma abubuwa kamar su telibijin, ko su rediyo.

An raɗa wa yaron suna Yesu. Ya zama mutum mafi hikima da ya taɓa rayuwa a wannan duniyar. Yesu kuma ya zama malami mafi ƙwarewa. Yana bayyana abubuwa masu wuya a hanyar da za ta sa su kasance da sauƙin fahimta.

Yesu ya koyar da mutane a dukan inda ya sadu da su. Ya koyar da mutane a bakin kogi da kuma a cikin jirgin ruwa. Ya koyar da su a gidaje da kuma sa’ad da suke tafiya. Yesu ba shi da mota, kuma bai yi tafiya a cikin bos ba ko kuwa jirgin ƙasa. Yesu ya yi tafiya a ƙar daga wuri zuwa wuri, yana koyar da mutane.

Muna koyon abubuwa da yawa daga wurin wasu mutane. Za mu koyi abu mafi muhimmanci daga wurin Babban Malami, Yesu. A cikin Littafi Mai Tsarki ne aka samu kalmomin Yesu. Sa’ad da muka ji waɗannan kalmomin daga cikin Littafi Mai Tsarki, kamar a ce Yesu yana magana da mu ne.

Me ya sa Yesu Babban Malami ne haka? Dalili guda shi ne Yesu kansa an koyar da shi ne. Ya san muhimmancin saurarawa. Amma Yesu ya saurari wanene? Waye ya koyar da shi?—Ubansa ne ya koyar da shi. Kuma Uban Yesu Allah ne.

 Kafin ya zo duniya cikin surar mutum, Yesu ya rayu a sama tare da Allah. Saboda haka, Yesu ya bambanta daga wasu mutane domin babu wani mutumin da ya rayu a sama kafin aka haife shi a duniya. A sama Yesu yaro ne na kirki, wanda yake sauraron Ubansa. Saboda haka Yesu ya iya koyar da mutane abin da ya koya daga wajen Allah. Ta wajen sauraron babanka da mamarka, kana koyi da Yesu.

Wani dalili kuma da ya sa Yesu Babban Malami ne domin yana ƙaunar mutane. Yana so ya taimaki mutane su koyi game da Allah. Yesu yana ƙaunar manyan mutane, amma yana ƙaunar yara ma. Kuma yara suna so su je wajen Yesu domin yana yin magana da su kuma yana sauraronsu.

Me ya sa yara suke so su kasance tare da Yesu?

Wata rana iyaye suka kawo yaransu ƙanana wajen Yesu. Amma abokanansa suna tsammanin yana aiki ba shi da lokacin yin magana da yara ƙanana. Saboda haka suka ce su tafi. Amma menene Yesu ya ce?— Yesu ya ce: “Ku bar yara ƙanƙanana su zo gareni; kada ku hana su.” Hakika, Yesu yana son yara su zo gare shi.  Ko da yake shi mutum ne mai hikima kuma babban mutum, Yesu ya ɗauki lokaci ya koyar da yara ƙanana.—Markus 10:13, 14.

Ka san abin da ya sa Yesu ya koyar da yara kuma ya saurare su? Dalili ɗaya shi ne yana so ya sa su farin ciki ta wajen faɗa musu game da Allah, Ubansa na samaniya. Ta yaya za ka sa mutane su yi farin ciki?—Ta wajen gaya musu abubuwa da ka koya game da Allah.

Wani lokaci, Yesu ya yi amfani da yaro ƙarami ya koya wa Abokanansa darasi mai muhimmanci. Ya ɗauki yaron ya tsayar da shi a tsakiyar almajiransa, waɗanda mabiyansa ne. Sai Yesu ya ce waɗannan manyan mutane dole ne su canja halinsu su zama kamar wannan yaro ƙarami.

Wane darasi yara da kuma manya za su koya daga zama kamar yaro ƙarami?

Menene Yesu yake nufi da ya faɗi haka? Ka san yadda babban mutum, ko ma ɗan samari, zai zama kamar yaro ƙarami?— To, yaro ƙarami ba shi da ilimi kamar na babban mutum kuma yana so ya yi ilimi. Saboda haka, Yesu yana cewa ne almajiransa suna bukatar su zama masu tawali’u, kamar yara ƙanana. Hakika, mu duka za mu iya koyon abubuwa da yawa daga wajen wasu mutane. Kuma ya kamata mu fahimci cewa koyarwar Yesu ta fi ra’ayinmu daraja.—Matta 18:1-5.

