Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kammalawa

Kammalawa

Ka taɓa tunanin abubuwa masu ban farin ciki da ka yi tare da mutanen Jehobah? Kamar halartan taron ikilisiya mai daɗi ko babban taro mai ban farin ciki ko wani abin farin ciki da ka shaida a wa’azi ko kuma wani tattaunawa mai ban ƙarfafa da ka yi da wani ɗan’uwa? Ba ka manta da Jehobah ba, shi kuma bai manta da kai ba. Bai manta da hidimar da ka yi da aminci ba, kuma hakan yana sa shi farin ciki. Ƙari ga haka, yana so ya taimaka maka ka komo gare shi.

Jehobah ya ce: “Zan biɗi tumakina, in bi sawunsu. Kamar yadda makiyayi yakan bi sawun tumakinsa . . . , haka nan ni kuma zan bi sawun tumakina; in cece su daga cikin dukan wuraren da an warwatsar da su.”—Ezekiyel 34:11, 12.