Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 26

Abin da Ya Sa Yake da Wuya a Yi Nagarta

Abin da Ya Sa Yake da Wuya a Yi Nagarta

SA’AD da Shawulu ya yi munanan abubuwa, waye ya yi farin ciki?— Shaiɗan Iblis ne ya yi farin ciki. Amma shugabanin addinin Yahudawa ma sun yi farin ciki. Sa’ad da Shawulu ya zama almajirin Babban Malami kuma ake kiransa Bulus, waɗannan shugabannan addinin suka fara ƙin shi. Ka ga abin da ya sa yake da wuya ga almajirin Yesu ya yi abin da yake da kyau?—

Menene Bulus ya sha wuyansa sa’ad da ya yi abin da yake da kyau?

Babban firist da ake kira Hananiya ya taɓa gaya wa mutane su naushi Bulus a fuskarsa. Hananiya ya yi ƙoƙari ma ya sa a jefa Bulus cikin kurkuku. Bulus ya wahala ƙwarai sa’ad da ya zama almajirin Yesu. Alal misali, miyagun mutane sun yi wa Bulus dūka kuma suka yi ƙoƙari su kashe shi da manyan duwatsu.—Ayukan Manzanni 23:1, 2; 2 Korinthiyawa 11:24, 25.

Mutane da yawa za su sa mu yi abin da ya ke baƙanta wa Allah  rai. Saboda haka, tambaya ita ce, Yaya yawan yadda kake son abin da yake da kyau? Kana son shi sosai da za ka yi abin da yake da kyau ko mutane sun ƙi ka domin haka? Yana bukatar gaba gaɗi mu yi haka, ko ba ya bukatar gaba gaɗi ne?—

Za ka yi mamaki, ‘Me ya sa mutane za su ƙi mu domin muna yin abin da yake da kyau? Bai kamata su yi farin ciki ba?’ Haka za ka gani. Sau da yawa mutane sun yi ƙaunar Yesu domin abubuwa nagari da ya yi. Dukan mutanen gari sun taɓa taruwa maƙil a ƙofar gidan da ya sauka. Sun zo ne domin Yesu yana warkar da mutane masu rashin lafiya.—Markus 1:33.

 Amma wani lokaci mutane ba sa son abin da Yesu yake koyarwa. Ko da yake koyaushe yana koyar da abin da yake da kyau, sun nuna sun tsane shi ƙwarai domin ya faɗi gaskiya. Wannan ya faru a Nazarat, birnin da Yesu ya girma. Ya je cikin majami’ar, wurin da Yahudawa suke taruwa su bauta wa Allah.

A nan Yesu ya yi jawabi mai kyau daga Nassosi. Da farko mutanen suna so. Suna mamakin kalmomi masu daɗi da suke fitowa daga bakinsa. Suna mamakin ko wannan ne saurayin da ya yi girma a garinsu.

Amma da Yesu ya faɗi wani abu. Ya yi magana game da lokacin da Allah ya yi wa mutanen da ba Yahudawa ba tagomashi na musamman. Sa’ad da Yesu ya faɗi wannan, waɗanda suke cikin majami’ar suka yi fushi. Ka san abin da ya sa?— Suna tsammani su ne kawai suke da tagomashi na musamman daga wurin Allah. Suna tsammanin sun fi wasu mutane. Saboda haka suka ƙi Yesu domin abin da ya ce. Ka san abin da suka yi ƙoƙarin su yi masa?—

Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Suka kama Yesu suka yi bayan gari da shi. Suka kai shi bakin dutse suna so su jefa shi ƙasa daga saman dutsen su kashe shi! Amma Yesu ya tsira.’—Luka 4:16-30.

Me ya sa waɗannan mutanen suke ƙoƙarin su kashe Yesu?

Idan haka ya faru da kai, za ka sake zuwa ka yi wa waɗannan mutane magana game da Allah?— Hakan zai bukaci gaba gaɗi, ko ba haka ba ne?— Amma bayan kamar shekara guda, Yesu ya sake zuwa Nazarat. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya koya musu cikin majami’arsu.” Yesu bai daina faɗar gaskiya ba domin tsoron mutane waɗanda ba su da ƙaunar Allah.—Matta 13:54.

