Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA ASHIRIN DA BIYU

Ya Kasance da Aminci a Lokacin Gwaji

Ya Kasance da Aminci a Lokacin Gwaji

1, 2. Mene ne Bitrus yake zato zai faru sa’ad da Yesu yake wa’azi a Kafarnahum, amma mene ne ya faru?

BITRUS ya kalli fuskokin mutanen da Yesu yake tattaunawa da su a majami’ar da ke Kafarnahum. Garin su Bitrus ke nan kuma nan ne yake sana’ar sū a arewacin Tekun Galili. Abokansa da dangoginsa da kuma abokan sana’arsa suna zama a wannan birnin. Bitrus ya yi zato cewa mutanen za su amince da Yesu a matsayin Almasihu kuma su saurari wa’azinsa game da Mulkin Allah. Amma hakan bai faru ba.

2 Mutane da yawa sun daina sauraron Yesu. Wasu suna gunaguni, ba su amince da koyarwarsa ba. Abin da wasu almajiran Yesu suka yi ne ya ma fi ci wa Bitrus rai. Wani abu da Yesu ya koya musu bai sa su farin ciki kamar dā ba. Wasu sun ce batun da wuya yake. Wasu cikinsu suka fita daga majami’ar kuma suka daina bin Yesu.Karanta Yohanna 6:60, 66.

3. Mene ne bangaskiyar Bitrus ta taimaka masa ya yi sau da yawa?

3 Wannan lokaci mai wuya ne sosai ga Bitrus da kuma sauran manzannin. Bitrus bai fahimci abin da Yesu ya ce a ranar ba. Babu shakka, ya san cewa maganar da Yesu ya faɗa tana da wuyan fahimta idan bai bayyana ta ba. Mene ne Bitrus ya yi? Wannan ba lokaci na farko da aka gwada amincinsa ga Ubangijinsa ba, kuma ba na ƙarshe ba ne. Bari mu ga yadda bangaskiyar Bitrus ta taimaka masa ya kasance da aminci duk da ƙalubalen da ya fuskanta.

Ya Kasance da Aminci Sa’ad da Wasu Suka Ƙi

4, 5. Mene ne Yesu ya yi da mutanen ba su zata ba?

4 Abubuwan da Yesu yake yi suna yawan sa Bitrus mamaki. Ubangijinsa yana faɗin wasu abubuwa a wasu lokatai da mutane da yawa ba su yi zato ba. Kwana ɗaya kafin Yesu ya furta waɗannan kalmomin, ya ciyar da dubban mutane ta mu’ujiza. A sakamako, suka so su naɗa shi sarki. Amma, Yesu ya janye tare da almajiransa kuma ya ce su shiga jirgi su tafi Kafarnahum. Hakan ya sa mutane da yawa mamaki sosai. Sa’ad da almajiran suke cikin jirgin daddare, Yesu ya yi wani abu da ya daɗa sa su mamaki. Ya yi tafiya a kan Tekun Galili da akwai manya-manyan raƙuman ruwa kuma hakan ya daɗa ƙarfafa bangaskiyar Bitrus.

5 Sa’ad da gari ya waye, sai suka ankara cewa mutanen sun bi su zuwa ɗayan hayin kogin. Babu shakka, ba koyarwar Yesu ba ne ya sa suka bi shi ba, amma suna so ya sake ciyar da su ta mu’ujiza. Yesu ya tsauta musu don yadda suke son abin duniya. (Yoh. 6:25-27) Sun ci gaba da tattaunawar a majami’ar da ke Kafarnahum kuma a wurin ne Yesu ya koyar da wata gaskiya mai muhimmanci da ta yi musu wuyar fahimta.

6. Wane kwatanci ne Yesu ya ba da, kuma yaya masu sauraronsa suka ji?

6 Yesu ba ya so mutane su zo wurinsa don sun san cewa zai iya ciyar da su. Amma, yana so su san cewa za su samu rai na har abada idan suka yi imani da fansar da zai yi musu kuma suka bi misalinsa. Sai ya yi musu wani kwatanci inda ya gwada kansa da manna, wato abincin da Allah ya aiko daga sama a zamanin Musa. Sa’ad da wasu suka soma gunaguni, sai Yesu ya ba da wani kwatanci cewa wajibi ne duk mutumin da ke son rai na har abada ya ci namansa kuma ya sha jininsa. A wannan lokacin ne abin da Yesu ya ce ya ɓata musu rai sosai. Wasu suka ce: “Wannan batu da wuya yake; wane ne ya iya jinsa?” Almajiran Yesu da yawa suka daina bin sa. *Yoh. 6:48-60, 66.

