Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA UKU

“Uban Masu-Bada Gaskiya Duka”

“Uban Masu-Bada Gaskiya Duka”

1, 2. Ta yaya duniya ta lalace bayan zamanin Nuhu, kuma yaya Ibrahim ya ji?

IBRAHIM ya kalli sama sai ya hangi hasumiya da ke birnin Ur. * Birnin da aka haife shi ke nan. Mutane suna hayaniya kuma hayaƙi na tashiwa cikin birnin. Firistocin allan-wata ne suke miƙa hadayu. Ka kwatanta a zuci ka ga yadda Ibrahim ya juya baya yana kaɗa kansa kuma ya ɗaure fuska, yayin da yake ratsawa cikin jama’a da suka yi maƙil kan hanya sa’ad da za shi gida. Wataƙila yana tunanin bautar gumaka da ta zama ruwan dare a birnin Ur. Wannan bauta ta ƙarya ta yaɗu sosai a duniya tun daga zamanin Nuhu!

2 An haifi Ibrahim shekara biyu bayan mutuwar Nuhu. Bayan babban Rigyawa, Nuhu ya miƙa hadaya ga Jehobah Allah sa’ad da shi da iyalinsa suka fito daga jirgin, kuma Jehobah ya sa bakan gizo ya fito. (Far. 8:20; 9:12-14) Jehobah ne kaɗai ake bauta wa a wannan zamanin. Amma yanzu da shekaru da yawa suka shige kuma mutane sun ƙaru, yawancinsu ba sa bauta wa Jehobah. Mutane a ko’ina suna bauta wa allolin arna. Har Terah mahaifin Ibrahim ma yana bauta wa gumaka, kuma wataƙila yana ƙera su.—Josh. 24:2.

Me ya sa Ibrahim fitaccen misali ne na mai bangaskiya?

3. Wane hali ne ya yi fice a rayuwar Ibrahim, kuma mene ne hakan ya koya mana?

3 Halin Ibrahim ya yi dabam da na yawancin mutanen zamaninsa, domin yana da bangaskiya ga Allah. Shi ya sa daga baya aka hure manzo Bulus ya kira shi “uban masu-bada gaskiya duka.” (Karanta Romawa 4:11.) Bari mu ga abin da ya sa Ibrahim ya kasance da bangaskiya sosai. Ta hakan, mu ma za mu ga yadda za mu yi koyi da bangaskiyarsa.

Bauta wa Jehobah Bayan Rigyawa

4, 5. Mene ne wataƙila ya taimaki Ibrahim ya san Jehobah, kuma me ya sa?

4 Mene ne ya taimaki Ibrahim ya san Jehobah? Jehobah yana da bayi masu aminci a duniya a zamanin dā, alal misali, Shem. Ko da yake ba shi ne ɗan fari na Nuhu ba, amma sau da yawa shi ake fara ambatawa. Wataƙila domin Shem mutumi ne mai bangaskiya sosai. * Bayan Rigyawa, Nuhu ya kira Jehobah “Allah na Shem.” (Far. 9:26) Shem yana daraja Jehobah da kuma bauta ta gaskiya.

5 Shin Ibrahim ya san Shem kuwa? Wataƙila. Ka yi tunanin irin farin ciki da Ibrahim ya yi sa’ad da yake yaro, kuma ya san cewa yana da kaka da ya rayu fiye da shekaru 400. Shem ya ga muguntar da ke ko’ina a duniya kafin Rigyawa da sa’ad da aka halaka miyagu. Ya ga sa’ad da ’yan Adam suke ƙaruwa a duniya har aka sami al’ummai na farko da kuma lokacin da Nimrod ya yi tawaye a Hasumiyar da ke Babel. Shem bai saka hannu a tawayen ba, shi ya sa sa’ad da Jehobah ya rikitar da yaren masu gina hasumiyar, shi da iyalinsa sun ci gaba da yin yaren da Nuhu ya yi, wato yare na farko a duniya. Kuma Ibrahim da iyalinsa ma sun ci gaba da yin wannan yaren. Babu shakka, Ibrahim ya girma yana daraja Shem sosai, kuma ya kusan tsufa kafin Shem ya mutu. Mai yiwuwa, Shem ne ya koya masa game da Jehobah.

