Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA SHIDA

Ta Yi Addu’a da Dukan Zuciyarta

Ta Yi Addu’a da Dukan Zuciyarta

1, 2. (a) Me ya sa Hannatu take baƙin ciki sa’ad da take shirin yin tafiya? (b) Mene ne za mu iya koya daga labarin Hannatu?

HANNATU ta shagala da shirye-shiryen yin tafiya don kada ta riƙa tunani game da matsalolinta. Ya kamata wannan ya zama lokacin farin ciki, don a kowace shekara mijinta Elkanah yakan kai dukan iyalin mazaunin da ke Shiloh don bauta wa Allah. Jehobah yana son mutane su yi farin ciki a wannan lokaci. (Karanta Kubawar Shari’a 16:15.) Babu shakka, Hannatu tana farin ciki sosai a waɗannan bukukuwa tun tana yarinya. Amma hakan ya canja.

2 Ta yi dacen miji domin yana ƙaunarta sosai, amma ya yi mata kishiya. Sunanta Peninnah ne kuma kamar tana son sa Hannatu baƙin ciki sosai musamman ma a lokacin da suke tafiya bauta a Shiloh. Ta yaya ta yi hakan? Ta yaya bangaskiyar Hannatu ta taimaka mata ta jimre da wannan yanayi mai wuya? Labarin Hannatu zai ƙarfafa ka idan kana fuskantar ƙalubale da ke sa ka baƙin ciki.

‘Don Me Zuciyarki ta Ɓace?’

3, 4. Waɗanne matsaloli biyu ne Hannatu ta fuskanta, kuma me ya sa suke da wuyan jimrewa?

3 Littafi Mai Tsarki ya ambata matsaloli biyu da Hannatu take fuskanta. Na farko yana da wuyan jimrewa kuma na biyun ya fi ƙarfinta sosai. Hannatu ba ta iya haihuwa ba, kuma kishiyarta ta tsane ta. Yana da wuya kowace mace da ke son ta haifi yara ta jimre da wannan yanayin, musamman ma a zamanin dā. Kowace iyali tana so ta samu yara da za su sa zuriyar ta ci gaba da wanzuwa. Rashin haihuwa abin kunya ne sosai a lokacin.

4 Da ba don kishiyar Hannatu ba, da ta jimre da yanayin da take ciki. An cika kishi da jayayya da baƙin ciki a iyalin da aka auri mata da yawa. Hakan ya saɓa wa mizanin aure da Allah ya kafa a lambun Adnin, kuma abin da ya faru a iyalin Elkanah misali ne mai kyau da ya nuna hakan. (Far. 2:24) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki bai goyi bayan mutum ya auri mata da yawa ba.

5. Me ya sa Peninnah take son ta sa Hannatu baƙin ciki, kuma ta yaya ta yi hakan?

5 Elkanah ya fi son Hannatu kuma tarihin Yahudawa ya nuna cewa ya aure ta kafin ya auri Peninnah bayan wasu shekaru. Peninnah wadda take kishin Hannatu sosai, tana sa ta baƙin ciki a hanyoyi da yawa. Da yake Hannatu ba ta haihu ba, Peninnah tana yin amfani da wannan zarafin don sa ta baƙin ciki sosai. Duk sa’ad da Peninnah ta haihu, sai ta ga kamar ta fi Hannatu daraja. Maimakon ta ji tausayin Hannatu kuma ta ƙarfafa ta, takan yi amfani da wannan yanayin don ta ƙara sa ta baƙin ciki. Littafi Mai Tsarki ya ce Peninnah takan tsokani Hannatu sosai “domin ta riƙa ba ta haushi.” (1 Sam. 1:6) Peninnah ta yi hakan da gangan domin tana son ta sa Hannatu baƙin ciki, kuma ta yi nasara.

