Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwa

Gabatarwa

‘Ka zama mai-koyi da waɗanda ke gādan alkawarai ta wurin bangaskiya da haƙuri.’—IBRANIYAWA 6:12.

1, 2. Yaya wani mai kula mai ziyara da ya manyanta ya ɗauki mutanen da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki, kuma me ya sa su abokan kirki ne?

BAYAN wata ’yar’uwa ta saurari jawabin wani mai kula mai ziyara da ya manyanta, sai ta ce: “Yana magana game da mutanen da aka ba da labarinsu a cikin Littafi Mai Tsarki kamar abokansa ne a dā.” Abin da ’yar’uwar nan ta ce gaskiya ne, domin wannan ɗan’uwan ya kwashe shekaru yana nazarin Kalmar Allah da kuma koyar da ita. Hakan ne ya sa waɗannan maza da mata da aka ba da labarinsu a cikin Littafi Mai Tsarki suka zama musu kamar abokan da ya sani tun da daɗewa.

2 Zai yi kyau waɗannan maza da mata da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki su zama abokanmu. Kana ɗaukansu kamar wannan ɗan’uwan kuwa? Ka yi tunanin yadda zai kasance idan ka yi magana da kuma sha’ani da mutane kamar su Nuhu da Ibrahim da Ruth da Iliya da kuma Esther. Ka yi tunanin yadda za su yi tasiri a rayuwarka da kuma irin shawara da ƙarfafa da za su yi maka.—Karanta Misalai 13:20.

3. (a) Ta yaya za mu iya amfana daga yin nazari a kan bangaskiyar maza da mata da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

3 Babu shakka, a lokacin ‘tashin matattu na masu-adalci,’ ƙulla irin wannan dangantakar za ta yi sauƙi. (A. M. 24:15) Amma har ila, za mu iya amfana ta wajen yin nazari a kan bangaskiyar maza da mata da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki. Ta yaya? Manzo Bulus ya ba da shawarar da ke gaba, ya ce: ‘Ka zama mai-koyi da waɗanda ke gādan alkawarai ta wurin bangaskiya da haƙuri.’ (Ibran. 6:12) Yayin da za mu soma nazarin abubuwa dabam-dabam game da maza da mata masu bangaskiya, bari mu yi la’akari da wasu tambayoyin da za mu iya yi don abin da Bulus ya faɗa. Mece ce bangaskiya, kuma me ya sa muke bukatarta? Ta yaya za mu iya yin koyi da maza da mata masu aminci na zamanin dā?

Mece Ce Bangaskiya Kuma Me Ya Sa Muke Bukatarta?

4. Mene ne mutane suke zato game da bangaskiya, kuma me ya sa hakan kuskure ne?

4 Bangaskiya hali ne mai kyau da maza da matan da za mu tattauna a wannan littafin suka daraja sosai. Mutane da yawa a yau ba sa daraja bangaskiya, suna zato cewa tana nufin sa rai a abin da ba mu da tabbaci a kansa. Amma dai, hakan kuskure ne. Bangaskiya ba ta ruɗan mu kuma ba yadda muke ji ba ne. Irin wannan ra’ayin ba shi da kyau domin yadda muke ji zai iya canjawa, kuma bauta wa Allah da irin wannan ra’ayin bai dace ba domin har “aljanu kuma suna gaskantawa, suna kuwa rawan jiki.”—Yaƙ. 2:19.

5, 6. (a) Bangaskiyarmu ta ƙunshi waɗanne abubuwa biyu ne da ba a gani? (b) Shin ya kamata bangaskiyarmu ta yi ƙarfi? Ka bayyana.

5 Ainihin bangaskiya ba abin da muka gaskata ba ne kawai. Ka tuna yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta bangaskiya. (Karanta Ibraniyawa 11:1.) Bulus ya ce bangaskiya ta ƙunshi abubuwa biyu da ba za mu iya gani ba. Na farko, ta ƙunshi abubuwan da suka wanzu yanzu da “ba a gani ba tukuna.” Ba za mu iya ganin abubuwan da ke cikin sama ɓaro-ɓaro ba, kamar Jehobah Allah da Ɗansa ko kuma Mulkinsa da ya soma sarauta a sama. Na biyu, bangaskiya ta ƙunshi “abin da muke begensa,” wato abubuwan da ba su faru ba tukun. A yanzu, ba za mu iya ganin sabuwar duniyar da Mulkin Allah zai kawo nan ba da daɗewa ba. Shin hakan yana nufin cewa babu ainihin tabbacin waɗannan abubuwan da ba mu gani ba kuma muke begensu?

