Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA SHA ƊAYA

Ya Lura, Kuma Ya Jira

Ya Lura, Kuma Ya Jira

1, 2. Wane irin aiki ne Iliya zai yi, kuma ta yaya shi da Ahab suka bambanta?

ILIYA yana so ya kasance shi kaɗai don ya yi addu’a ga Ubansa na sama. Amma, bai daɗe ba da taron jama’a da ke kewaye da wannan annabin gaskiya suka ga ya kira wuta daga sama, kuma babu shakka mutane da yawa cikinsu suna so su sami tagomashinsa. Kafin Iliya ya hau tsololon Dutsen Karmel kuma ya yi addu’a ga Jehobah, an ba shi aiki da ba ya so. Yana bukatar ya yi magana da Sarki Ahab.

2 Da akwai bambanci sosai tsakanin waɗannan mutane biyu. Ahab da ke sanye da tufafi masu kyau na sarauta, mai haɗama ne da kuma ɗan ridda da ke barin mutane su riƙa jujjuya shi. Iliya kuma da ke sanye da tufafin annabi, wanda wataƙila aka yi da fatan raƙumi ko kuma na akuya, mutumi ne mai gaba gaɗi da aminci da kuma bangaskiya. Abubuwan da suka faru wannan ranar ne suka sa aka san halin kowannensu.

3, 4. (a) Me ya sa Ahab da masu bautar Baal suka sha kunya? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

3 Ahab da kuma masu bautar Baal sun sha kunya a wannan ranar. An fallasa ƙaryan addinin arna da Ahab da matarsa Sarauniya Jezebel suke yaɗawa a masarautar ƙabila goma ta Isra’ila. Wannan alla marar rai ya kasa sa wuta ta cinye hadayar, duk da roƙo da rawa da kuma zubar da jini da annabawansa suka yi. Baal ya kasa ceton waɗannan mutane 450 daga halaka. Akwai wata hanya dabam kuma da wannan allan ƙarya ya kasa. Fiye da shekara uku, annabawan Baal suna roƙonsa ya kawo ƙarshen fari da ya addabi ƙasar, amma Baal ya kasa yin haka. Ba da daɗewa ba, Jehobah da kansa zai nuna cewa shi ne Allah na gaskiya ta wajen kawo ƙarshen farin.—1 Sar. 16:30–17:1; 18:1-40.

4 Amma, a yaushe ne Jehobah zai yi hakan? Mene ne Iliya zai yi yayin da yake jiran Jehobah ya aikata? Kuma mene ne za mu koya daga wannan mutumi mai bangaskiya? Bari mu gani yayin da muke bincika labarin.—Karanta 1 Sarakuna 18:41-46.

Ya Ci Gaba da Yin Addu’a

5. Mene ne Iliya ya gaya wa Ahab ya yi, kuma shin da alama ne cewa Ahab ya koyi darasi daga abin da ya faru a ranar?

5 Iliya ya je gaban Ahab, sai ya ce: “Ka hau, ka ci, ka sha; gama da motsin ruwan sama mai-yawa.” Shin wannan mugun sarki ya koyi wani abu kuwa daga abin da ya faru a wannan rana? Ba a ambata hakan a labarin ba, kuma ba mu ga wata kalma ta tuba ba, ko kuma roƙo da Ahab ya yi don annabin ya roƙi Jehobah ya gafarta masa. Ahab dai kawai “ya hau garin ya ci ya sha.” (1 Sar. 18:41, 42) Iliya kuma fa?

6, 7. Mene ne Iliya ya roƙa, kuma me ya sa?

6 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Iliya ya hau ƙwanƙolin Karmel; ya sunkuyar da kansa a ƙasa, ya sa fuskatasa tsakanin guwawunsa.” Sa’ad da Ahab ya tafi ya cika tumbinsa, Iliya ya sami zarafin yin addu’a ga Ubansa da ke sama. Yadda Iliya ya zauna a ƙasa kuma ya sunkuyar da kansa kusa da gwiwoyinsa ya nuna cewa shi mai tawali’u ne. Mene ne Iliya yake yi? Hakika mun sani. Littafin Yaƙub 5:18, ya ce Iliya ya yi addu’a don a kawo ƙarshen farin. Kuma babu shakka ya yi wannan addu’ar ce a kan Dutsen Karmel.