Wani dalili kuma da ya sa Yesu ne Babban Malami shi ne cewa ya san yadda zai sa abubuwa su yi wa mutane daɗi. Yana yin bayani game da abubuwa a hanya mai sauƙi. Ya yi magana game da tsuntsaye da kuma furanni da wasu abubuwa na yau da kullum su taimaki mutane su fahimci abubuwa game da Allah.

 Wata rana sa’ad da Yesu yake gefen dutse, mutane da yawa suka zo wajensa. Yesu ya zauna ya yi musu jawabi, ko kuma huɗuba, kamar yadda kake gani a nan. Wannan jawabin ana kiransa Huɗuba Bisa Dutse. Ya ce: ‘Dubi tsuntsayen sama. Ba sa shuki. Ba sa tara abinci a rumbuna. Amma Allah a sama yana ciyar da su. Ba ka fi su daraja ba ne?’

Wane darasi yara da kuma manya za su koya daga zama kamar yaro ƙarami?

Yesu kuma ya ce: ‘Ka ɗauki darasi daga furannin daji. Sun yi girma ba tare da aiki ba. Kuma ka ga yadda suke da kyau! Har Sarki Sulemanu mai arziki bai yi ado mai kyau irin na furannin dawa ba. Saboda haka, idan Allah yana kula da furannin da suke girma, ba zai kula da ku ba ne?’—Matta 6:25-33.

Ka fahimci darasi da Yesu yake koyarwa?—Ba ya so mu damu game da inda za mu samu abinci ko kuma tufafi da za mu saka a jiki. Allah ya sani muna bukatar waɗannan abubuwa. Yesu bai ce kada  mu yi aiki domin abinci ba ko kuma tufafi. Amma ya ce mu saka Allah da farko. Idan muka yi haka, Allah zai tabbata cewa mun samu abincin da za mu ci da kuma tufafi da za mu saka. Ka yarda da haka?—

Sa’ad da Yesu ya gama magana, menene mutane suka yi?— Littafi Mai Tsarki ya ce sun yi mamakin yadda yake koyarwa. Yana da daɗi a saurare shi. Abin da ya ce ya taimaki mutane su yi abin da yake da kyau.—Matta 7:28.

 Saboda haka yana da muhimmanci ƙwarai mu koya daga wurin Yesu. Ka san yadda za mu yi haka?— Muna da maganarsa a rubuce cikin littafi. Menene sunan wannan littafin?— Littafi Mai Tsarki ne. Wannan yana nufi cewa za mu saurari Yesu ta wajen mai da hankali da abubuwa da muka karanta a cikin Littafi Mai Tsarki. Hakika, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labarai masu daɗi game da yadda Allah da kansa ya gaya mana mu saurari Yesu. Ka ga abin da ya faru.

Wata rana, Yesu ya ɗauki abokanansa uku suka hau saman dutse. Sunayensu Yaƙub, Yohanna da kuma Bitrus. Za mu koyi abubuwa da yawa game da waɗannan mutanen a gaba, tun da dukansu uku abokane ne na kud da kud da Yesu. Amma a wannan lokaci na musamman, fuskar Yesu ta yi walƙiya ƙwarai. Kuma tufarsa ta zama kamar rana, kamar yadda kake gani a nan.

“Wannan Ɗana ne . . . ku ji shi”

Daga baya, Yesu da abokanansa suka ji murya daga sama. Ta ce: “Wannan Ɗana ne ƙaunatacena, wanda raina ya ji daɗinsa sarai; ku ji shi.” (Matta 17:1-5) Ka san ko muryar wanene wannan?— Muryar Allah ce! Allah ne ya ce su saurari Ɗansa.

To, mu fa a yau? Za mu yi wa Allah biyayya mu saurari Ɗansa, Babban Malami?— Wannan shi ne abin da dukanmu ya kamata mu yi. Ka tuna yadda za mu iya yin haka?—

Hakika, za mu saurari Ɗan Allah ta wajen karatun tarihin Littafi Mai Tsarki game da rayuwarsa. Da akwai abubuwa da yawa da Babban Malamin zai gaya mana. Za ka ji daɗin karanta waɗannan abubuwa da suke rubuce cikin Littafi Mai Tsarki. Kuma zai sa ka farin ciki idan ka gaya wa abokananka abubuwa masu kyau da ka koya.

Domin ƙarin koyarwa game da abubuwa masu kyau da za su zo daga sauraron Yesu, ka buɗe Littafi Mai Tsarki naka ka karanta Yohanna 3:16; 8:28-30; da Ayukan Manzanni 4:12.