NA 2
SASHEKada Ku Ci Amanar Juna
“Abin da Allah ya gama fa, kada mutum ya raba.”
Jehobah ya umurce mu da cewa: “Kada ku ci amana.” (Malakai 2:16) Wannan ya nuna cewa riƙon amana yana da muhimmanci sosai a aure domin idan babu riƙon amana a aure, ma’aurata ba za su yarda da juna ba. Kuma sai da yarda ake ƙauna.
A yau, cin amana tsakanin ma’aurata ya zama ruwan dare gama-gari. Idan kana so ka kāre aurenka daga wannan matsalar, wajibi ne ka yi abubuwa biyu masu muhimmanci.
1 KU BA WA AURENKU FIFIKO
ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: Ku zaɓi “mafifitan al’amura.” (Filibiyawa 1:10) Ɗaya daga cikin abubuwa mafifita a rayuwarku shi ne aurenku. Saboda haka, kuna bukatar ku ba aurenku fifiko.
Jehobah yana so ka kula da matarka sosai kuma ku yi ‘farin ciki’ tare. (Mai-Wa’azi 9:9) Ya bayyana sarai cewa bai kamata ku yi watsi da juna ba ko kaɗan, amma ku nemi hanyoyin faranta wa juna rai. (1 Korintiyawa 10:24) Ka nuna wa matarka cewa tana da muhimmanci sosai a rayuwarka kuma tana da tamani.
SHAWARA:
-
Ka tabbata cewa kana keɓe lokaci a kai a kai don ka kasance tare da matarka kuma kada ka bar kome ya janye hankalinka yayin da kuke tare
-
A duk abin da za ka yi, ka riƙa tunawa da matarka
2 KU KĀRE ZUCIYARKU
BIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: ‘Duk wanda ya dubi mace har ya yi sha’awarta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.’ (Matta 5:28) Idan mutumin da yake da aure yana tunanin abubuwan da za su riƙa tayar masa da sha’awa, to yana cin amanar matarsa ke nan.
Jehobah ya ce “ka kiyaye zuciyarka.” (Misalai 4:23; Irmiya 17:9) Idan kana so ka yi hakan, wajibi ne ka kiyaye idanunka. (Matta 5:29, 30) Ka yi koyi da Ayuba, wanda ya ƙulla yarjejeniya da idanunsa cewa ba zai taɓa kallon wata mace har ya yi sha’awar ta ba. (Ayuba 31:1) Ka ƙudura cewa ba za ka yi sha’ani da duk wani abin batsa ba ko kuma ka yi sha’awar wata da ba matarka ba.
SHAWARA:
-
Ka nuna wa kowa cewa ka ƙuduri anniyar kasancewa da aminci ga matarka
-
Idan matarka ba ta son zumuncin da ke tsakaninka da wata, ka yanke zumuncin nan da nan