Addu’o’in Iliya sun nuna cewa yana so ya ga an yi nufin Allah

7 Da farko, Jehobah ya ce: ‘Ni ma in aika da ruwa a bisa ƙasa.’ (1 Sar. 18:1) Saboda haka, Iliya ya yi addu’a don nufin Jehobah ya cika, kamar yadda Yesu ya koya wa mabiyansa su yi shekara dubu ɗaya bayan haka.—Mat. 6:9, 10.

8. Mene ne muka koya game da addu’a daga misalin Iliya?

8 Mun koyi abubuwa da yawa game da addu’a daga misalin Iliya. Abin da ya fi muhimmanci ga Iliya shi ne ya ga nufin Allah ya cika. Sa’ad da muka yi addu’a, yana da kyau mu tuna cewa: “Idan mun roƙi komi daidai da nufinsa [Allah], yana jinmu.” (1 Yoh. 5:14) A bayyane yake cewa, muna bukatar mu san nufin Allah domin mu yi addu’ar da zai amsa. Hakan dalili ne mai kyau na yin nazarin Littafi Mai Tsarki kullum. Babu shakka, Iliya ma yana so ya ga cewa an kawo ƙarshen farin domin wahalar da mutanen ƙasar suke sha. Wataƙila kuma ya yi godiya ƙwarai ganin mu’ujiza da Jehobah ya yi a ranar nan. Sa’ad da muke addu’a, ya kamata mu ma mu yi godiya ga Allah kuma mu ambata matsalolin wasu.—Karanta 2 Korintiyawa 1:11; Filibiyawa 4:6.

Yana da Tabbaci Kuma Ya Kasance a Faɗake

9. Mene ne Iliya ya ce baransa ya yi, kuma waɗanne abubuwa biyu ne za mu tattauna?

9 Iliya ya tabbata cewa Jehobah zai kawo ƙarshen wannan farin, amma bai san ranar da zai yi hakan ba. To, mene ne annabin ya yi kafin lokacin? Ka lura da abin da aka ce a labarin: “Ya ce wa baransa, Ka hau yanzu, ka duba wajen teku. Ya hau, ya duba, ya ce, Babu komi. Ya ce, Ka sake tafiya har sau bakwai.” (1 Sar. 18:43) Mun koyi aƙalla darussa biyu daga misalin Iliya. Na farko, annabin yana da tabbaci cewa Jehobah zai cika alkawarinsa. Na biyu kuma ya kasance a faɗake.

Iliya ya yi ɗokin ganin alama cewa Jehobah ya kusa ya kawo ruwa

10, 11. (a) A wace hanya ce Iliya ya nuna cewa ya tabbata Jehobah zai cika alkawarinsa? (b) Me ya sa za mu kasance da irin wannan tabbacin?

10 Domin Iliya yana da tabbaci cewa Jehobah zai cika alkawarinsa, ya yi ɗokin ganin alama cewa Jehobah ya kusa ya aikata. Saboda haka, ya aiki baransa ya hau tudu ya ga ko akwai hadari. Sa’ad da baran ya dawo, sai ya ba shi wannan rahoto mai kashe gwiwa: “Babu komi.” Hakika kuwa, babu alamar hadari a sararin sama. Shin ka lura da wani abu kuwa? Ka tuna cewa bai daɗe ba da Iliya ya gaya wa Sarki Ahab cewa: “Gama da motsin ruwan sama mai-yawa.” Me ya sa annabin zai faɗi haka tun da babu ma ko alamar hadari?

11 Iliya ya san alkawarin da Jehobah ya yi. Da yake shi annabin Jehobah ne da kuma wakilinsa, yana da tabbaci cewa Allahnsa zai cika alkawarinsa. Iliya yana da tabbaci sosai da har yana ji kamar an soma ruwan. Ƙila hakan zai tuna mana da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Musa: “Ya jimre, kamar yana ganin wanda ba shi ganuwa.” Shin haka Allah yake a gare ka? Allah ya ba mu dalilai masu yawa na kasancewa da irin wannan bangaskiya a gare shi da kuma alkawuransa.—Ibran. 11:1, 27.