Wata rana kuma, ranar Asabarci, Yesu yana wani wurin da akwai mutumin da hannunsa ya shanye. Yesu yana da iko daga wurin Allah ya warkar da mutumin. Amma wasu mutanen da suke wajen suna so su jawo wa Yesu masifa. Menene Babban Malamin ya yi?—  Da farko ya yi tambaya: ‘Idan kuna da tunkiya da ta faɗi cikin babban rami a ranar Asabarci, za ka cire ta?’

E, za su yi haka ga tunkiya, har a ranar Asabarci, a ranar da ake so su huta. Saboda haka, Yesu ya ce: ‘Ya fi ma a taimaki mutum ranar Asabarci, tun da mutum ya fi tunkiya daraja!’ Ya bayyana sarai cewa Yesu ya kamata ya taimaki wannan mutumin!

Saboda haka, Yesu ya gaya wa mutumin ya miƙe hannunsa. A take ya warke. Mutumin ya yi farin ciki ƙwarai! Amma waɗannan mutanen kuma fa? Sun yi farin ciki?— A’a. Suka sake ƙin Yesu. Suka fita suka yi shawarar su kashe shi!—Matta 12:9-14.

Kamar wannan ranar ne. Kome muka yi ba za mu faranta wa kowa rai ba. Saboda haka, dole ne mu yanke shawara game da wanda za mu faranta wa rai. Idan Jehovah ne da kuma Ɗansa, Yesu Kristi, to dole ne mu yi abin da suka koyar ko da yaushe. Amma idan muka yi haka, waye zai ƙi mu? Waye zai sa ya yi mana wuya mu yi abin da yake da kyau?—

Shaiɗan zai yi haka. Kuma da waye?— Waɗanda Iblis ya ruɗe su suka yarda da abubuwa da ba su da kyau. Yesu ya gaya wa shugabannan addinin zamaninsa: “Ku na ubanku Shaiɗan ne, ƙyashe ƙyashe na ubanku kuma kuna da nufi ku yi.”—Yohanna 8:44.

Da akwai mutane da yawa da Shaiɗan yake so. Yesu ya kira su “duniya.” Menene kake tsammanin “duniya” take nufi da Yesu ya yi magana game da ita?— Bari mu ga Yohanna sura 15, aya 19, ka gani? A nan mun karanta wannan kalmomin Yesu: “Da na duniya ne ku, da duniya ta yi ƙaunar nata; amma domin ku ba na duniya ba ne, amma ni na zaɓe ku daga cikin duniya, saboda wannan duniya tana ƙinku.”

Saboda haka, wannan duniya da ta ƙi almajiran Yesu, na dukan mutane ne da ba mabiyansa ba. Me ya sa duniya ta ƙi almajiran  Yesu?— Ka yi tunani game da wannan. Waye ne yake mallakar duniyar?— Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” Shaiɗan Iblis shi ne mugun.—1 Yohanna 5:19.

Yanzu ka ga abin da ya sa yake da wuya a yi abin da yake da kyau?— Shaiɗan da duniyarsa suna sa yanayi ya yi wuya. Amma da wani dalili kuma? Ka tuna ko menene wannan?— A Babi na 23 na wannan littafi, mun koyi cewa dukanmu an haife mu da zunubi. Ba zai yi kyau ba ne idan zunubi, Iblis, da kuma duniyarsa suka shuɗe?—

Sa’ad da wannan duniya ta shige, menene zai faru da waɗanda suka yi abin da yake da kyau?

Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari: “Duniya tana shigewa.” Wannan yana nufi ne cewa dukan waɗanda ba sa bin Babban Malami ba za su ƙara kasancewa ba. Ba za a ƙyale su su rayu har abada ba. Ka san waɗanda za su rayu har abada?— Littafi Mai Tsarki ya ci gaba da cewa: “Wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.” (1 Yohanna 2:17) Hakika, waɗanda suka yi abu mai kyau ne kawai, waɗanda suka yi “nufin Allah,” za su rayu har abada a sabuwar duniya ta Allah. Saboda haka, ko yana da wuya, muna so mu yi abin da yake da kyau, ko ba ma so ne?—

Mu karanta tare waɗannan nassosi da suka nuna abin da ya sa yake da wuya a yi abin da yake da kyau: Matta 7:13, 14; Luka 13:23, 24; da kuma Ayukan Manzanni 14:21, 22.