7, 8. (a) Mene ne Bitrus bai fahimta ba tukun game da matsayin Yesu? (b) Ta yaya Bitrus ya amsa tambayar da Yesu ya yi wa almajiransa?

7 Mene ne Bitrus zai yi? Babu shakka, abin da Yesu ya ce ya ba shi mamaki. Bai fahimci cewa wajibi ne Yesu ya mutu domin ya cika nufin Allah ba. Shin Bitrus ya so ya daina bin Yesu kamar sauran almajiran ne? A’a. Bitrus ya yi wani abu mai muhimmanci da ya bambanta shi da sauran almajiran da suka daina bin Yesu. Me ke nan?

8 Yesu ya juya ya kalli sauran manzanninsa, ya ce: “Ku kuma kuna so ku tafi?” (Yoh. 6:67) Yesu ya furta waɗannan kalmomin ga almajiransa 12, amma Bitrus ne ya amsa kuma abin da yake yawan yi ke nan. Wataƙila shi ne ya girme su. Ko da hakan ne ko a’a, shi ya fi magana cikinsu kuma yana yawan faɗin ra’ayinsa a fili. Bitrus ya faɗi abin da ba za mu taɓa mantawa ba. Ya ce: “Ubangiji, wurin wa za mu tafi? Kai ne da maganar rai na har abada.”—Yoh. 6:68.

9. Ta yaya Bitrus ya kasance da aminci ga Yesu?

9 Shin waɗannan kalmomin ba su ratsa zuciyarka ba? Bangaskiyar Bitrus ga Yesu ta taimaka masa ya kasance da aminci. Bitrus ya ga cewa Yesu ne kaɗai Mai-ceton da Jehobah ya tanadar kuma koyarwarsa game da Mulkin Allah tana sa a samu ceto. Bitrus ya san cewa ko da akwai abin da bai fahimta ba, dole ne ya kasance tare da Yesu idan yana son tagomashin Allah da kuma rai na har abada.

Muna bukatar mu amince da koyarwar Yesu, ko da sun saɓa da abin da muka sani a dā

10. Ta yaya za mu iya yin koyi da amincin Bitrus a yau?

10 Shin hakan kai ma kake ji? Abin baƙin ciki, mutane da yawa a yau suna da’awar cewa suna ƙaunar Yesu amma ba su da aminci. Idan muna so mu kasance da aminci ga Yesu kamar yadda Bitrus ya yi, wajibi ne mu amince da koyarwarsa. Ya kamata mu koyi waɗannan koyarwar kuma mu fahimce su ko da sun saɓa da abin da muka sani a dā. Sai idan muka kasance da aminci ne za mu yi begen samun rai na har abada da Yesu ya yi alkawari.Karanta Zabura 97:10.

Ya Kasance da Aminci Sa’ad da Aka Yi Masa Gyara

11. Wace tafiya mai nisa ce Yesu da manzanninsa suka yi?

11 Ba da daɗewa ba, Yesu da almajiransa suka nufi arewa. A lokacin, za a iya hangan saman Tudun Harmon daga Tekun Galili cike da ƙanƙara. Suna daɗa ganin tudun sosai yayin da suke kusa da ƙauyen Kaisariya Filibi. Sa’ad da suke wannan tafiyar da suke hangan wani ɓangare na Ƙasar Alkawari ne Yesu ya yi musu wata muhimmiyar tambaya.

12, 13. (a) Me ya sa Yesu ya tambayi mabiyansa ra’ayin jama’a game da shi? (b) Ta yaya amsar da Bitrus ya bayar ta nuna cewa yana da bangaskiya sosai?

12 Yesu ya tambaye su: “Taron suna ce da ni wane ne?” Ka kwatanta a zuci yadda Bitrus ya kalli Yesu yana sane cewa Ubangijinsa yana da kirki da kuma basira. Yesu yana son ya san ra’ayin jama’a game da shi. Almajiransa suka amsa tambayar, sun faɗi wasu wai-wai da ake cewa game da shi. Yesu yana son ƙarin bayani don ya ga ko mabiyansa ma suna wannan kuskuren. Sai ya tambaye su: “Amma ku kuna ce da ni wane ne?”—Luk 9:18-20.

13 A wannan ƙaron ma, Bitrus ne ya amsa da gaggawa. Ya furta ra’ayin sauran manzannin Yesu, ya ce: “Kai Kristi ne, Ɗan Allah mai-rai.” Ka yi tunanin yadda Yesu yake murmushi yana kallon Bitrus yayin da yake ƙarfafa shi. Yesu ya gaya masa cewa Jehobah ne ya bayyana masa wannan gaskiyar ba mutum ba. Jehobah yana bayyana irin wannan gaskiyar ga masu bangaskiyar sosai. Bitrus ya san gaskiya mafi tamani da mutane ba su sani ba tukun, wato bayyanuwar Almasihu ko Kristi da aka yi alkawarinsa tun da daɗewa!Karanta Matta 16:16, 17.

