Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA SHA BIYU

Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai

Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai

Ta yaya za ka zama abokin Allah?

A wace hanya ce ƙalubalan Shaiɗan ya shafe ka?

Waɗanne irin halaye ne suke ɓata wa Jehobah rai?

Ta yaya za ka rayu a hanyar da take faranta wa Allah rai?

WANE irin mutum za ka zaɓa ya zama abokinka? Wataƙila za ka zaɓi mutumin da yake da irin ra’ayinka, yana son irin abin da kake so, wanda yake da irin halinka. Kuma za ka kusaci mutumin da yake da halayen kirki irinsu aminci da alheri.

2 A tarihi, Allah ya zaɓi wasu mutane su zama abokansa. Alal misali, Jehobah ya kira Ibrahim abokinsa. (Ishaya 41:8; Yaƙub 2:23) Allah ya kira Dauda “mutum gwalgwadon zuciyata” domin mutum ne da Jehobah yake ƙauna. (Ayukan Manzanni 13:22) Kuma Jehobah ya ce game da annabi Daniel “kai ƙaunatace ne ƙwarai.”—Daniel 9:23.

3 Me ya sa Jehobah ya zaɓi Ibrahim, Dauda, da kuma Daniyel su zama abokanansa? Ya gaya wa Ibrahim: “Ka yi biyayya da maganata.” (Farawa 22:18) Saboda haka Jehobah yana kusantar waɗanda suka yi abin da ya gaya musu cikin tawali’u. Ya gaya wa Isra’ilawa: “Ku kasa kunne ga muryata; ni kuma in zama Allahnku.” (Irmiya 7:23) Idan ka yi wa Jehobah biyayya kai ma za ka zama abokinsa!

JEHOBAH YANA ƘARFAFA ABOKANANSA

4 Ka yi tunani game da abin da abota da Allah take nufi. Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah yana neman zarafi don ya nuna “bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.” (2 Labarbaru 16:9) Ta yaya Jehobah zai nuna ikonsa a gare ka? An fito da hanya ɗaya a Zabura 32:8, a nan mun karanta: “[Ni Jehobah] ni koya maka cikin tafarkin da za ka bi: da idona a kanka zan ba ka shawara.”

5 Hakika furci ne na ƙauna daga Jehobah! Zai yi maka ja-gora da kake bukata kuma ya kula da kai sa’ad da kake amfani da su. Allah yana so ya taimake ka ka jimre gwaji kuma ka yi nasara. (Zabura 55:22) Saboda haka idan ka bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya, za ka kasance da tabbaci kamar mai Zabura wanda ya ce: “Na sa Ubangiji a gabana tuttur: Da shi ke yana ga hannun damana ba zan jijjigu ba.” (Zabura 16:8; 63:8) Hakika, Jehobah zai taimake ka ka rayu a hanyar da za ta faranta masa rai. Amma, kamar yadda ka sani, Allah yana da abokin gaba da ba zai so ka yi haka ba.

ƘALUBALAN DA SHAIƊAN YA YI

6Babi na 11 na wannan littafin ya yi bayani game da yadda Shaiɗan Iblis ya ƙalubalanci ikon mallaka na Allah. Shaiɗan ya zargi Allah da yin ƙarya kuma ya nuna cewa Jehobah bai yi adalci ba da bai ƙyale Adamu da Hauwa’u su zaɓi wa kansu abin da ke nagarta da abin da ke mugunta ba. Bayan da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi kuma duniya ta fara cika da ’ya’yansu, Shaiɗan ya ƙalubalanci dukan ’yan adam. “Mutane ba sa bauta wa Allah domin suna ƙaunarsa,” in ji Shaiɗan. “Ka ba ni zarafi ka gani, zan sa kowa ya juya maka baya.” Tarihin mutumin da aka kira Ayuba ya nuna cewa abin da Shaiɗan ya gaskata ke nan. Wanene Ayuba, kuma ta yaya ƙalubalan da Shaiɗan ya yi ya shafe shi?

