Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 23

Abin da Ya Sa Mutane Suke Rashin Lafiya

Abin da Ya Sa Mutane Suke Rashin Lafiya

KA SAN wani wanda ba shi da lafiya?— Wataƙila kai ma da kanka wani lokaci kana rashin lafiya. Wataƙila mura ya dame ka, ko kuma ka yi ciwon ciki. Wasu mutane suna rashin lafiya sosai. Ba za su iya tashi da kansu ba, ba tare da wani ya taimake su ba. Wannan yana yawan faruwa ne sa’ad da mutane suka tsufa sosai.

Kowa yana rashin lafiya wani lokaci. Ka san abin da ya sa mutane suke rashin lafiya, suke tsufa, kuma suke mutuwa?— Wata rana aka kawo wani mutum da ba ya iya tafiya wurin Yesu, sai Yesu ya nuna abin da ya sa mutane suke rashin lafiya kuma suke mutuwa. Bari in ba ka labari.

Yesu ya sauka a wani gida a wani gari kusa da Tekun Galili. Taron jama’a ta zo ta gan shi. Mutane da yawa ne suka zo wurinsa a cikin gidan har da wasu ba su samu shiga ba. Babu wanda zai iya zuwa kusa da ƙofar ma. Duk da haka mutane, suka ci gaba da zuwa! Wasu mutane suka kawo wani mutum bai iya tafiya ba mai shan inna. Mutane huɗu ne suka ɗauke shi a kan ƙaramin gado.

Ka san abin da ya sa suke so su kawo wannan mutum mai rashin lafiya wurin Yesu?— Sun gaskata cewa Yesu zai iya taimakonsa. Sun gaskata cewa Yesu zai iya warkar da wannan ciwon. Ka san yadda suka shigar da wannan mutumin wajen Yesu da dukan mutanen nan a cikin gidan?—

Hoton da kake gani a nan ya nuna yadda suka yi. Da farko, suka ɗora mutumin a kan jinka. Jinkar shimfiɗaɗɗiya ce. Sai suka huda  babban rami. A ƙarshe suka saukar da mutumin ta ramin zuwa cikin ɗakin. Lallai suna da bangaskiya!

Dukan mutane da suke gidan suka yi mamaki da suka ga abin da ya faru. Mutumin da yake da shan inna ya sauka a tsakiyarsu. Yesu ya yi fushi ne da ya ga abin da mutanen suka yi?— Bai yi fushi ba ko kaɗan! Ya yi farin ciki domin suna da bangaskiya. Ya gaya wa mutum mai shan inna: “An gafarta zunubanka.”

Menene Yesu ya gaya wa mutum mai shan inna ya yi?

Wasu mutanen suna tunani ba daidai ba ne Yesu ya faɗi haka. Ba su yi tsammanin zai iya gafarta zunubai ba. Domin ya nuna musu lallai zai iya, Yesu ya ce wa mutumin: “Ka tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka tafi gidanka.”

 Da Yesu ya faɗi haka, sai mutumin ya warke! Ba shi da shan inna kuma. Yanzu shi da kansa yake iya tashi kuma ya yi tafiya. Mutanen da suka ga wannan mu’ujiza suka yi mamaki. Ba su taɓa ganin abin mamaki irin wannan ba a dukan rayuwarsu! Suka yabi Jehovah domin ya ba su wannan Babban Malami, wanda zai iya warkar da mutane marasa lafiya.—Markus 2:1-12.

Menene muka koya daga wannan mu’ujiza?

Menene muka koya daga wannan mu’ujiza?— Mun koyi cewa Jehovah yana da iko ya gafarta zunubi kuma ya warkar da mutane masu rashin lafiya. Muka koyi wani abu kuma, wani abu mai muhimmanci. Mun koyi cewa mutane suna rashin lafiya ne domin zunubi.