Ibrahim ya yi tir da bautar gumaka da ta zama ruwan dare a birnin Ur

6. (a) Ta yaya Ibrahim ya nuna cewa ya koyi darasi sosai daga labarin Rigyawa? (b) Wace irin rayuwa ce Ibrahim da Saratu suka yi?

6 Ko ta yaya dai, Ibrahim ya koyi darasi sosai daga labarin Rigyawa. Ya ƙoƙarta sosai ya bauta wa Allah yadda Nuhu ya yi. Shi ya sa ya ƙi bauta wa gumaka kuma ya fita dabam daga mutanen birnin Ur, wataƙila har da danginsa. Kuma ya yi sa’ar mata, domin Saratu kyakkyawar mace ce kuma mai bangaskiya sosai ga Jehobah. * Ko da yake ba su haifi yara ba, sun yi farin ciki sosai domin suna bauta wa Jehobah tare. Sun kuma yi renon Lutu, ɗan yayan Ibrahim.

7. Ta yaya ya kamata mabiyan Yesu su yi koyi da Ibrahim?

7 Ibrahim bai taɓa bauta wa allolin birnin Ur ba. Shi da matarsa sun kasance a shirye su yi fice daga mutanen yankinsu. Ya kamata mu kasance a shirye mu yi hakan idan muna son mu zama masu bangaskiya sosai. Yesu ya ce za a tsane mabiyansa domin su “ba na duniya ba ne.” (Karanta Yohanna 15:19.) Idan danginka ko mutanen yankinku sun tsane ka domin kana bauta wa Jehobah, ka tuna cewa ba kai kaɗai ba ne ke fuskantar irin wannan yanayin ba. Hakan ya nuna cewa kana yin koyi da misalin Ibrahim da Saratu da suka bauta wa Allah da aminci.

“Ka Fita Daga Cikin Ƙasarka”

8, 9. (a) Mene ne Ibrahim bai zai taɓa mantawa ba? (b) Mene ne Jehobah ya gaya wa Ibrahim?

8 Wata rana, Ibrahim ya ga abin da ba zai taɓa mantawa ba. Ya sami saƙo daga wurin Jehobah Allah! Littafi Mai Tsarki bai gaya mana dalla-dalla yadda ya sami saƙon ba, amma ya ce “Allah maɗaukaki” ya bayyana ga wannan mutumin mai aminci. (Karanta Ayyukan Manzanni 7:2, 3.) Wataƙila ta wurin mala’ika ne Ibrahim ya ɗan ga ɗaukakar Allah Maɗaukaki. Babu shakka, Ibrahim ya yi farin ciki sosai sa’ad da ya ga bambanci tsakanin Allah mai rai da gumaka marasa rai da tsararakinsa suke bauta wa.

9 Jehobah ya ce wa Ibrahim: “Ka fita daga ƙasarka, daga danginka kuma, da gidan ubanka, zuwa ƙasa da zan nuna maka.” Jehobah ya ce zai nuna wa Ibrahim ƙasar, amma bai ambata sunan ƙasar ba. Ibrahim zai bar ƙasarsu da danginsa. Dangantakar iyali tana da muhimmanci sosai a al’adun mutanen Gabas ta Tsakiya a zamanin dā. Wasu suna gani gwamma mutum ya mutu da ya bar danginsa.