6 Ko kaɗan! Bulus ya nuna cewa bangaskiya tabbataciya ce. Ya ce bangaskiya ‘ainihin abin da muke begensa ne,’ kuma hakan yana iya nufin “takardar shaida.” A ce wani ya yi maka kyautar gida. Zai iya miƙa maka takardar gidan kuma ya ce, “Ga sabon gidanka.” Ba wai yana nufin za ka zauna a cikin takardar ba, amma takardar shaida ce cewa gidan naka ne. Hakazalika, bangaskiyarmu ta sa mu ji kamar dukan alkawuran da Allah ya yi a cikin Kalmarsa sun riga sun cika domin tabbas, dukansu za su cika.

7. Mene ne ainihin bangaskiya ta ƙunsa?

7 Saboda haka, ainihin bangaskiya ta ƙunshi kasancewa da tabbaci sosai ga Jehobah. Bangaskiya tana sa mu ɗauki Jehobah a matsayin Ubanmu na sama kuma mu dogara cewa dukan alkawuransa za su cika. Bugu da ƙari, bangaskiya tana kamar abu mai rai domin muna bukatar mu ciyar da ita don ta ci gaba da wanzuwa. Wajibi ne mu ci gaba da nuna ta ta ayyukanmu, idan ba haka ba, za ta mutu.—Yaƙ. 2:26.

8. Me ya sa bangaskiya take da muhimmanci?

8 Me ya sa bangaskiya take da muhimmanci? Bulus ya ba da amsa mai daɗaɗawa. (Karanta Ibraniyawa 11:6.) Idan ba mu da bangaskiya, ba za mu iya kusantar Jehobah ko kuma mu faranta masa rai ba. Saboda haka, muna bukatar bangaskiya don mu yi rayuwa cikin jituwa da nufin Jehobah ga mala’iku da kuma ’yan Adam, wato mu ɗaukaka da kuma kusace shi.

9. Mene ne Jehobah ya yi da ya nuna cewa ya san muna bukatar bangaskiya?

9 Jehobah ya san cewa muna bukatar bangaskiya sosai, shi ya sa ya tanadar da misalan da za mu yi koyi da su don mu ƙarfafa bangaskiyarmu. Ya albarkace mu ta wajen tanadar mana da maza masu aminci da suke yin ja-gora a cikin ikilisiyar Kirista. Kalmarsa ta ce: ‘Ka yi koyi da bangaskiyarsu.’ (Ibran. 13:7) Ƙari ga hakan, Manzo Bulus ya ambata “taron shaidu mai-girma,” wato maza da mata na zamanin dā waɗanda suka nuna bangaskiya sosai. (Ibran. 12:1) Babu shakka, akwai maza da mata masu ɗimbin yawa da Bulus bai ambata a littafin Ibraniyawa sura ta 11 ba. Akwai labaran maza da mata, manya da ƙanana daga al’adu dabam-dabam da suka kasance da bangaskiya. Za mu iya yin koyi da waɗannan mutanen a wannan zamanin da babu ruwan yawancin mutane da bangaskiya.

Ta Yaya Za Mu Iya Yin Koyi da Bangaskiyar Wasu?

10. Ta yaya yin nazari zai iya taimaka mana mu yi koyi da maza da mata masu aminci da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki?

10 Ba za mu iya yin koyi da wani ba sai idan mun lura da shi sosai. Yayin da kake karanta wannan littafin, za ka lura cewa an yi bincike sosai da zai taimaka maka ka yi koyi da waɗannan maza da mata masu bangaskiya. Zai dace kai ma ka yi naka bincike game da waɗannan maza da mata. Sa’ad da kake nazarin Littafi Mai Tsarki kai kaɗai, ka yi bincike sosai da littattafan da kake da su. Yayin da kake bimbini a kan abin da ka nazarta, ka yi tunani a kan ƙasa da kuma tarihin waɗannan maza da mata a zuciyarka. Ka ji kamar kana wurin, kana ji da kuma ganin abubuwan da ke faruwa. Mafi muhimmanci ma, ka yi la’akari da yadda mutanen suka ji. Yayin da kake saka kanka cikin yanayin waɗannan maza da mata masu aminci, za ka daɗa fahimtarsu kuma za su zama kamar abokanka na dā.

