Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 6

Yadda Haihuwa Take Shafan Aure

Yadda Haihuwa Take Shafan Aure

“’Ya’ya gādo ne daga wurin Ubangiji.”Zabura 127:3

Haihuwar jariri tana sa farin ciki da kuma gajiya. Bayan haihuwarku ta farko, za ku ga cewa kuna ba da yawancin lokacinku da kuzarinku wajen kula da jaririnku. Rashin isashen barci da dare da kuma canjin yanayin da ke zuwa da haihuwa suna iya shafan dangantakarku. Kai da matarka kuna bukatar ku yi gyara don ku kula da jaririn kuma ku ci gaba da jin daɗin aurenku. Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimaka muku ku shawo kan waɗannan ƙalubalen?

1 KU FAHIMCI YADDA HAIHUWA ZA TA SHAFI RAYUWARKU

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ƙauna tana sa haƙuri da kirki.” Ƙari ga haka, ƙauna “ba ta sa sonkai, ba ta jin tsokana.” (1 Korintiyawa 13:4, 5, Littafi Mai Tsarki) A matsayin sabuwar mahaifiya, za ki mayar da hankalinki gaba ɗaya ga jaririnki, kuma hakan yana iya sa maigidanki ya ji kamar ba ki damu da shi ba. Saboda haka, kada ki manta cewa shi ma yana bukatar lokacinki. Idan kika bi da shi cikin haƙuri, zai fahimci cewa yana da amfani kuma yana taimakawa wajen kula da jaririnku.

“Ku mazaje, ku zauna da matayenku bisa ga sani.” (1 Bitrus 3:7) Ka san cewa matarka za ta yi amfani da kuzarinta sosai wajen kula da jaririnku. Ƙarin aikin da jaririn yake ba ta yana iya gajiyar da ita ko kuma ya sa ta baƙin ciki. A wasu lokatai ma tana iya yin fushi da kai. Amma kada hakan ya tayar maka da hankali, domin Littafi Mai Tsarki ya ce ‘mai-jinkirin fushi ya fi mai-iko.’ (Misalai 16:32) Ka kasance da fahimi kuma ka taimaka mata.Misalai 14:29.

SHAWARA:

  • Ubanni: Ku taimaka wa matanku wajen kula da jaririnku, ko da da dare ne. Ku rage yawan ayyukan da kuke yi don ku sami lokacin kasancewa da matanku da kuma jaririnku

  • Iyaye mata: Idan mazajenku suna so su taimaka wajen kula da jaririn, kada ku ƙi. Idan ba su kula da jaririn yadda kuke so ba, kada ku kushe su. Amma da ladabi, ku nuna musu yadda za su yi hakan da kyau

2 KU ƘARFAFA DANGANTAKARKU

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Za su zama nama ɗaya.” (Farawa 2:24) Duk da cewa kun sami ƙaruwa a iyalinku, ku tuna cewa ku biyu “nama ɗaya” ne har ila. Ku yi ƙoƙari sosai wajen ƙarfafa dangantakarku.

Mata, ku yi wa mazajenku godiya don taimakon da suke yi muku. Idan kuna yaba musu, hakan zai ƙarfafa su kuma ya zama kamar ‘warkarwa’ a gare su. (Misalai 12:18, LMT) Mazaje, ku riƙa gaya wa matanku cewa kuna ƙaunarsu sosai kuma kuna daraja su. Ku yaba musu don yadda suke kula da iyalin.Misalai 31:10, 28.

‘Ba dai kowa yana lura da nasa abu ba, amma kowanne a cikinku yana lura da na waɗansu kuma.’ (Filibiyawa 2:4) A kowane lokaci, ka riƙa yin abin da zai amfani matarka. A matsayinku na ma’aurata, ku nemi lokacin tattauna, ku yaba ma juna kuma ku saurari juna. Idan ya zo ga batun jima’i kada ku nuna son kai. Ku biya wa kowannenku hakkinsa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku hana ma juna, sai dai da yardan juna.” (1 Korintiyawa 7:3-5) Saboda haka, ku tattauna wannan batun da kyau. Ta wajen nuna haƙuri da kuma fahimi, za ku ƙarfafa dangantakarku.

SHAWARA:

  • Ku riƙa keɓe lokacin tattaunawa tsakaninku

  • Ku riƙa yi wa juna abubuwan da za su nuna cewa kuna ƙaunar juna, kamar aika wa juna saƙo ko kuma yi wa juna kyauta

3 YADDA ZA KU YI RAINON ƊANKU

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Tun kana jariri fa ka san littattafai masu-tsarki, waɗanda ke da iko su hikimtar da kai zuwa ceto.” (2 Timotawus 3:15) Ku tsara yadda za ku koyar da jaririnku. Ku san cewa jarirai suna iya koyo tun suna ciki kuma za su iya gane muryarku kuma su san yadda kuke ji. Ku riƙa yi wa jaririnku karatu. Ko da yake ba zai fahimci abin da kuke karantawa ba, hakan zai taimaka masa ya so yin karatu sa’ad da ya girma.

Ko da yake jariri ne, ya kamata ya ji ku kuna tattaunawa game da Allah kuma ya ji kuna addu’a ga Jehobah. (Kubawar Shari’a 11:19) Sa’ad da kuke wasa tare, ku yi magana a kan abubuwan da Allah ya halitta. (Zabura 78:3, 4) Yayin da yaronku yake girma, zai ga cewa kuna ƙaunar Jehobah kuma hakan zai sa ya ƙaunaci Jehobah.

SHAWARA:

  • Ku roƙi Allah ya ba ku hikimar yin renon jaririnku

  • Ku riƙa maimaita wa jaririnku abubuwan da kuke so ya sani don ya soma koyo da wuri