Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA BIYU

Littafi Mai Tsarki—Littafi Ne Daga Allah

Littafi Mai Tsarki—Littafi Ne Daga Allah

A waɗanne hanyoyi ne Littafi Mai Tsarki ya bambanta da dukan wani littafi?

Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimake ka ka magance matsalolinka?

Me ya sa za ka yarda da annabce-annabcen da suke rubuce cikin Littafi Mai Tsarki?

KA TUNA lokacin da abokinka abin ƙauna ya yi maka kyauta? Wataƙila, wannan ta faranta maka rai matuƙa kuma ta sa ka yi godiya. Hakika, kyautar ta nuna maka wani abu game da mai bayarwa, mai bayarwan yana ko tana mutunta abota da ke tsakaninku. Babu shakka, ka yi godiya domin zurfin tunanin abokinka.

2 Littafi Mai Tsarki kyauta ne daga Allah, wanda ya kai mu yi godiya gaya. Wannan littafin ya bayyana abubuwan da ba za mu taɓa sani ba idan ba domin sa ba. Alal misali, ya gaya mana game da halittar taurarin samaniya, game da duniya, game da mata da miji na fari. Littafi Mai tsarki ya ƙunshi mizanai da za su taimake mu mu jimre wa matsaloli da damuwa na rayuwa. Ya yi bayani game da yadda Allah zai cika nufinsa kuma ya kawo yanayi mai ni’ima a duniya. Hakika Littafi Mai Tsarki kyauta ne mai ba da farin ciki!

3 Littafi Mai Tsarki kyauta ne mai ban sha’awa, domin ya bayyana wani abu game da mai bayarwa, Jehobah Allah. Da yake ya ba da irin wannan littafin, hakan ya tabbatar da cewa yana so mu san shi da kyau. Hakika, Littafi Mai Tsarki zai taimake mu mu kusaci Jehobah.

4 Idan kana da Littafi Mai Tsarki, da mutane da yawa kamar ka. An fassara Littafi Mai Tsarki cikakkensa ko rabinsa cikin fiye da harsuna 2,300, saboda haka yana samuwa ga fiye da kashi 90 na mutanen duniya. A matsakaicinsa ana raba Littafi Mai Tsarki fiye da miliyan kowane mako! An buga biliyoyi a cikakkensa ko kuma rabinsa. Hakika, babu wani littafi kamar Littafi Mai Tsarki.

The “New World Translation of the Holy Scriptures” ana samun sa a cikin harsuna da yawa

The New World Translation a harsuna da yawa

5 Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki “hurarre daga wurin Allah” ne. (2 Timothawus 3:16) A wace hanya? Littafi Mai Tsarki kansa ya amsa: “Mutane suka yi magana daga wurin Allah, Ruhu Mai-tsarki ne yana motsa su.” (2 Bitrus 1:21) Alal misali: Ɗan kasuwa yana iya sa sakatarensa ya rubuta wasiƙa. Wannan wasiƙar za ta ƙunshi lafazi da umurnin ɗan kasuwan. Saboda haka, wasiƙar hakika ta ɗan kasuwan ne, ba ta sakatarensa ba. Hakazalika, Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi saƙon Allah ne, ba na mutanen da suka rubuta shi ba. Saboda haka, Littafi Mai Tsarki gaba ɗayansa “maganar Allah” ne.—1 Tassalunikawa 2:13.

CIKAKKE NE KUMA MAI JITUWA

6 Rubuta Littafi Mai Tsarki ya ɗauki fiye da shekara 1,600. Marubutansa sun rayu a zamani dabam dabam kuma sun fito ne daga yanayin rayuwa dabam dabam. Wasunsu manoma ne, wasu masūnta, wasu kuma makiyaya ne. Wasu annabawa ne, wasu mahukunta, wasu sarakuna. Marubucin Linjila Luka likita ne. Duk da bambance bambancen marubutansa, Littafi Mai Tsarki ya jitu daga fari har ƙarshe.*

7 Littafi na farko na Littafi Mai Tsarki ya faɗa mana yadda matsalar ’yan Adam ta fara. Littafi na ƙarshe ya nuna mana yadda dukan duniya za ta zama aljanna, ko kuma lambu. Dukan littattafai na Littafi Mai Tsarki sun ba da tarihin shekaru dubbai na rayuwa da kuma yadda suka shafi cikar nufin Allah. Jituwa na Littafi Mai Tsarki tana da ban sha’awa, kuma haka littafi daga Allah ya kamata ya kasance.

8 Littafi Mai Tsarki cikakke ne a batun kimiyya. Ya ƙunshi bayani ma da ya wuce na zamaninsa. Alal misali, Leviticus yana ɗauke da dokoki domin Isra’ila ta dā game da keɓewa da kuma tsabta sa’ad da al’ummai da suke maƙwabtaka da su ba su san kome ba game da wannan. Sa’ad da ba a fahimci siffar duniya ba, Littafi Mai tsarki ya ce duniya tana kama da ƙwai. (Ishaya 40:22) Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya ‘rataye duniya ba bisa kome ba.’ (Ayuba 26:7) Hakika, Littafi Mai Tsarki ba littafin kimiyya ba ne. Amma sa’ad da ya yi magana a kan batun kimiyya daidai yake. Ba haka za mu yi tsammanin littafi daga wurin Allah ba?