11, 12. (a) Ta yaya za ka iya kusantar Ibrahim da Saratu sosai? (b) Ta yaya za ka iya yin koyi da misalan Hannatu ko Iliya ko kuma Sama’ila?

11 Idan ka san su sosai, za ka so ka yi koyi da su. Alal misali, a ce kana so ka soma wata sabuwar hidima. Sai ƙungiyar Jehobah ta ce ka ƙaura zuwa wani yankin da ake bukatar masu wa’azi da gaggawa ko kuma aka ce ka gwada wani sabon fasali na yin wa’azi da ba ka saba da shi ba. Shin misalin Ibrahim zai iya taimaka maka yayin da kake bimbini da kuma addu’a game da batun? Shi da Saratu sun yarda su bar rayuwar jin daɗi a ƙasar Ur kuma Jehobah ya albarkace su sosai. Idan ka yi koyi da su, za ka ga cewa ka daɗa sanin su sosai.

12 Hakazalika, a ce wani danginka ko abokinka yana kishinka har ka yi sanyin gwiwa kuma kana son ka ƙi halartar taro. Shin me za ka yi? Ka yi bimbini a kan misalin Hannatu da kuma yadda ta ƙi ƙyale kishin Peninnah ya sa ta sanyin gwiwa. Idan ka yi haka, za ka tsai da shawara mai kyau kuma Hannatu za ta zama abokiyarka. Kuma idan kana ji cewa ba ka da daraja, yin nazari a kan matsalolin da Iliya ya fuskanta da kuma yadda Jehobah ya ƙarfafa shi zai taimaka maka. Bugu da ƙari, matasan da abokan makarantarsu suke matsa musu su yi lalata, za su amfana idan suka yi nazari a kan yadda Sama’ila ya ƙi saka hannu a lalatar da ’ya’yan Eli suka yi a mazaunin.

13. Shin yin koyi da wani da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki zai sa Jehobah ya ƙi daraja bangaskiyarka? Ka bayyana.

13 Shin yin koyi da bangaskiyar waɗannan maza da mata da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki zai sa Jehobah ya ƙi daraja naka bangaskiyar? Sam! Ka tuna cewa Kalmar Jehobah ta ƙarfafa mu mu yi koyi da maza da mata masu bangaskiya. (1 Kor. 4:16; 11:1; 2 Tas. 3:7, 9) Ƙari ga hakan, wasu ma da za mu yi nazari game da su sun yi koyi da maza da mata da suka rayu kafin su. Alal misali, Babi na 17 na wannan littafin ya nuna cewa Maryamu ta yi ƙaulin kalaman Hannatu. Shin hakan ya sa Jehobah ya ƙi daraja bangaskiyar Maryamu? A’a! Maimakon haka, misalin Hannatu ya taimaka wa Maryamu ta kasance da bangaskiya kuma ta zama aminiyar Jehobah.

14, 15. Mene ne wasu fasaloli na wannan littafin, kuma yaya za mu iya yin amfani da su daidai wa daida?

14 Me ya sa aka wallafa wannan littafin? Domin ya taimaka maka ka ƙarfafa bangaskiyarka. An harhaɗa wani talifi mai jigo: “Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu” da aka soma wallafawa a cikin Hasumiyar Tsaro daga shekara ta 2008 zuwa 2013. An ɗan yi wasu gyare-gyare a talifofin da aka wallafa a dā domin su jitu da sababbin talifofin da aka daɗa a cikin wannan littafin kuma don Shaidun Jehobah su amfana sosai. Kowane talifi yana da tambayoyi da za su taimaka mana mu tattauna kuma mu yi amfani da darussan a rayuwarmu. An zana wasu hotuna musamman don wannan littafin. An daɗa girman wasu da ke talifin a dā kuma an ɗan yi musu gyara. An saka wasu sababbin fasaloli kamar su jerin shekaru da kuma taswira. An wallafa wannan littafin don ya taimaka mana sa’ad da muke nazari mu kaɗai da iyalinmu da kuma a ikilisiya. Iyalai da yawa za su kuma ji daɗin karanta labarun tare.

15 Muna fatar cewa wannan littafin zai taimaka maka ka yi koyi da bangaskiyar bayin Jehobah masu aminci na zamanin dā. Kuma fatar mu ce cewa zai taimaka maka ka ƙarfafa bangaskiyarka yayin da kake daɗa kusantar Jehobah.