Tun da dukanmu muna yin rashin lafiya wani lokaci, wannan yana nufi ne cewa dukanmu masu zunubi ne?— E, Littafi Mai Tsarki ya ce dukanmu an haife mu cikin zunubi. Ka san abin da yake nufi a haifi mutum cikin zunubi?— Yana nufin cewa an haife mu ajizai. Muna yin abubuwa da ba daidai ba wani lokaci ko ma ba ma son mu yi haka. Ka san yadda dukanmu muka kasance da zunubi?—

Mun kasance haka domin mutum na farko Adamu bai yi wa Allah biyayya ba. Ya yi zunubi sa’ad da ya taka dokar Allah. Kuma dukanmu muka sami zunubi daga wurin Adamu. Ka san yadda muka sami zunubinmu daga wurinsa? Bari in yi bayani a hanyar da za ka fahimta.

Ta yaya dukanmu muka sami zunubi?

Wataƙila ka taimaki wani ya gasa burodi a cikin gwangwaninsa.  Menene zai sami burodin idan gwangwanin a lanƙwashe yake? Ka san abin da zai faru?— Wannan lanƙwasar za ta bayyana a dukan burodi da ka yi a cikin wannan gwangwani, ko ba zai lanƙwashe ba?—

Adamu kamar wannan gwangwanin yake, mu kuma kamar burodin muke. Ya zama ajizi sa’ad da ya taka dokar Allah. Kamar a ce ya lanƙwashe ne. Ta haka, idan ya haifi yara, yaya za su zama?— Dukan yaransa za su sami wannan lanƙwasar ta ajizanci su ma.

Yawancin yara ba a haifansu da ajizanci da za ka iya gani ba. Alal misali, ba hannu guda ko kuma ƙafa guda suke da shi ba. Amma ajizanci da suke da shi yana da tsanani da suke rashin lafiya kuma su mutu da shigewar lokaci.

Hakika, wasu mutane suna rashin lafiya fiye da wasu. Me ya sa haka? Domin an haife su da zunubi da yawa ne?— A’a, dukan mutane an haife su da zunubi iri ɗaya ne. An haife mu ajizai. Saboda haka, ko ba jima ko ba daɗe, kowa zai kamu da wani irin rashin lafiya. Har da mutane da suke ƙoƙarin su kiyaye dokokin Allah da ba sa yin wani abu da ba shi da kyau suna rashin lafiya.

Wace irin lafiya za mu samu sa’ad da zunubinmu ya ƙare?

To, me ya sa wasu suke rashin lafiya fiye da wasu?— Da akwai dalilai da yawa. Wataƙila ba su da isashen abin da za su ci. Ko kuma ba sa cin abin da ya dace. Wataƙila suna cin nakiya da yawa da minti. Wani dalili kuma wataƙila ba sa barci da wuri domin haka ba sa samun isashen barci. Ko kuma wataƙila ba sa saka kaya da zai ɗimama su lokacin sanyi. Jikin wasu mutane ya raunana sosai, shi  ya sa ba za su iya faɗā da cuta ba, ko idan suna ƙoƙarin su kula da kansu.

Za a yi lokaci kuwa da ba za mu yi rashin lafiya ba? Za mu taɓa rabuwa da zunubi kuwa?— To, menene Yesu ya yi wa wannan mutumin mai shan inna?— Yesu ya gafarta masa zunubansa kuma ya warkar da shi. Ta wannan hanyar, Yesu ya nuna abin da zai yi wata rana ga dukan waɗanda suka yi ƙoƙari su yi abin da yake da kyau.

Idan muka nuna cewa ba ma so mu yi zunubi, muna ƙin abin da ba shi da kyau, Yesu zai warkar da mu. Zai cire mana ajizanci da yanzu muke da shi a nan gaba. Zai yi haka tun da shi Sarki ne na Mulkin Allah. Ba za a cire zunubi ba a gare mu a take. Za a cire a hankali. Sa’ad da zunubinmu ya ƙare, ba za mu taɓa yin rashin lafiya ba kuma. Dukanmu za mu kasance da koshin lafiya. Wannan lallai albarka ce!

Domin ƙarin bayani game da yadda zunubi ya shafi dukan mutane, karanta Ayuba 14:4; Zabura 51:5 (50:7, “Dy”); Romawa 3:23; 5:12 da kuma 6:23.