12. Ta yaya Iliya ya kasance a faɗake, kuma mene ne ya yi sa’ad da aka gaya masa cewa akwai ɗan girgije?

12 Ka kuma lura da yadda Iliya ya kasance a faɗake. Ya aiki baransa har sau bakwai! Wannan baran ya je aikan sau da yawa, kuma ka yi tunanin yadda ƙila hakan ya gajiyar da shi, amma Iliya ya yi ɗokin ganin alama kuma bai yi sanyin gwiwa ba. A ƙarshe, bayan tafiyarsa ta bakwai, baran ya ba da rahoto: “Ga shi, wani girgije yana tasowa daga cikin teku, ƙanƙani kamar tafin hannun mutum.” Za ka iya tunanin yadda wannan baran ya miƙa hannunsa yana kwatanta girman girgije da ya gani? Wataƙila hakan bai burge baran ba. Amma ga Iliya, wannan girgijen yana da muhimmanci ƙwarai. Sai ya ba baransa umurni na gaggawa cewa: “Tashi, ka ce wa Ahab, Ka shirya karusarka, ka gangara, kada ruwa ya tare ka.”—1 Sar. 18:44.

13, 14. (a) Ta yaya za mu yi koyi da yadda Iliya ya kasance a faɗake? (b) Waɗanne dalilai ne muke da su na aikatawa da gaggawa?

13 Akwai wani misali mai kyau kuma da Iliya ya kafa mana a yau. Mu ma yanzu muna rayuwa ne a lokacin da Allah zai cika nufinsa. Kamar yadda Iliya ya jira ƙarshen farin, bayin Allah a yau ma suna jiran ƙarshen wannan lalataciyar duniya. (1 Yoh. 2:17) Kamar Iliya, muna bukatar mu kasance a faɗake har sai Jehobah Allah ya aikata. Yesu ɗan Allah ya shawarci mabiyansa cewa: “Ku yi tsaro fa: gama ba ku sani ba cikin kowace rana Ubangijinku ke zuwa.” (Mat. 24:42) Shin Yesu yana nufin mabiyansa ba za su san cewa suna zama a kwanaki na ƙarshe ba? A’a, domin ya bayyana dalla-dalla yadda kwanaki na ƙarshe za su kasance. Dukanmu za mu iya sanin alamar “cikar zamani.”—Karanta Matta 24:3-7.

14 Kowane fannin wannan alamar yana ba da ƙwaƙƙwaran tabbaci. Shin ya kamata irin waɗannan tabbaci su motsa mu mu aikata da gaggawa a hidimarmu ga Jehobah? Ɗan ƙaramin girgije kawai da ya taru ya tabbatar wa Iliya cewa Jehobah ya kusa ya kawo ruwa. Shin wannan annabi mai bangaskiya ya ji kunya ne?

Jehobah Ya Kawo Sauƙi da Kuma Albarka

15, 16. Waɗanne abubuwa ne suka faru cikin hanzari, kuma wataƙila wane tunani Iliya ya yi game da Ahab?

15 Labarin ya ce: “Ya zama kuwa kamin an jima kaɗan, sararin sama ya yi baƙi ƙirin da hadari da iska, aka yi babban ruwa kuwa. Ahab ya hau, ya tafi Jezreel.” (1 Sar. 18:45) Abubuwa suka soma faruwa cikin hanzari. Sa’ad da baran Iliya yake idar da saƙon annabin ga Ahab, sai wannan ƙaramin girgijen ya zama hadari mai duhu sosai da ya cika sararin sama. Sai kuma aka yi iska mai ƙarfi. A ƙarshe, an sake yin ruwan sama a ƙasar Isra’ila bayan shekaru uku da rabi. Busashiyar ƙasa ta jiku sharaf. Sa’ad da ruwan saman ya yi ƙarfi, sai kogin Kishon ya cika, kuma babu shakka ya wanke jinin annabawan Baal da aka kashe. Kuma aka ba Isra’ilawa ’yan tawaye zarafin kawar da tasirin bautar Baal daga ƙasar.