7 Ayuba ya rayu shekaru 3,600 da suka shige. Mutumin kirki ne, domin Jehobah ya ce: “Babu mai-kama da shi cikin duniya, kamili ne, mutum mai-adalci, mai tsoron Allah, yana ƙin mugunta.” (Ayuba 1:8) Ayuba ya faranta wa Allah rai.

8 Shaiɗan ya zargi dalilin da ya sa Ayuba yake bauta wa Allah. Iblis ya gaya wa Jehobah: “Ba ka kewaye shi da shinge ba, da shi da gidansa, da dukan abin da ya ke da shi, a kowane sassa? Ka albarkaci aikin hannuwansa, dabbobinsa sun ƙaru a ƙasa. Miƙa hannunka kaɗai yanzu, ka taɓa dukan abin da ya ke da shi, za ya la’anta ka a fuskarka!”—Ayuba 1:10, 11.

9 Saboda haka Shaiɗan ya ce Ayuba yana bauta wa Allah ne saboda abin da yake samu. Iblis ya ce idan aka gwada Ayuba zai juya wa Allah baya. Yaya Jehobah ya amsa ƙalubalan da Shaiɗan ya yi? Tun da batun ya shafi dalilin bautar Ayuba, Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya gwada Ayuba. Ta wannan hanyar, za a tabbatar da ko Ayuba yana ƙaunar Allah ko ba ya ƙaunarsa.

AN GWADA AYUBA

10 Ba da daɗewa ba Shaiɗan ya gwada Ayuba ta hanyoyi da yawa. Na farko, aka sace wasu daga cikin dabbobin Ayuba, aka kuma kashe wasu. Kuma an kashe yawancin bayinsa. Wannan ya karya masa arziki. Masifa ta sake faɗa wa Ayuba sa’ad da guguwa ta kashe ’ya’yansa goma. Duk da waɗannan masifu da suka faru, “Ayuba ba ya yi zunubi ba, ba ya kuwa saɓi Allah ba.”—Ayuba 1:22.

An ba wa Ayuba lada domin tafarkinsa na aminci

Ayuba ya samu lada saboda tafarkinsa na aminci

11 Shaiɗan bai gaji ba. Wataƙila ya yi tunanin cewa ko da yake Ayuba ya jimre wa hasarar dukiyarsa, rashin bayinsa da ’ya’yansa, zai juya wa Allah baya idan ya yi ciwo. Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya harbi Ayuba da muguwar cuta mai matsananciyar zafi. Wannan ba zai sa Ayuba ya yi rashin bangaskiya ga Allah ba. Maimakon haka, ya ce da tabbaci: “Har in mutu ba ni rabuwa da gaskiyata.”—Ayuba 27:5.

12 Ayuba bai san cewa Shaiɗan ne dalilin masifarsa ba. Da yake ba shi da cikakken bayani game da ƙalubalan da Iblis ya yi game da ikon mallaka na Jehobah, Ayuba yana zaton ko Allah ne ya sa masa masifa. (Ayuba 6:4; 16:11-14) Duk da haka, ya kasance da amincinsa ga Jehobah. Kuma ta wajen amincin Ayuba aka tabbatar da da’awar da Shaiɗan ya yi wai Ayuba yana bauta wa Allah ne saboda son kai, ƙarya ce!

13 Amincin Ayuba ya ba wa Jehobah dalilin ba da kyakkyawar amsa ga ƙalubalantar ikon mallaka na Jehobah da Shaiɗan ya yi. Babu shakka, Ayuba abokin Jehobah ne na gaskiya, kuma Allah ya ba shi lada domin tafarkinsa na aminci.—Ayuba 42:12-17.

