Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RATAYE

Mecece Ranar Shari’a?

Mecece Ranar Shari’a?

YAYA kake tsammanin ranar shari’a take? Wasu suna tsammanin cewa da ɗaiɗai da ɗaiɗai mutane biliyoyi za su zo gaban kursiyin Allah. Saboda haka, sai a zartar da hukunci bisa kowa. Wasu za a ba su ladar salama a sama, wasu kuma a jefa su cikin wuta a azabtar da su har abada. Amma, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta wannan lokaci a wata hanya dabam. Kalmar Allah ta kwatanta lokacin, ba lokaci ba ne na tsoro da razana, amma lokaci ne na bege da yin gyara.

A Ru’ya ta Yohanna 20:11, 12, mun karanta yadda manzo Yohanna ya kwatanta wannan Ranar Shari’a: “Na ga kuma babban farin kursiyi, da wanda ke zaune a bisansa, wanda duniya da sama suka guje ma fuskatasa; ba a kuwa samu musu wuri ba. Na ga matattu kuma, ƙanana da manya, suna tsaye a gaban kursiyin; aka buɗe littattafai: aka buɗe wani littafi kuma, littafin rai ke nan: aka yi ma matattu shari’a kuma bisa ga abin da aka rubuta cikin littattafai, gwargwadon ayyukansu.” Wanene Alƙali da aka kwatanta a nan?

Jehobah Allah shi ne babban Alƙali na ’yan adam. Amma, ya ba da aikin zartar da shari’a. In ji Ayukan Manzanni 17:31, manzo Bulus ya ce Allah, “ya sanya rana, inda za ya yi ma duniya duka shari’a mai-adalci ta wurin mutum wanda ya ƙadara.” Wannan Alƙalin Yesu Kristi ne da aka ta da daga matattu. (Yohanna 5:22) Amma, a yaushe ne Ranar Shari’a za ta fara? Yaya tsawonta?

Littafin Ru’ya ta Yohanna ya nuna cewa Ranar Shari’a za ta fara bayan yaƙin Armagedon, sa’ad da aka riga aka halaka dukan tsarin Shaiɗan daga duniya.* (Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16; 19:19-20:3) Bayan Armagedon, za a ɗaure Shaiɗan da aljannunsa a cikin rami marar-matuƙa na shekara dubu. A wannan lokaci ne, mutane 144,000 abokan gado na sama za su yi “mulki kuma tare da Kristi shekara dubu.” (Ru’ya ta Yohanna 14:1-3; 20:1-4; Romawa 8:17) Ranar Shari’a ba abu ba ne cikin hanzari da za a yi cikin awoyi 24. Zai ɗauki shekara dubu.

A cikin waɗannan shekaru dubu, Yesu zai yi shari’a ga “masu-rai da matattu.” (2 Timothawus 4:1) “Masu-rai” su ne “taro mai-girma” da suka tsira daga Armagedon. (Ru’ya ta Yohanna 7:9-17) Manzo Yohanna ya ga “matattu…suna tsaitsaye a gaban kursiyin” shari’a. Kamar yadda Yesu ya yi alkawari, “waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji murya [Kristi], su fito kuma” ta wajen tashin matattu. (Yohanna 5:28, 29; Ayukan Manzanni 24:15) A kan me za a yi musu shari’a?

In ji wahayin manzo Yohanna, “aka kuma buɗe littattafai,” kuma “aka kuwa yi wa matattu shari’a bisa ga abin da ke rubuce cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi.” Waɗannan littattafan sun ƙunshi abubuwa da mutane suka yi ne a dā? A’a, shari’ar ba bisa abin da mutane suka yi ba ne kafin su mutu. Ta yaya muka san haka? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda ya mutu ya kuɓuta daga zunubi.” (Romawa 6:7) Waɗanda aka tashe su daga matattu wato za su fito ne babu zunubi. Saboda haka, waɗannan littattafai suna wakiltan ƙarin umurni ne na Allah. Domin su rayu har abada waɗanda suka tsira daga Armageddon da waɗanda aka tashe su daga matattu dole ne su bi umurnin Allah, haɗe da dukan wani umurni da za a bayyana a cikin shekara dubun. Saboda haka, mutane za a yi musu hukunci ne bisa abin da suka yi ciki Ranar Shari’a.

Ranar Shari’a za ta ba miliyoyin mutane zarafinsu na farko su koyi game da nufin Allah kuma su bi shi. Wannan yana nufin cewa za a yi aikin koyarwa mai yawa. Hakika, ‘mazaunan duniya za su koyi adalci.’ (Ishaya 26:9) Amma, ba duka ba ne za su so su yi nufin Allah. Ishaya 26:10 ta ce: “Ko an nuna ma mugu alheri, ba za ya koyi adilci ba: a cikin ƙasa mai-gaskiya za ya aika mugunta, ba kuwa za shi ga ɗaukakar Ubangiji ba.” Za a halaka miyagu har abada a Ranar Shari’a.—Ishaya 65:20.

A ƙarshen Ranar Shari’a, mutane da suka tsira za su “rayu” su zama mutane kamilai. (Ru’ya ta Yohanna 20:5) Saboda haka, a Ranar Shari’a za a mai da mutane kamar yadda suke tun farko. (1 Korinthiyawa 15:24-28) Daga nan, sai gwaji na ƙarshe ya biyo baya. Za a saki Shaiɗan daga kurkuku kuma a ƙyale shi ya yi ruɗi na ƙarshe ga mutane. (Ru’ya ta Yohanna 20:3, 7-10) Waɗanda suka guje shi za su more cikar alkawarin Littafi Mai Tsarki: “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.” (Zabura 37:29) Hakika, Ranar Shari’a za ta kasance albarka ga dukan ’yan adam masu aminci!


*  Game da Armagedon, don Allah, ka dubi Insight on the Scriptures, Littafi na 1, shafuffuka 594-595, 1037-1038, sai kuma babi na 20 na littafin nan Bauta wa Allah Makaɗaici na Gaskiya, duka biyu Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

← Ka duba inda babin yake