14. Wane gata mai muhimmanci ne Yesu ya danƙa wa Bitrus?

14 Wannan Kristi ne aka yi annabcinsa da daɗewa cewa shi dutse ne wanda magina suka ƙi. (Zab. 118:22; Luk 20:17) Yesu yana magana ne game da wannan annabcin sa’ad da ya ce Jehobah zai kafa ikilisiya bisa dutse kuma shi ne Bitrus ya shaida. Sai ya danƙa wa Bitrus wani matsayi mai muhimmanci sosai a cikin ikilisiya. Wasu mutane sun ce matsayin da aka danƙa wa Bitrus ya fi na sauran manzannin, amma hakan ba gaskiya ba ne. Ya ba Bitrus “mabuɗan Mulkin.” (Mat. 16:18, 19, Littafi Mai Tsarki) Bitrus ne zai sa mutane kashi uku su samu begen shigar Mulkin Sama. Yahudawa da Samariyawa da kuma ’Yan Al’ummai.

15. Me ya sa Bitrus ya tsauta wa Yesu kuma me ya ce?

15 Amma daga baya, Yesu ya ce za a bukaci abu mai yawa daga mutumin da aka danƙa wa gata mai yawa kuma abin da Bitrus ya shaida ke nan. (Luk 12:48) Yesu ya ci gaba da bayyana gaskiya mai tamani game da kansa. Ya ce zai sha wahala kuma za a kashe shi a Urushalima, babu shakka hakan ya dami Bitrus sosai. Sai ya ja Yesu gefe, ya soma tsauta masa, ya ce: “Allah shi sawwaƙa maka, Ubangiji: wannan ba za ya same ka ba daɗai.”—Mat. 16:21, 22.

16. Ta yaya Yesu ya yi wa Bitrus gyara, kuma wane darasi ne dukanmu za mu iya koya daga kalmomin Yesu?

16 Bitrus ya ɗauka cewa yana taimaka wa Yesu ne, amma abin da Yesu ya gaya masa ya ba shi mamaki. Yesu ya juya baya ya kalli sauran almajiransa da wataƙila suna da ra’ayin Bitrus, ya ce: “Ka koma bayana, Shaitan: abin tuntuɓe ka ke a gareni; gama ba ka yi tattalin abin da ke na Allah ba, sai na mutane.” (Mat. 16:23; Mar. 8:32, 33) Kalmomin Yesu suna ɗauke da darasi ga dukanmu. Yana da sauƙi mu ƙyale tunanin mutane su shawo kan na Allah. Idan muka yi hakan ko da muna son mu yi taimako ne, za mu iya goyan bayan Shaiɗan ba da saninmu ba. Mene ne Bitrus ya ce?

17. Mene ne Yesu yake nufi sa’ad da ya ce wa Bitrus “ka koma bayana”?

17 Babu shakka, Bitrus ya san cewa Yesu bai ce shi Shaiɗan Iblis ba ne. Balantana ma, ba abin da Yesu ya ce wa Shaiɗan ya ce wa Bitrus ba. Sa’ad da Yesu yake tsauta wa Shaiɗan, ya ce: “Rabu da ni.” (Mat. 4:10) Mene ne bambancin furucin nan biyu? Yesu bai kori manzonsa mai aminci ba kamar yadda ya yi wa Shaiɗan, amma ya ɗan yi masa gyara ne. Saboda haka, Bitrus yana bukatar ya goyi bayan Yesu maimakon ya zama masa abin tuntuɓe.

Idan muka amince da horo kuma muka yi amfani da shi, za mu ci gaba da kusantar Jehobah da kuma Yesu

18. Ta yaya Bitrus ya nuna cewa yana da aminci, kuma ta yaya za mu yi koyi da shi?

18 Shin Bitrus ya ci mūsu ne ko kuma ya ɓata rai? A’a. Ya amince da gyarar. Ta hakan ya nuna cewa yana da aminci. A wasu lokatai dukan mabiyan Kristi za su bukaci gyara. Sai idan mun amince da gyarar da aka yi mana ne za mu ci gaba da kusantar Yesu da kuma Ubansa, wato Jehobah Allah.Karanta Misalai 10:17.