10. Waɗanne sadaukarwa ne Ibrahim da Saratu suka yi sa’ad da suka bar gidansu a birnin Ur?

10 Babu shakka, Ibrahim ya yi sadaukarwa sosai da ya bar ƙasarsu. Hakika, Ur birni ne mai ni’ima sosai. (Duba akwatin nan  “Birnin da Ibrahim da Saratu Suka Baro.”) Abubuwan da aka tono daga ƙasa sun nuna cewa a dā, akwai gidaje masu kyau a birnin Ur, wasu suna da ɗakuna da yawa da aka gina kewaye da farfajiya don iyalai da bayinsu. A cikin birnin akwai isashen ruwan sha da na wanki da kuma na yin ba haya. Ka tuna cewa Ibrahim da Saratu ba matasa ba ne, wataƙila ya wuce shekara 70, matarsa kuma 60. Babu shakka, yana son matarsa ta ji daɗin rayuwa, abin da mijin kirki zai so ga matarsa ke nan. Ka yi tunanin yadda suka damu da kuma irin tambayoyin da suka yi wa juna game da abin da aka ce su yi. Babu shakka, Ibrahim ya yi farin ciki sosai sa’ad da matarsa Saratu ta amince ta yi hakan. Kamar mijinta, ta yarda ta yi wa dukan jin daɗin da ke ƙasarsu baya.

11, 12. (a) Waɗanne shirye-shirye da shawarwari ne Ibrahim da iyalinsa suka yi kafin su bar birnin Ur? (b) Ka kwatanta abin da ya faru a ranar da suka bar birnin Ur.

11 Ibrahim da Saratu suna da abubuwa da yawa da za su yi da yake sun tsai da shawara su bi umurnin Allah. Suna bukatar su kintsa kuma su tsara tafiyarsu. Waɗanne abubuwa ne za su ɗauka kuma waɗanne ne za su bari? Barin danginsu ne ya fi damunsu. Mahaifinsu Terah kuma fa? Shin ya yarda ya bi su? Littafi Mai Tsarki ya ce Terah ya ƙaura daga birnin Ur tare da iyalinsa. Hakan ya nuna cewa ƙila ya yarda da dukan zuciyarsa ya bi su, kuma sun kula da shi har sa’ad da ya rasu. Babu shakka, Terah ya daina bautar gumaka, kuma Lutu, ɗan yayan Ibrahim zai tafi tare da su.—Far. 11:31.

12 A ƙarshe, ranar tafiyar ta kai. Ka yi tunanin yadda suke kai kayayyakin da suka tattara hayen tafkin da ya kewaye birnin Ur. Ibrahim da iyalinsa sun shirya kome, sun ɗora wa raƙuma da jakai kaya, sun tattara dukan dabbobi da suke so su tafi da su, kuma kowa na jiran a soma tafiya. * Wataƙila kowa yana jiran Ibrahim ya ce a tafi. A ƙarshe, lokacin tafiyarsu ya yi, kuma suka tafi suka bar birnin Ur har abada.

13. Ta yaya bayin Jehobah da yawa a yau suka yi koyi da Ibrahim da Saratu?

13 A yau, bayin Jehobah da yawa sun ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shelar Mulki sosai. Wasu sun koyi sabon yare don su yi wa’azi sosai. Ko kuma sun gwada wata irin hidima da ba su taɓa yi ba. Yin hakan yana bukatar sadaukarwa sosai, wato kasancewa a shirye mu bar rayuwar jin daɗi. Abin yabawa ne sa’ad da bayin Allah suka yi koyi da Ibrahim da Saratu ta wajen sadaukar da kansu. Idan muka kasance da irin wannan bangaskiyar, muna da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace mu sosai. Ba zai taɓa manta da amincinmu ba. (Ibran. 6:10; 11:6) Shin ya albarkaci Ibrahim kuwa?

Sun Haye Kogin Yufiretis

14, 15. Mene ne tafiya daga Ur zuwa Haran ta ƙunsa, kuma me ya sa wataƙila Ibrahim ya sauka a birnin Haran na ɗan lokaci?