Hannatu ta damu ƙwarai don ba ta haihu ba, kuma Peninnah ta yi iya ƙoƙari don ta sa ta baƙin ciki

6, 7. (a) Me ya sa wataƙila Hannatu ta ƙi gaya wa Elkanah abin da yake faruwa duk da cewa ya nemi ya ƙarfafa ta? (b) Shin rashin haihuwar Hannatu yana nufin cewa Jehobah yana fushi da ita ne? Ka bayyana. (Ka duba hasiya.)

6 Zarafin da Peninnah ta fi yin amfani da shi don sa Hannatu baƙin ciki, shi ne lokacin da suke zuwa bauta a Shiloh kowace shekara. Elkanah yakan ba kowanne cikin ’ya’yan Peninnah “maza da mata” hadayun da za su miƙa ga Jehobah. Amma, da yake Hannatu ba ta da yara, takan samu rabonta kaɗai. Peninnah takan yi amfani da wannan zarafin don ta tuna wa Hannatu cewa ba ta da yara, kuma hakan na sa ta kuka har ta ƙi cin abinci. Elkanah ya lura cewa matarsa wadda ya fi so tana baƙin ciki kuma ta ƙi cin abinci, sai ya nemi ya ƙarfafa ta. Ya ce mata: “Hannatu, don me ki ke kuka? Don me kuma ki ke ƙin ci? Don me zuciyarki ta ɓaci? Ni ban fi miki ’ya’ya maza goma ba?”—1 Sam. 1:4-8.

7 Elkanah ya fahimci cewa matarsa tana baƙin ciki don ba ta haihu ba. Babu shakka, Hannatu ta yi farin ciki sosai don yadda mijinta ya tabbatar mata cewa yana ƙaunarta. * Amma, Elkanah bai ambata abin da Peninnah take yi ba, kuma Littafi Mai Tsarki bai ce Hannatu ta gaya masa ba. Wataƙila ta ga cewa gaya wa mijinta abin da kishiyarta take mata zai daɗa sa yanayin muni. Idan ma ta gaya wa Elkanah, shin zai iya canja yanayin ne? Da a ce ta yi hakan, wataƙila da Peninnah da yaranta da kuma bayinta sun tsananta mata, kuma hakan zai daɗa sa ta zama kamar bare a gidan.

8. Sa’ad da aka maka rashin adalci, me ya sa yake da ban ƙarfafa ka tuna cewa Jehobah Allah ne mai adalci?

8 Ko da Elkanah ya san dukan abin da Peninnah take yi ko a’a, Jehobah dai ya sani. Kalmarsa ta bayyana cewa ya ga kome, kuma hakan gargaɗi ne ga duk wani da ke yin kishi da kuma ƙiyayya. Amma, marasa laifi da masu son zaman lafiya kamar Hannatu, za su samu ƙarfafa ta sanin cewa Allah zai magance dukan matsaloli a lokacin da ya dace kuma a hanyar da yake so. (Karanta Kubawar Shari’a 32:4.) Wataƙila Hannatu ma ta san da hakan, shi ya sa ta nemi taimakon Jehobah.

‘Ba Ta Ƙara Baƙin Ciki Ba’

9. Wane darasi ne muka koya daga yadda Hannatu ta kasance a shirye ta yi tafiya zuwa Shiloh ko da yake ta san abin da kishiyarta za ta yi?

9 Da sassafe, kowa a cikin iyalin ya shagala da aiki. Kowa yana shirin tafiya. Dukan iyalin za su yi tafiya fiye da mil 20 zuwa Shiloh da ke tudun ƙasar Ifraimu. * Za su yi tafiya na kwana ɗaya ko biyu da kafa. Hannatu ta san abin da kishiyarta za ta yi, amma ba ta zauna a gida ba. Ta hakan, ta kafa misali mai kyau ga bayin Allah a yau. Bai dace mu ƙyale halin wasu ya hana mu bauta wa Allah ba. Idan muka zauna a gida, ba za mu samu ƙarfafa da za ta taimaka mana mu jimre da yanayi mai wuya ba.

