Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RATAYE

Yesu Kristi—Almasihu da Aka Yi Alkawarinsa

Yesu Kristi—Almasihu da Aka Yi Alkawarinsa

DOMIN a taimake mu mu gane Almasihu, Jehobah Allah ya huri annabawan Littafi Mai Tsarki da yawa su ba da bayani game da haihuwa, hidima, da kuma mutuwar wannan Mai Ceto. Dukan waɗannan annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki sun cika a kan Yesu Kristi. Abin ban sha’awa, daidai suke a bayaninsu. Alal misali, bari mu bincika wasu annabce-annabce da suka faɗi abubuwa da suka shafi haihuwa da kuma yaranta na Almasihu.

Annabi Ishaya ya annabta cewa Almasihu zai fito daga zuriyar Sarki Dauda. (Ishaya 9:7) Kuma hakika an haifi Yesu daga zuriyar Dauda.—Matta 1:1, 6-17.

Miƙah wani annabin Allah, ya annabta cewa wannan ɗan zai zama sarki a ƙarshe kuma ya ce za a haife shi a “Bai’talahmi Ephrathah.” (Miƙah 5:2) Sa’ad da aka haifi Yesu, akwai garuruwa biyu a Isra’ila da ake kira Bai’talahmi. Ɗaya tana kusa da Nazarat a yankin arewaci na ƙasar, ɗayar kuma tana kusa da Urushalima ta Yahuda. Bai’talahmi da ke kusa da Urushalima a dā ana kiranta Ephrathah. An haifi Yesu a wannan garin, daidai yadda aka ce a annabcin!—Matta 2:1.

Wani annabci na Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa Allah zai kira ɗansa daga “Masar.” An ɗauki Yesu zuwa Masar. An mai da shi bayan mutuwar Herod, da haka ya cika annabcin.—Hosea 11:1; Matta 2:15.

A taswira da ke [“Annabce-Annabce Game da Almasihu”], nassosi da aka jere a ƙarƙashin “Annabci” suna ɗauke da bayani dalla-dalla game da Almasihun. Don Allah ka gwada da nassosi da aka jera a ƙarƙashin “Cika.” Yin haka zai sake ƙarfafa bangaskiyarka game da gaskiyar Kalmar Allah.

Sa’ad da kake bincika waɗannan nassosin, ka tuna cewa waɗannan annabci ne da aka rubuta su shekaru ɗarurruwa kafin a haifi Yesu. Yesu ya ce: “Dukan abin da aka rubuta a kaina a cikin Attaurat ta Musa, da Annabawa, da Zabura, dole a cika su.” (Luka 24:44) Kamar yadda za ka gani a cikin naka Littafi Mai Tsarki, hakika sun cika!

ANNABCE-ANNABCE GAME DA ALMASIHU
AUKUWA ANNABCI CIKA
Haifa a zuriyar Yahuda Farawa 49:10 Luka 3:23-33
Budurwa za ta haife shi Ishaya 7:14 Matta 1:18-25
Daga zuriyar Sarki Dauda Ishaya 9:7 Matta 1:1, 6-17
Jehobah ya furta cewa Ɗansa ne Zabura 2:7 Matta 3:17
Ba a gaskata shi ba Ishaya 53:1 Yohanna 12:37, 38
Ya shiga Urushalima a kan jaki Zechariah 9:9 Matta 21:1-9
Abokinsa na kusa ya ci amanarsa Zabura 41:9 Yohanna 13:18, 21-30
An ci amanarsa domin zinariya 30 Zechariah 11:12 Matta 26:14-16
Ya yi shiru a gaban masu zarginsa Ishaya 53:7 Matta 27:11-14
An jefa ƙuri’a domin tufafinsa Zabura 22:18 Matta 27:35
An zazzage shi a kan gungume Zabura 22:7, 8 Matta 27:39-43
Ba a fasa ƙasusuwansa ko ɗaya ba Zabura 34:20 Yohanna 19:33, 36
An binne shi da masu arziki Ishaya 53:9 Matta 27:57-60
An ta da shi kafin ya ruɓe Zabura 16:10 Ayukan Manzanni 2:24, 27
Yana tsaye dama ga Allah Zabura 110:1 Ayukan Manzanni 7:56

← Ka duba inda babin yake