14 Ibrahim da jama’arsa suka ci gaba da tafiya. Sa’ad da Ibrahim da Saratu suka gaji da hawan raƙumi, sai suka taka da ƙafa, suna taɗi kuma ana jin ƙarar ƙararrawa da ke wuyan dabbobinsu. A hankali, sai kowa ya saba da tafiyar da yadda ake kafa da rushe tanti da kuma taimaka wa Terah ya hau raƙumi ko kuma jaki. Sun nufi arewa maso yamma kuma sun bi ta Kogin Yufiretis. Aka yi makonni da watanni suna tafiya.

15 Bayan tafiyar mil 600, sai suka kai bukkokin Haran, wanda babban birnin kasuwanci ne a Gabas maso Yamma. Sun sauka a wurin na ɗan lokaci, wataƙila don Terah ya tsufa ainun kuma ba zai iya ci gaba da tafiyar ba.

16, 17. (a) Wane alkawari ne ya sa Ibrahim farin ciki sosai? (b) Ta yaya Jehobah ya albarkaci Ibrahim sa’ad da yake birnin Haran?

16 Da shigewar lokaci, Terah ya mutu yana ɗan shekara 205. (Far. 11:32) Jehobah ya ta’azantar da Ibrahim sosai ta wajen sake yin magana da shi. Ya maimaita umurnin da ya ba shi a birnin Ur, kuma ya daɗa wasu abubuwa a cikin alkawarin da ya yi masa. Ibrahim zai zama “al’umma mai-girma,” kuma dukan iyalai da ke duniya za su samu albarka ta wurinsa. (Karanta Farawa 12:2, 3.) Wannan alkawarin da Allah ya yi masa, ya sa shi farin ciki sosai, kuma hakan ya ƙarfafa shi ya ci gaba da tafiya.

17 A wannan ƙaron, Ibrahim yana da kaya da yawa da zai kintsa, domin Jehobah ya albarkace shi sosai sa’ad da yake birnin Haran. Labarin ya ambata “dukan dukiyarsu da suka tattara, da masu-rai waɗanda suka samu cikin Haran.” (Far. 12:5) Da yake Ibrahim zai zama al’umma, zai bukaci dukiya mai yawa da bayi, wato iyali mai girma. Ba a koyaushe ba ne Jehobah yake sa bayinsa su zama masu arziki, amma yana ba su duk abin da suke bukata don su yi nufinsa. Da yake Jehobah ya ƙarfafa shi, sai ya ci gaba da tafiya zuwa ƙasar da bai sani ba.

Barin rayuwar jin daɗi a birnin Ur bai kasance wa Ibrahim da Saratu da sauƙi ba

18. (a) A wane lokaci ne Ibrahim ya kai rana mai muhimmanci a tarihin mutanen Allah? (b) Waɗanne abubuwa masu muhimmanci ne suka faru a ranar 14 ga Nisan? (Ka duba akwatin nan “Kwanan Wata Mai Muhimmanci.”)

18 Tafiya daga Haran zuwa birnin Karchemish zai ɗauki kwanaki da yawa, kuma matafiya da yawa suna bin wurin don su haye Kogin Yufiretis. Wataƙila a nan ne Ibrahim ya kai rana mai muhimmanci a tarihin mutanen Allah. Hakika, a ranar 14 ga Nisan a shekara ta 1943 kafin zamaninmu ne Ibrahim da mutanensa suka haye ƙogin. (Fit. 12:40-43) Ƙasar da Jehobah ya yi alkawari zai nuna wa Ibrahim tana kudancin ƙogin. A ranar ce Allah ya soma cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim.