10, 11. (a) Me ya sa Hannatu ta nufi mazauni nan da nan? (b) Ta yaya Hannatu ta gaya wa Allah dukan matsalolinta?

10 Bayan iyalin sun yi tafiya mai nisan gaske, sai suka isa garin Shiloh. Manya-manyan tuddai suna kewaye da shi. Yayin da suka kusan shiga garin, mai yiwuwa Hannatu ta yi tunani sosai a kan abin da za ta faɗa a addu’arta ga Jehobah. Da suka isa wurin kuma suka ci abinci tare, sai Hannatu ta bar su nan da nan ta tafi mazaunin Jehobah. Eli Babban Firist yana zaune kusa da ƙofa, amma Hannatu ba ta gan shi ba domin ta mai da hankali ga addu’ar da take yi. Tana da tabbaci cewa idan ta yi addu’a a mazaunin, Allah zai saurare ta domin shi ne kaɗai zai fahimci irin yanayin da take ciki. Don yawan baƙin ciki da take yi, sai ta soma kuka.

11 Duk jikin Hannatu yana rawa yayin da take yin addu’a a cikin zuciyarta ga Jehobah. Leɓunanta suna motsi yayin da take furta baƙin ciki da take yi. Ta yi addu’a na dogon lokaci, kuma ta gaya wa Ubanta dukan abin da yake damunta. Bayan da Hannatu ta roƙi Allah ya sa ta haihu, sai ta yi wani abu kuma. Me ke nan? Ta yi alkawari cewa idan ta haifi ɗa, za ta keɓe shi ga Jehobah muddar ransa. Hakan ya nuna cewa ba albarka kaɗai ba ce Hannatu take bukata, amma tana son ta ba Jehobah abin da za ta iya bayarwa.—1 Sam. 1:9-11.

12. Kamar yadda misalin Hannatu ya nuna, mene ne ya kamata mu riƙa tunawa sa’ad da muke son mu yi addu’a?

12 Hannatu ta kafa wa dukan bayin Allah misali mai kyau a batun yin addu’a. Jehobah ya gaya wa mutanensa su yi addu’a a gare shi ba tare da jinkiri ba, su gaya masa dukan abin da yake damunsu kamar yadda ɗa yake dogara ga uba da ke ƙaunarsa. (Karanta Zabura 62:8; 1 Tasalonikawa 5:17.) An hure manzo Bitrus ya rubuta waɗannan kalmomi masu ban ƙarfafa game da addu’a ga Jehobah: “Kuna zuba dukan alhininku a bisansa, domin yana kula da ku.”—1 Bit. 5:7.

13, 14. (a) Wane zargi ne Eli ya yi wa Hannatu, kuma me ya sa? (b) Wane misali mai kyau na bangaskiya ne muka koya daga amsar da Hannatu ta ba Eli?

13 Amma, ’yan Adam ba sa jin tausayi da kuma fahimtar abubuwa kamar yadda Jehobah yake yi. Sa’ad da Hannatu take kuka da addu’a, ta yi mamaki sa’ad da ta ji muryar mutum. Muryar Eli ne, babban firist da yake lura da abin da take yi. Sai ya ce: “Har yaushe za ki yi maye? ki kawar da ruwan anab naki daga gareki.” Eli ya lura cewa leɓunanta suna motsi, kuma tana kuka da baƙin ciki. Maimakon ya tambaye ta abin da yake damunta, sai ya kammala cewa ta yi maye.—1 Sam. 1:12-14.