YADDA YA SHAFE KA

14 Wannan al’amari game da aminci ga Allah da Shaiɗan ya yi zargi ba ga Ayuba ba ne kawai. Ya shafe ka. Wannan ya bayana a fili a Misalai 27:11, inda Kalmar Jehobah ta ce: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.” Waɗannan kalmomi da aka rubuta shekaru da yawa bayan mutuwar Ayuba, sun nuna cewa Shaiɗan har yanzu yana sūkan Allah kuma yana zargin bayinsa. Idan muka yi rayuwa da take faranta wa Jehobah rai, muna taimakawa ne wajen amsa zargin Shaiɗan, kuma a wannan hanyar muna faranta wa Allah rai. Yaya ka ji game da wannan? Ba zai kasance da ban sha’awa ba idan ka saka hannu wajen amsa da’awar Iblis, idan ma ya zamanto kana bukatar ka yi wasu canji a rayuwarka?

15 Ka lura cewa Shaiɗan ya ce: ‘Dukan abin da mutum ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa.’ (Ayuba 2:4) Da ya ce “mutum” Shaiɗan ya bayyana a fili cewa zarginsa ba ga Ayuba ba ne kawai amma ga dukan mutane ne. Wannan al’amari ne mai muhimmanci. Shaiɗan ya zargi amincinka ga Allah. Iblis zai so ya ga ka yi wa Allah rashin biyayya kuma ka yi watsi da tafarkin adalci sa’ad da wahala ta samu. Ta yaya Shaiɗan zai so ya yi haka?

16 Kamar yadda aka tattauna a Babi na 10, Shaiɗan yana amfani da hanyoyi dabam dabam ya sa mutane su juya wa Allah baya. A wata hanyar yana faɗā wa ne “kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” (1 Bitrus 5:8) Ta haka, kana iya ganin rinjayar Shaiɗan sa’ad da abokane, ’yan’uwa, ko kuma wasu suka yi hamayya da ƙoƙarinka ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ka yi abin da ka koya.* (Yohanna 15:19, 20) A wani gefen kuma, Shaiɗan “ya kan mayarda kansa kamar mala’ika na haske.” (2 Korinthiyawa 11:14) Iblis yana iya yin amfani da dabara ya yaudare ka daga tafarkin rayuwa mai faranta wa Allah rai. Zai iya kuma yin amfani da karaya, wataƙila ya sa ka ji kai ba ka cancanta ka faranta wa Allah rai ba. (Misalai 24:10) Ko Shaiɗan ya kasance kamar “zaki mai-ruri” ko “kamar shi mala’ika na haske” ne, ƙalubalensa ya kasance ɗaya ne: Ya ce sa’ad da ka fuskanci gwaji, ko jarabta, za ka bar bauta wa Allah. Ta yaya za ka amsa wannan ƙalubale kuma ka tabbatar da amincinka ga Allah, kamar yadda Ayuba ya yi?

YIN BIYAYYA GA UMURNIN JEHOBAH

17 Za ka iya amsa ƙalubalen Shaiɗan ta wajen rayuwa da take faranta wa Allah rai. Menene wannan ya ƙunsa? Littafi Mai Tsarki ya amsa: “Kuma za ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka.” (Kubawar Shari’a 6:5) Sa’ad da ƙaunarka ga Allah ta ƙaru, za ka cika da muradin ka yi abin da ya bukace ka da yi. “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa,” in ji manzo Yohanna. Idan ka yi ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarka, za ka ga cewa “dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.”—1 Yohanna 5:3.

18 Menene umurnin Jehobah? Wasu sun haɗa da halaye da dole ne mu guje wa. Alal misali, ka lura da akwatin nan, mai jigo “Ka Guje wa Abin da Jehobah ya Ƙi.” A nan za ka ga jerin halaye da Littafi Mai Tsarki ya haramta. A ganin farko, wasu halaye da aka jera ba za su kasance da wani laifi ba. Amma idan ka yi bimbini a kan nassosi da aka rubuta, wataƙila ka ga hikimar dokar Jehobah. Yin canji a halinka zai kasance ƙalubale mafi girma da ka taɓa fuskanta. Duk da haka, rayuwa a hanyar da take faranta wa Allah rai tana kawo gamsuwa da kuma farin ciki. (Ishaya 48:17, 18) Kuma abin da za ka iya yi ne. Ta yaya muka san haka?