“Aka yi babban ruwa kuwa”

16 Hakika Iliya ya kasance da bege cewa za a kawar da bautar Baal daga ƙasar Isra’ila! Wataƙila ya yi tunani a kan abin da Ahab zai yi saboda abubuwan da suke faruwa. Shin Ahab zai tuba kuwa, kuma ya daina bauta wa Baal? Abubuwan da suka faru a wannan ranar sun isa su sa ya yi hakan. Hakika, ba za mu iya sanin abin da Ahab yake tunani a kai ba bayan dukan abubuwan da suka faru a ranar. Labarin kawai ya gaya mana cewa sarki “ya hau, ya tafi Jezreel.” Shin ya koyi wani abu kuwa? Ya ƙudura niyyar canja halinsa kuwa? Abubuwan da suka faru daga baya sun nuna cewa amsar a’a ce. Duk da haka, ranar ba ta ƙare ba tukuna ga Ahab, ko kuma ga Iliya.

17, 18. (a) Mene ne ya faru da Iliya sa’ad da yake hanya zuwa birnin Jezreel? (b) Me ya sa gudun da Iliya ya yi daga Karmel zuwa Jezreel ya zama abin mamaki? (Duba hasiya.)

17 Annabin Jehobah ya bi wannan hanyar da Ahab ya bi. Yana da sauran tafiya sosai, kuma ga hanyar ta yi caɓi. Amma wani abin mamaki ya faru.

18 “Hannun Ubangiji kuwa yana bisan Iliya; ya kuwa ɗamarce gidinsa, ya yi gudu a gaban Ahab har ƙofar Jezreel.” (1 Sar. 18:46) A bayyane yake cewa “hannun Ubangiji” ya yi aiki bisa Iliya a hanya ta musamman. Birnin Jezreel yana da nisan mil 19, kuma Iliya ba matashi ba ne. * Ka yi tunanin yadda wannan annabin ya tattara rigarsa, kuma ya ɗaura ta a kwankwasonsa domin ya samu damar yin tafiya a sake, sai kuma ya fara gudu a hanyar da ta cika da ruwa, yana gudu da sauri har ya tarar kuma ya wuce karusar sarkin!

19. (a) Ƙoshin lafiya da kuma ƙarfi da Allah ya ba Iliya sun sa mu tuna da waɗanne annabce-annabce? (b) Wane tabbaci ne Iliya yake da shi sa’ad da yake gudu zuwa Jezreel?

19 Hakika, wannan albarka ce ga Iliya! Ya yi farin ciki sosai don irin kuzarin da ya ji, wataƙila fiye ma da yadda ya ji sa’ad da yake matashi. Hakan zai tuna mana annabce-annabce da suka ba da tabbacin ƙoshin lafiya da ƙarfi ga masu aminci a aljanna a duniya. (Karanta Ishaya 35:6; Luk 23:43) Babu shakka, sa’ad da Iliya yake gudu a wannan jiƙakkiyar hanya, ya sani cewa Ubansa Jehobah, wanda shi ne kaɗai Allah na gaskiya ya amince da shi!

20. Mene ne za mu yi don Jehobah ya albarkace mu?

20 Jehobah yana a shirye ya albarkace mu. Albarkarsa tana da tamani, kuma ya kamata mu yi duk iya ƙoƙarinmu don mu ga cewa mun sami wannan albarkar. Kamar Iliya, muna bukatar mu kasance a faɗake, mu gwada alamun da suka nuna cewa Jehobah ya kusa ya ɗauki mataki a waɗannan miyagun lokatai. Kamar Iliya, muna da ƙwaƙƙwaran dalilai na kasancewa da tabbaci cewa Jehobah “Allah na gaskiya” zai cika alkawuransa.—Zab. 31:5.

^ sakin layi na 18 Ba da daɗewa ba bayan hakan, Jehobah zai umurci Iliya ya koyar da Elisha, mutumin da za a sani a matsayin “wanda dā ya kan zuba ruwa a hannuwan Iliya.” (2 Sar. 3:11) Elisha ya zama baran Iliya, babu shakka yana taimaka masa don ya tsufa.

Dan karamin girgije kawai da ya taru ya tabbatar wa Iliya cewa Jehobah ya kusa ya kawo ruwa. Alamun kwanaki na ƙarshe ma sun ba da ƙwaƙƙwarar dalilai na aikatawa da gaggawa