19. Mene ne alkawarin da Jehobah ya yi wa Ibrahim ya ƙunsa, kuma mene ne wataƙila hakan ya tuna wa Ibrahim?

19 Ibrahim da iyalinsa suka tafi kudancin ƙasar, sai suka tsaya kusa da manyan itatuwa da ke garin Moreh, kusa da Shechem. Jehobah ya sake yi wa Ibrahim magana a wurin. A wannan lokacin, Allah ya ambata zuriyar Ibrahim da za ta gāji ƙasar. Shin Ibrahim ya tuna da annabcin da Jehobah ya yi a Adnin game da “zuriya” da za ta ceci ’yan Adam wata rana? Wataƙila. (Far. 3:15; 12:7) Mai yiwuwa, ya soma fahimta cewa yana cikin waɗanda Jehobah zai cika nufinsa ta wajensu.

20. Ta yaya Ibrahim ya daraja gatan da Jehobah ya ba shi?

20 Ibrahim ya daraja gatan da Jehobah ya ba shi sosai. Yayin da yake tafiya a ƙasar, ya mai da hankali sosai da yake har ila Kan’aniyawa suna ciki. Amma, Ibrahim ya tsaya kuma ya gina wa Jehobah bagadai, da farko kusa da manyan itatuwa da ke Moreh sai kuma kusa da Bethel. Ya kira bagadan da sunan Jehobah, kuma ya yabi Allah yayin da yake tunanin albarka da ’ya’yansa za su samu a nan gaba. Wataƙila ya yi wa maƙwabtansa Kan’aniyawa wa’azi. (Karanta Farawa 12:7, 8.) Hakika, Ibrahim zai fuskanci ƙalubale sosai a rayuwa. Abin farin ciki shi ne Ibrahim bai yi kewar abubuwan da ya bari a birnin Ur ba. Ya mai da hankali ga alkawuran da Jehobah ya yi masa. Littafin Ibraniyawa 11:10 ya ce Ibrahim yana jiran “birnin da ke da tussa, wanda mai-sifansa da mai-aikinsa Allah ne.”

21. Mene ne muka sani game da Mulkin Allah da Ibrahim bai sani ba, kuma mene ne hakan ya motsa ka ka yi?

21 Mu da ke bauta wa Jehobah a yau mun fi Ibrahim sanin wannan birnin, wato Mulkin Allah. Mun san cewa Mulkin ya soma sarauta a sama kuma jim kaɗan zai kawar da wannan mugun zamanin. Har ila, mun san cewa Yesu Kristi, Zuriyar Ibrahim da aka yi alkawarinsa ne Sarkin Mulkin. Hakika, gata ne sosai mu ga lokacin da Ibrahim zai sake rayuwa kuma zai sami cikakkiyar fahimi a kan yadda nufin Jehobah ya cika. Za ka so ka ga yadda Jehobah zai cika kowane alkawarinsa? Idan amsarka e ce, ka ci gaba da yin abin da Ibrahim ya yi. Ka kasance da halin son sadaukar da kai don yin nufin Jehobah. Ka ci gaba da yin biyayya kuma ka riƙa yin godiya don kowane gata da Jehobah ya ba ka. Yayin da kake yin koyi da imanin Ibrahim, wanda shi ne “Uban masu ba da gaskiya duka,” zai zama uba a gare ka.

^ sakin layi na 1 A wannan lokacin, sunan Ibrahim Abram ne. Amma daga baya, Allah ya canja sunan zuwa Ibrahim, wanda ke nufin “Uban jama’a.”—Far. 17:5.

^ sakin layi na 4 Hakazalika, ana yawan fara ambata Ibrahim a cikin ’ya’yan Terah, ko da yake ba shi ba ne ɗan fari.

^ sakin layi na 6 A wannan lokacin, sunan Saratu Saraya ne. Amma daga baya, Allah ya canja sunan zuwa Saratu, wanda ke nufin “Sarauniya.”—Far. 17:15.

^ sakin layi na 12 Wasu masana sun ce raƙumi ba dabbar gida ba ce a zamanin Ibrahim. Amma, ba su da ƙwararan dalilai na faɗin hakan. Sau da yawa, Littafi Mai Tsarki ya ambata cewa Ibrahim yana da raƙuma.—Far. 12:16; 24:35.