KA GUJE WA ABIN DA JEHOBAH YA ƘI

’Yan daba guda biyu
Ma’aurata suna shan giya da taba
Matar da ke sata
 • Kisan Kai.—Fitowa 20:13; 21:22, 23.
 • Lalata.—Leviticus 20:10, 13, 15, 16; Romawa 1:24, 26, 27, 32; 1 Korinthiyawa 6:9, 10.
 • Sihiri.—Kubawar Shari’a 18:9-13; 1 Korinthiyawa 10:21, 22; Galatiyawa 5:20.
 • Bautar Gumaka.—1 Korinthiyawa 10:14.
 • Maye.—1 Korinthiyawa 5:11.
 • Sata.—Leviticus 6:2, 4; Afisawa 4:28.
 • Ƙarya.—Misalai 6:16, 19; Kolossiyawa 3:9; Ru’ya ta Yohanna 22:15.
 • Kwaɗayi.—1 Korinthiyawa 5:11.
 • Nuna Ƙarfi.—Zabura 11:5; Misalai 22:24, 25; Malachi 2:16; Galatiyawa 5:20
 • Ɗanyen Magana.—Leviticus 19:16; Afisawa 5:4; Kolossiyawa 3:8.
 • Amfani da Jini.—Farawa 9:4; Ayukan Manzanni 15:20, 28, 29.
 • Ƙin Yi wa Iyali Tanadi.—1 Timothawus 5:8.
 • Saka hannu cikin yaƙe-yaƙe da hargitsin siyasa na wannan duniyar.—Ishaya 2:4; Yohanna 6:15; 17:16.
 • Shan taba ko kuma ƙwayoyi.—Markus 15:23; 2 Korinthiyawa 7:1.

19 Jehobah ba ya bukatar abin da ba za mu iya yi ba a gare mu. (Kubawar Shari’a 30:11-14) Ya san abin da za mu iya da abin da ba za mu iya ba fiye da yadda muka sani. (Zabura 103:14) Bugu da ƙari, Jehobah zai iya ba mu ƙarfin da za mu yi masa biyayya. Manzo Bulus ya rubuta: “Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi muku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi muku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.” (1 Korinthiyawa 10:13) Domin ya taimake ka ka jimre, Jehobah zai iya ba ka “mafificin girman iko.” (2 Korantiyawa 4:7) Bayan da ya jimre wa gwaji da yawa, Bulus ya ce: “Na iya yin abu duka a cikin wannan da ya ke ƙarfafata.”—Filibbiyawa 4:13.

KOYON HALAYE DA ALLAH YAKE SO

20 Hakika, faranta wa Jehobah rai ya ƙunshi fiye da faranta masa rai kawai ta wajen guje wa abubuwa da ya ƙi. Kana bukatar kuma ka ƙaunaci abin da yake ƙauna. (Romawa 12:9) Kana kusantar waɗanda suke da irin ra’ayinka, abin da kake so da kuma halayenka? Haka Jehobah ma yake. Saboda haka ka koyi ka yi ƙaunar abin da Jehobah yake ƙauna. An kwatanta wasu cikin waɗannan a Zabura 15:1-5, a nan mun karanta game da waɗanda Allah ya ɗauke su abokanansa. Abokanan Jehobah suna nuna abin da Littafi Mai Tsarki ya kira “ɗiyan ruhu.” Waɗanda suka haɗa da “ƙauna, farinciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa.”—Galatiyawa 5:22, 23.

21 Karatu da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki a kullum zai taimake ka ka koyi halaye da Allah yake so. Koyon abin da Allah yake bukata zai taimake ka ka sa tunaninka ya jitu da na Allah. (Ishaya 30:20, 21) Da zarar ka ƙarfafa ƙaunarka ga Jehobah, haka nan muradinka zai kasance na son ka faranta wa Allah rai.