14 Abin da Eli ya ce wa Hannatu a wannan mawuyacin lokacin ya sa ta baƙin ciki sosai, musamman ma da yake shi Babban Firist ne. Duk da haka, ta kafa misali mai kyau na kasancewa da bangaskiya. Ba ta bar ajizancin ’yan Adam ya hana ta bauta wa Jehobah ba. Ta amsa wa Eli cikin ladabi kuma ta bayyana masa yanayin da take ciki. Sa’ad da ya fahimci cewa ya yi kuskure, wataƙila ya yi mata magana yanzu da hankali, ya ce: “Je ki dai da salama: Allah kuwa na Isra’ila shi ba ki roƙonki da kika roƙa a gareshi.”—1 Sam. 1:15-17.

15, 16. (a) Ta yaya yadda Hannatu ta gaya wa Jehobah dukan matsalolinta da kuma bauta masa a mazaunin suka taimaka mata? (b) Ta yaya za mu bi misalin Hannatu sa’ad da muke fama da baƙin ciki?

15 Ta yaya yadda Hannatu ta gaya wa Jehobah duk abin da ke damunta da kuma yadda ta bauta masa a mazaunin suka taimaka mata? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Macen fa ta kama hanyarta, ta kuwa ci, fuskarta ba ta ƙara nuna baƙinciki ba.” (1 Sam. 1:18) Hannatu ta wartsake sa’ad da ta furta matsalolinta ga Ubanta na sama mafi iko. (Karanta Zabura 55:22.) Shin akwai matsalolin da suka fi ƙarfinsa ne? Sam, babu!

16 Sa’ad da muka yi sanyin gwiwa, ya kamata mu bi misalin Hannatu kuma mu gaya wa “mai-jin addu’a” dukan matsalolinmu. (Zab. 65:2) Idan muka yi hakan da bangaskiya, za mu daina baƙin ciki kuma za mu kasance da ‘salama ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka.’—Filib. 4:6, 7.

“Babu Mai Ƙarfi Kamar Allahnmu”

17, 18. (a) Ta yaya Elkanah ya amince da alkawarin da matarsa ta yi? (b) Me ya sa Peninnah ta daina sa Hannatu baƙin ciki?

17 Washegari, sai Hannatu da mijinta suka koma mazaunin tare. Wataƙila ta gaya masa game da roƙo da kuma alkawarin da ta yi, gama a Dokar da aka ba da ta hannun Musa, miji yana da iko ya ƙi amince da alkawari da matarsa ta yi ba tare da izininsa ba. (Lit. Lis. 30:10-15) Amma wannan mutumi mai aminci bai yi hakan ba, maimako, shi da matarsa sun bauta wa Jehobah tare a mazaunin kafin su koma gida.

18 A wane lokaci ne Peninnah ta fahimci cewa ba za ta ƙara iya sa Hannatu baƙin ciki ba? Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba, amma furucin nan ‘fuskarta ba ta ƙara nuna baƙinciki ba’ ya nuna cewa tun daga lokacin, Hannatu tana farin ciki kuma ta daina damuwa. Ba da daɗewa ba, Peninnah ta ga cewa halinta ya daina shafan Hannatu. Littafi Mai Tsarki bai sake ambata sunanta ba.

19. Wace albarka ce Hannatu ta samu, kuma ta yaya ta nuna godiya ga Allah?

19 Da shigewar watanni, wani abu ya faru da ya daɗa sa Hannatu farin ciki. Ta yi juna biyu, kuma ba ta manta cewa Allah ne ya albarkace ta ba. Sa’ad da ta haifi yaron, sai ta ba shi suna Sama’ila wanda ke nufin “Sunan Allah.” Hakan ya nuna cewa ta nemi Jehobah ya taimaka mata. A wannan shekarar, Hannatu ba ta tafi Shiloh tare da iyalin ba. Ta yi shekara uku a gida tare da yaron, har ta yaye shi. Ta soma tunani da kuma shirin yadda za ta jimre sa’ad da ta rabu da ɗanta ƙaunatacce.

