Ka ji dadin abubuwan da ka koya?
Za ka so ka ƙara koya game da Littafi Mai Tsarki?
Wannan soma taɓi ne na abubuwan da ke cikin littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki.
Littafin da kuma nazarin kyauta ne. Za mu so mu yi nazari da kai a wuri da kuma lokaci da kake so.
A wannan nazarin, za ka koyi batutuwa da yawa kamar su:
Dalilin da ya sa aka halicce mu
Yadda za mu samu kwanciyar hankali
Yadda iyalinmu za ta riƙa farin ciki
Abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya ce za su faru a nan gaba
Don ka sami littafin kuma ka ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki, ka tuntuɓi Shaidun Jehobah ko kuma ka cika fom a dandalin jw.org.