Bitrus ya kasance da aminci duk da gyarar da aka yi masa

An Albarkace Shi don Amincinsa

19. Wane furci mai ban mamaki ne Yesu ya yi, kuma wane tunani ne wataƙila Bitrus ya yi?

19 Yesu ya daɗa yin wani furci mai ban mamaki, ya ce: “Hakika ina ce maku, akwai waɗansu a cikin na tsaye a wurin nan, da ba za su ɗanɗana mutuwa ba daɗai, har sun ga Ɗan mutum yana zuwa cikin mulkinsa.” (Mat. 16:28) Babu shakka, Bitrus ya so ƙarin bayani a kan wannan zancen. Shin mene ne Yesu yake nufi? Wataƙila Bitrus ya yi tunani cewa gyarar da Yesu ya yi masa zai sa ya ƙi danƙa mai wannan gata na musamman.

20, 21. (a) Ka bayyana wahayin da Bitrus ya gani. (b) Ta yaya zancen da aka yi a wannan wahayin ya daidaita ra’ayin Bitrus?

20 Bayan mako ɗaya, Yesu ya kai Yaƙub da Yohanna da kuma Bitrus “wani dutse mai-tsawo,” wataƙila Tudun Harmon wanda bai da nisa sosai. Mai yiwuwa daddare ne domin mazaje ukun sun yi ta fama da barci. Amma yayin da Yesu yake addu’a, wani abu ya faru da ya sa dukansu suka farka.—Mat. 17:1; Luk 9:28, 29, 32.

21 Sun ga kamanin Yesu ya soma canjawa. Fuskarsa ta soma haske, har ta yi haske sosai kamar rana, rigarsa ma ta zama fara fat. Sai mutane biyu suka bayyana kusa da Yesu, ɗaya yana wakiltar Musa, ɗayan kuma Iliya. Suna tattaunawa da shi game da mutuwarsa da kuma tashiwarsa daga matattu da za su faru a Urushalima. Bitrus ya fahimci cewa bai yi daidai ba da ya ce Yesu ba zai sha wahala ya kuma mutu ba!—Luk 9:30, 31.

22, 23. (a) Ta yaya Bitrus ya nuna alheri da kuma ƙwazo? (b) Wace albarka ce Bitrus da Yaƙub da kuma Yohanna suka samu a daren?

22 Bitrus ya ji cewa ya kamata ya yi wani abu a wannan wahayin. Ya ga kamar Musa da Iliya suna son su bar Yesu, sai ya ce: “Ya yi mana kyau da muna nan zaune: bari mu yi bukkoki uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.” Hakika, waɗannan bayin Jehobah biyu da aka nuna a wahayin ba sa bukatar bukkoki. Bitrus bai yi la’akari da abin da ya faɗa ba. Babu shakka, muna ƙaunarsa don alheri da kuma ƙwazonsa.—Luk 9:33.

An albarkaci Bitrus da Yaƙub da kuma Yohanna ta wajen sa su ga wahayi

23 Bitrus da Yaƙub da kuma Yohanna sun sami wata albarka a daren. Gajimare ya rufe su a kan tudun. Suka ji muryar Jehobah na cewa: “Wannan Ɗana ne, zaɓaɓena: ku ji shi.” Sai aka daina wahayin kuma suka ga Yesu kaɗai tare da su a tudun.—Luk 9:34-36.

24. (a) Ta yaya wahayi ya amfani Bitrus? (b) Ta yaya za mu amfana daga wahayin a yau?

24 Hakika, wannan wahayin baiwa ne ga Bitrus da kuma mu! Bayan wasu shekaru, Bitrus ya rubuta cewa abin da ya gani a daren soma taɓi ne na sarautar Yesu a sama kuma ‘ɗaukakarsa ce ya gani murara.’ Wannan wahayin ya cika wasu annabce-annabce da ke cikin Kalmar Allah kuma ta ƙarfafa bangaskiyar Bitrus don ya iya jimre gwaje-gwajen da zai fuskanta a nan gaba. (Karanta 2 Bitrus 1:16-19.) Wannan wahayin zai iya ƙarfafa bangaskiyarmu ga annabce-annabce game da Yesu da kuma Mulkin Allah. Idan muka kasance da aminci ga Yesu, muka bi koyarwarsa, muka amince da horonsa kuma muka yi koyi da shi a koyaushe, za mu more albarka ta Mulkinsa.

^ sakin layi na 6 Sa’ad da Yesu ya ciyar da jama’ar, sun ce shi annabin Allah ne. Amma washegari, sa’ad da suke majami’a sun faɗi wani abu dabam. Hakan ya nuna cewa kalamansu ba su jitu ba.—Yoh. 6:14.