22 Ana bukatar ƙoƙari domin a rayu a hanyar da take faranta wa Jehobah rai. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta canza rayuwarka da yin watsi da hali na dā da ɗaukan sabon hali. (Kolossiyawa 3:9, 10) Amma game da umurnin Jehobah, mai zabura ya rubuta: “Cikin kiyaye su da lada mai-girma.” (Zabura 19:11) Kai ma za ka sami ladan rayuwa a hanyar da take faranta wa Allah rai. Ta wajen yin haka, za ka ba da amsa ga ƙalubalan da Shaiɗan ya yi kuma ka faranta wa Jehobah rai!

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

 • Za ka zama abokin Allah ta wajen yi masa biyayya.—Yaƙub 2:23.
 • Shaiɗan ya ƙalubalanci amincin dukan mutane.—Ayuba 1:8, 10, 11; 2:4; Misalai 27:11.
 • Dole ne mu guje wa abubuwa da Allah ba ya so.—1 Korinthiyawa 6:9, 10.
 • Za mu faranta wa Jehobah rai ta wajen ƙin abin da ya ƙi da kuma ƙaunar abin da yake ƙauna.—Romawa 12:9.

*  Wannan ba ya nufin cewa waɗanda suka yi hamayya da kai Shaiɗan ne yake rinjayarsu kai tsaye ba. Amma Shaiɗan shi ne allahn wannan zamanin, kuma dukan duniya tana cikin ikonsa. (2 Korinthiyawa 4:4; 1 Yohanna 5:19) Saboda haka, rayuwa irin ta ibada ba za ta kasance abin da mutane suke so ba, kuma saboda haka wasu za su yi hamayya da kai.


Tambayoyin Nazari

1, 2. Ka ba da misalin mutane da Jehobah ya zaɓa su zama abokanansa.

3. Me ya sa Jehobah ya zaɓi wasu mutane su zama abokanansa?

4, 5. Ta yaya Jehobah yake nuna ikonsa ga mutanensa?

6. Wane zargi Shaiɗan ya yi wa ’yan adam?

7, 8. (a) Me ya sa Ayuba ya yi fice a tsakanin mutane na zamaninsa? (b) Ta yaya Shaiɗan ya zargi dalilin da ya sa Ayuba yake bauta?

9. Yaya Jehobah ya amsa ƙalubalan Shaiɗan, kuma me ya sa?

10. Waɗanne gwaji ne suka faɗo wa Ayuba, kuma me ya yi?

11. (a) Wane zargi na biyu Shaiɗan ya yi game da Ayuba, kuma ta yaya Jehobah ya amsa? (b) Yaya Ayuba ya yi da cutarsa mai matsananciyar zafi?

12. Ta yaya Ayuba ya mai da martani ga ƙalubalan Iblis?

13. Menene ya faru domin Ayuba ya kasance da aminci ga Allah?

14, 15. Me ya sa za mu ce ƙalubalan Shaiɗan ya shafi dukan mutane?

16. (a) Ta waɗanne hanyoyi ne Shaiɗan yake so ya juya mutane daga Allah? (b) Ta yaya Iblis zai yi amfani da waɗannan salo a gareka?

17. Menene ainihin dalilin yin biyayya da dokokin Jehobah?

18, 19. (a) Faɗi wasu cikin umurnin Jehobah. (Dubi akwati.) (b) Ta yaya muka sani cewa Allah ba ya bukatar abin da ya fi ƙarfinmu?

20. Waɗanne halaye ne da Allah yake so ya kamata ka koya, kuma me ya sa wannan yake da muhimmanci?

21. Menene zai taimake ka ka koyi halaye da Allah yake so?

22. Menene za ka cim ma idan ka rayu a hanyar da take faranta wa Allah rai?