Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 8

Sa’ad da Bala’i Ya Auku

Sa’ad da Bala’i Ya Auku

‘A kan wannan ne kuke da matuƙar farin ciki, ko da yake da ɗan lokaci za ku yi baƙin ciki ta dalilin gwaje-gwaje iri iri.’—1 Bitrus 1:6, Littafi Mai Tsarki

Ko da kuna zaman lafiya da iyalinku, abubuwa suna iya faruwa ba zato da za su sa ku baƙin ciki. (Mai-Wa’azi 9:11) Allah ya yi mana tanadin abin da zai taimake mu sa’ad da bala’i ya auku. Idan kuka bi waɗanda ƙa’idodi daga Littafi Mai Tsarki, kai da iyalinka za ku iya jure matsaloli, har da masu tsanani.

1 KU DOGARA GA JEHOBAH

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: ‘Ku zuba dukan alhininku a bisansa, domin yana kula da ku.’ (1 Bitrus 5:7) A kowane lokaci, ku tuna cewa ba Allah ba ne sanadin matsalolin da kuke fuskanta ba. (Yaƙub 1:13) Idan kuka kusace shi, zai taimaka muku sosai. (Ishaya 41:10) “Ku zazzage zuciyarku a gabansa.”Zabura 62:8.

Za ku sami ƙarfafawa sa’ad da kuka karanta Littafi Mai Tsarki kuma kuka yi nazarinsa a kowace rana, kuma za ku shaida yadda Jehobah yake “yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu.” (2 Korintiyawa 1:3, 4; Romawa 15:4) Jehobah ya yi mana alkawari cewa “salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa” za ta kasance da mu.”Filibiyawa 4:6, 7, 13.

SHAWARA:

  • Ku roƙi Jehobah ya taimake ku ku natsu don ku yi tunani sosai

  • Ku yi la’akari da dukan zaɓin da kuke da shi sa’an nan ku yi amfani da mafi kyau daga cikinsu

2 KU KULA DA LAFIYARKU DA NA IYALINKU

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Zuciyar mai-hankali ta kan sami ilimi: Kunnen mai-hikima kuma yana biɗan sani.” (Misalai 18:15) Ku bincika dukan bayanan da za su taimaka muku. Ku yi ƙoƙari ku san abin da kowa a cikin iyalinku yake bukata. Ku tattauna da su kuma ku saurare su sa’ad da suke magana.Misalai 20:5.

Idan aka yi muku rashi kuma fa? Kada ku ji tsoron nuna cewa kuna baƙin ciki. Ku tuna cewa ko Yesu da kansa ma “ya yi kuka.” (Yohanna 11:35; Mai-Wa’azi 3:4) Samun isashen hutu da kuma barci yana da muhimmanci. (Markus 6:31) Hakan zai taimaka muku ku jure da yanayi mai wuya.

SHAWARA:

  • Ku riƙa tattaunawa sosai a matsayin iyali a kowane lokaci. Idan kuna yin hakan, tattaunawa ba za ta yi muku wuya ba sa’ad da bala’i ya auku

  • Ku yi magana da wasu da suka taɓa shiga yanayinku

3 KU NEMI TAIMAIKO

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Aboki kullayaumi ƙauna ya ke yi,” kuma yana kama da ɗan’uwan da aka haifa “domin kwanakin shan wuya.” (Misalai 17:17) Abokanku za su so su taimake ku amma ba su san abin da ya kamata su yi ba. Kada ku ƙi gaya musu ainihin abin da kuke bukata. (Misalai 12:25) Ƙari ga haka, ku nemi taimako daga wurin waɗanda suka san Littafi Mai Tsarki a kan yadda za ku bi ƙa’idodin da ke cikinsa. Shawarar da suka ba ku daga Littafi Mai Tsarki za ta taimaka muku sosai..—Yaƙub 5:14.

Idan kuka yi tarayya da mutanen da suka yi imani da Allah da kuma alkawuransa, za su ƙarfafa ku. Ƙari ga haka, idan kuka ƙarfafa wasu, ku ma za ku sami ƙarfin gwiwa. Ku bayyana musu abubuwan da kuka gaskata game da Jehobah da kuma alkawuransa. Ku riƙa taimaka ma waɗanda suke bukatar taimako, kuma kada ku yi nisa da waɗanda suke ƙaunar ku.Misalai 18:1; 1 Korintiyawa 15:58.

SHAWARA:

  • Ku tattauna batun da aminanku kuma ku bari su taimaka muku

  • Ku gaya musu ainihin abin da ke damun ku