Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 5

Yadda Za Ku Zauna Lafiya da Danginku

Yadda Za Ku Zauna Lafiya da Danginku

“Ku ɗau halin . . . kirki, da tawali’u, da salihanci, da haƙuri.”Kolosiyawa 3:12, Littafi Mai Tsarki

Aure yana haifar da sabon iyali. Ko da yake kana bukatar ka ci gaba da yi wa iyayenka ladabi kuma ka ƙaunace su, amma bayan ka yi aure, matarka ta fi kowa a nan duniyar muhimmanci a gare ka. Wasu iyayen ba za su fahimci hakan ba. Duk da haka, ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka maka ka san yadda za ka zauna lafiya da iyayenka da kuma surukanka yayin da kake ƙoƙarin ƙarfafa sabon iyalinka. Za a iya yin amfani da dukan ƙa’idodin da aka ambata a wannan talifin sa’ad da ake sha’ani da ’yan’uwa, surukai, kawunai, gwaggo, kakanni da sauran dangi.

1 KU KASANCE DA RA’AYIN DA YA DACE GAME DA SURUKANKU

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ka girmama ubanka da uwarka.” (Afisawa 6:2) Kome yawan shekarunka, wajibi ne ka riƙa girmama iyayenka. Ka tuna cewa matarka ma tana da iyaye kuma tana bukatar ta kula da su. Kada dangantakar da ke tsakanin matarka da iyayenta ta sa ka yin kishi, domin “ƙauna ba ta jin kishi.1 Korintiyawa 13:4; Galatiyawa 5:26.

SHAWARA:

  • Ka guji yin furuci kamar su “Iyalinki sun cika raina ni” ko kuma “Babu abin da na taɓa yi da ya gamshi mahaifiyarki”

  • Ka yi ƙoƙari ka fahimci matarka

2 KU TASHI TSAYE IDAN DA BUKATA

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: ‘Mutum za ya rabu da ubansa da uwarsa, ya manne wa matarsa: za su zama nama ɗaya kuma.’ (Farawa 2:24) Bayan ka yi aure, iyayenka suna iya yin tunanin cewa har yanzu kana ƙarƙashinsu, kuma hakan zai sa su so su riƙa yawan sa baki a aurenku.

Kai da matarka ne za ku kafa musu iyaka domin kada su wuce gona da iri, sa’an nan ku bayyana musu hakan da ladabi. Za ku iya gaya musu abin da ke zuciyarku ba tare da raini ba. (Misalai 15:1) Idan kuna da haƙuri da kuma sauƙin kai, za ku ji daɗin dangantakarku da surukanku kuma za ku ci gaba da yin “haƙuri da junanku cikin ƙauna.”—Afisawa 4:2.

SHAWARA:

  • Idan kun damu sosai da yadda surukanku suke yawan sa baki a sha’aninku, ku tattauna hakan da matarku bayan kome ya lafa

  • Ku bari bakinku ya zo ɗaya a kan yadda za ku riƙa bi da irin wannan batu