Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 19

Daidai Ne A Yi Fada?

Daidai Ne A Yi Fada?

KA SAN wasu yara maza ko mata waɗanda suke nuna su manya ne kuma suna son faɗa?— Kana so ka zama kamarsu? Ko kuma za ka so ka zauna da wanda yake da kirki kuma yana son zaman lafiya?— Babban Malami ya ce: “Masu-albarka ne masu-sada zumunta: gama za a ce da su ’ya’yan Allah.”—Matta 5:9.

Amma wani lokaci mutane suna yin abin da yake ba mu haushi. Ko ba haka ba ne?— Sai mu ji kamar ya kamata mu rama. Sau ɗaya wannan ya faru da almajiran Yesu sa’ad da suke tafiya tare da Yesu zuwa Urushalima. Bari in ba ka labarin.

Sa’ad da suka yi ɗan nisa kaɗan, Yesu ya aiki wasu almajiransa su yi gaba su je wani ƙauyen Samariyawa su nemi wajen da za su huta. Amma mutanen wajen ba sa so su zauna, tun da Samariyawan addininsu ya bambanta da nasu. Kuma ba sa son kowa da yake zuwa Urushalima domin bauta.

Menene Yaƙub da Yohanna suke so su yi domin su rama abin da Samariyawa suka yi musu?

 Idan haka ya faru da kai, menene za ka yi? Za ka ji haushi ne? Da za ka so ka rama abin da suka yi maka?— Haka almajirai Yaƙub da Yohanna suke so su yi. Suka gaya wa Yesu: ‘Kana so mu ce wa wuta ta sauko daga sama ta halaka su?’ Babu mamaki da Yesu ya kira su ’Ya’yan Aradu! Amma Yesu ya gaya musu cewa ba daidai ba ne a bi da mutane haka.—Luka 9:51-56; Markus 3:17.

Gaskiya ne cewa mutane za su yi mana rashin hankali a wasu lokatai. Wasu yara ba za su so mu yi wasa da kayan wasansu ba. Za su ma ce: “Ka tafi daga nan.” Idan haka ya faru zai sa ka ka yi fushi ko ba haka ba? Za mu ji kamar mu yi musu wani abu domin mu rama. Amma ya kamata ne mu yi haka?

Ka ɗauko Littafin Mai Tsarki. Bari mu ga Misalai sura 24, aya ta 29. Nan ta ce: “Kada ka ce, sai in yi masa yadda ya yi mini: in saka ma mutumin bisa ga aikinsa.”

Menene ka gane game da wannan?— Yana cewa ne kada mu yi ƙoƙarin ramako. Kada mu yi rashin kirki ga mutane kamar yadda suka yi mana rashin kirki. Amma idan mutum yana so ya yi faɗa da mu fa? Zai yi ƙoƙarin ya ba ka haushi ta wajen zaginka. Zai yi maka dariya ya ce ka ji tsoro. Idan kuma ya ce da kai matsoraci fa? Me za ka yi? Ya kamata ka ƙyale kanka ka yi faɗa ne?—

Bari mu ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Bari mu juya zuwa ga Matta sura 5, aya ta 39. A nan Yesu ya ce: “Ba za ku yi tsayayya da wanda shi ke mugu ba: amma iyakar wanda ya mare ka a kumatu na dama, juya masa wancan kuma.” Menene kake tsammani Yesu yake nufi? Yana nufi ne cewa idan mutum ya naushe ka a gefen fuskarka ɗaya sai ka juya masa gefe ɗayan ne?—

A’a, ba haka Yesu yake nufi ba. Mari ba kamar naushi ba ne. Ya  fi kama da turi. Mutum zai iya marinmu domin ya sa mu yi faɗa. Yana so ka yi fushi. Idan kuma ka yi fushi ka ture shi, me zai faru?— Wataƙila sai ku fara faɗa.

Amma Yesu ba ya son mabiyansa su yi faɗa. Saboda haka, ya ce idan mutum ya mare mu kada mu mare shi. Bai kamata mu yi fushi ba mu fara faɗa. Idan muka yi haka, za mu tuna cewa muna da hali irin na wanda ya jawo faɗan.

Idan aka fara faɗa, me kake tsammanin ya fi dacewa ka yi?— Ka yi tafiyarka. Wataƙila mutumin ya ture ka sau da yawa. Wataƙila zai daina bayan haka. Idan ka yi tafiyarka bai nuna cewa ba ka da ƙarfi ba. Ya nuna cewa kana son abin da yake daidai.

Me ya kamata mu yi idan wani yana so ya yi faɗa da mu?

 Amma idan ka yi faɗa kuma ka yi nasara fa? Menene zai iya faruwa?— Wanda ka yi wa dūka zai zo da wasu abokane. Wataƙila su ji maka da sanduna ko kuma da wuƙaƙe. To, yanzu ka ga abin da ya sa Yesu ba ya so mu yi faɗa?—

To, me za mu yi idan muka ga wasu mutane suna faɗa? Ya kamata ne mu ɗaure wa waninsu gindi?— Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abin da yake daidai. Ka juya zuwa ga Misalai sura 26, aya ta 17. Ta ce: “Wanda yana kan wucewa, ya dami ransa da husuma wadda ba tasa ba ce, yana kama da mutum wanda ya kama kare da kunnuwansa.”

Ta yaya tare faɗar wasu kamar kama kunnuwan kare ne? Za ka ji rauni, saboda haka, kada ka yi shi!

Menene zai faru idan ka kama kunnuwan kare? Idan ka kama kunnen kare zai ji zafi, kuma ya cije ka, ko ba haka ba? Idan karen yana ƙoƙarin ya kuɓuce, kai kuma za ka damƙe kunnen da ƙarfi kuma karen zai ƙara fushi. Idan kuma ka ƙyale shi wataƙila ya cije ka da ƙarfi. Amma za ka iya tsayawa ne a wajen ka riƙe kunnensa har abada?—

Wannan ita ce masifa da za mu shiga idan muka tare faɗar da ba tamu ba. Ba za mu san ko wanene ya fara faɗan ba ko kuma dalilin da ya sa suke faɗa. Wataƙila an yi wa ɗaya dūka ne, ko kuma ya saci wani abu ne na ɗayan. Idan ka taimake shi, wataƙila kana taimakon ɓarawo. Hakan ba zai yi kyau ba, ko ba haka ba?

 Menene ya kamata ka yi idan ka ga ana faɗa?— Idan a makaranta ne, ka gudu ka gaya wa malami. Kuma idan ba a makaranta ba ne, ka kira babanka ko kuma ɗan sanda. Ko ma wasu mutane suna so su yi faɗa, mu ya kamata mu kasance masu son zaman lafiya.

Menene ya kamata ka yi idan ka ga ana faɗa?

Almajiran Yesu na gaskiya suna yin dukan abin da za su yi domin su guje wa faɗa. Ta haka za mu nuna cewa muna dagewa ga abin da yake da kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce almajirin Yesu ‘kada ya yi faɗa, amma sai ya kasance da nasiha ga duka.’—2 Timothawus 2:24.

Yanzu bari mu ga ƙarin gargaɗi da za su taimake mu mu guje wa faɗa: Romawa 12:17-21 da kuma 1 Bitrus 3:10, 11.