20. Ta yaya Hannatu da Elkanah suka cika alkawarin da suka yi wa Jehobah?

20 Hakika, Hannatu ta san cewa wataƙila wasu mata da ke hidima a mazaunin da ke Shiloh za su kula da Sama’ila sosai. Duk da haka, bai da sauƙi mahaifiya ta rabu da ɗanta tilo. Kuma Sama’ila ɗan shekara uku ne kawai. Amma, Hannatu da Elkanah ba su kawo yaron kamar an tilasta musu ba. Maimako, sun yi hakan da farin ciki. Sun miƙa hadayu a gidan Allah, sai suka ba da Sama’ila ga Eli, kuma suka tuna masa da alkawarin da Hannatu ta yi shekaru uku da suka shige.

Hannatu ta zama albarka sosai ga ɗanta Sama’ila

21. Ta yaya addu’ar Hannatu ta nuna cewa tana da bangaskiya sosai? (Ka kuma duba akwatin nan “ Addu’o’i Biyu Masu Ma’ana Sosai.”)

21 Sai Hannatu ta yi addu’a, kuma Allah ya ga cewa ya dace a rubuta ta cikin hurarriyar Kalmarsa. Yayin da ka karanta addu’arta da ke cikin littafin 1 Sama’ila 2:1-10, za ka ga cewa Hannatu tana da bangaskiya sosai. Ta yabi Jehobah don yadda ya yi amfani da ikonsa wajen ƙasƙantar da masu girman kai da saka wa waɗanda aka zalunta. Yana kuma da ikon ba da rai ko kuwa kawo ƙarshensa. Ta ɗaukaka Allah don yana da tsarki da adalci da kuma aminci. Shi ya sa Hannatu ta ce: “Babu wani fa kuma kamar Allahnmu.” Za mu iya dogara ga Jehobah don ba ya canjawa, kuma shi mafaka ne ga fakirai da kuma waɗanda ake zalunta.

22, 23. (a) Me ya sa muke da tabbaci cewa Sama’ila ya san cewa iyayensa suna ƙaunarsa? (b) Wace albarka ce Jehobah ya sake yi wa Hannatu?

22 Sama’ila ya yi dacen mahaifiya mai bangaskiya sosai ga Jehobah. Ko da yake ya yi kewar ta sa’ad da yake girma, bai ji kamar an yashe shi ba. A kowace shekara, Hannatu tana ziyarar sa a Shiloh kuma ta ɗinko masa riga don ya yi hidima da ita a mazaunin. Hakan tabbaci ne cewa tana ƙaunar ɗanta kuma tana kula da shi. (Karanta 1 Sama’ila 2:19.) Ka yi tunanin yadda take sa wa ɗanta sabuwar rigar, kuma take gyaggyara ta yayin da take kallonsa kuma take ƙarfafa shi. Sama’ila ya yi dacen uwa, kuma sa’ad da ya yi girma, ya zama albarka ga iyayensa da kuma dukan Isra’ilawa.

23 Jehobah bai mance da Hannatu ba, kuma ya albarkace ta da ƙarin yara biyar. (1 Sam. 2:21) Albarka da Hannatu ta fi samu ita ce dangantakar da ta ƙulla da Jehobah cikin shekaru da yawa. Ka ci gaba da ƙulla irin wannan dangantakar, yayin da kake yin koyi da bangaskiyar Hannatu.

^ sakin layi na 7 Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ya ‘kulle cikin Hannatu,’ babu abin da ya nuna cewa Allah yana fushi da wannan mace mai tawali’u da kuma aminci. (1 Sam. 1:5) A wasu lokatai, Littafi Mai Tsarki yakan ce Allah ne ya yi wani abu sa’ad da ya ƙyale abin ya faru na ɗan lokaci.

^ sakin layi na 9 Wataƙila an gwada nisan wurin daga garin su Elkanah, wato Ramah wanda ake kira Arimatiya a zamanin Yesu.

Hannatu ta nemi taimakon Jehobah sa’ad da take fuskantar zalunci a gida