9 Littafi Mai Tsarki abin dogara ne wajen tarihi. Labaransa takamammu ne. Ya ƙunshi sunayen mutane har da tarihin zuriyarsu.# Ya bambanta da ’yan tarihi, waɗanda sau da yawa ba sa faɗan yadda aka ci mutanensu a yaƙi, marubutan Littafi Mai Tsarki masu gaskiya ne, sun rubuta har kurakuransu da na al’ummarsu. Alal misali a cikin littafin Lissafi, marubuci Musa ya faɗi kurensa mai tsanani wanda ya sa aka yi masa horo. (Littafin Lissafi 20:2-12) Irin wannan gaskiya ba ta samuwa a cikin wasu littattafan tarihi amma tana samuwa cikin Littafi Mai Tsarki domin littafin Allah ne.

LITTAFI CIKE DA HIKIMA

10 Domin Littafi Mai Tsarki hurarre ne daga Allah yana da amfani wajen “koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma.” (2 Timothawus 3:16) Hakika, Littafi Mai Tsarki littafi ne mai amfani. Ya nuna fahimi sosai ga yanayi na ’yan Adam. Ba abin mamaki ba ne—Mawallafinsa Jehobah Allah, shi ne Mahalicci! Ya san tunaninmu da motsin zuciyarmu fiye da yadda muke tsammani. Ƙari ga haka, Jehobah ya san abin da muke bukata domin mu yi farin ciki. Ya san kuma tafarkin da ya kamata mu guje wa.

11 Ka yi la’akari da jawabin Yesu da ake kira Huɗuba bisa Dutse, da ke rubuce a Matta surori 5 zuwa 7. A cikin wannan fitacciyar koyarwarsa, Yesu ya yi magana game da abubuwa da yawa, har da yadda za a sami farin ciki na gaske, yadda za a yi sulhu, yadda za a yi addu’a, da yadda za a ɗauki abin duniya. Kalmomin Yesu suna da amfani a yau kamar yadda suke sa’ad da ya faɗe su.

12 Wasu mizanan Littafi Mai Tsarki suna magana ne game da zaman iyali, yadda za a yi aiki, da kuma dangantaka da wasu. Mizanan Littafi Mai Tsarki ya shafi dukan mutane, kuma gargaɗinsa a kullayaumi yana da amfani. Hikima da take cikin Littafi Mai Tsarki an taƙaita ta cikin kalmar Allah ta bakin annabi Ishaya: “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya ke koya maka zuwa amfaninka.”—Ishaya 48:17.

LITTAFI NE NA ANNABCI

13 Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi annabce-annabce masu yawa, da yawa kuma cikinsu sun riga sun cika. Ga wani misali. Ta bakin annabi Ishaya, wanda ya rayu a ƙarni na takwas K.Z., Jehobah ya annabta cewa birnin Babila za a halaka ta. (Ishaya 13:19; 14:22, 23) An ba da bayani dalla-dalla a nuna yadda hakan za ta faru. Sojoji mahara za su janye ruwan kogin Babila kuma su shiga cikin birnin ba tare da ɗauki ba daɗi ba. Da ƙari ga wannan. Annabcin Ishaya har ya ba da sunan sarkin da zai ci Babila—Cyrus.—Ishaya 44:27-45:2.

Marubucin Littafi Mai Tsarki Ishaya ya annabta halakar Babila

Wani mutum yana bincike a kan faɗuwar Babila

14 Shekaru 200 bayan haka—a daren 5 ko 6 ga Oktoba, 539 K.Z., dakaru suka yi zango a kusa da Babila. Waye ne shugabansu? Sarkin Fasiya mai suna Cyrus. Hanya ta buɗe na cika annabci da ban mamaki. Amma sojojin Cyrus za su shiga Babila ne ba tare da sun yi ɗauki ba daɗi ba kamar yadda aka annabta?

15 A wannan daren mutanen Babila suna cikin biki kuma suna jin babu dalilin tashin hankali domin manyan ganuwansu. Cyrus kuma cikin hikima ya kawar da ruwan kogin da ya bi cikin birnin. Ba da daɗewa ba ruwan ya janye yadda sojojinsa za su iya ketare kogin da ƙafa su tunkari ganuwar birnin. Amma ta yaya sojojin Cyrus za su sami wuce ganuwar Babila? Domin wasu dalilai a wannan daren an yi sakaci an bar ƙofofin birnin a buɗe!

16 Game da Babila, an annabta: “Ba za ta zama da mutane a cikinta ba daɗai, ba kuwa za a zauna a cikinta ba daga tsara zuwa tsara: Ba-larabe ba za ya kafa tent nasa a wurin ba; makiyaya kuma ba za su yi makwantar garkensu a wurin ba.” (Ishaya 13:20) Wannan annabci na halakar birnin ne, da kuma yadda zai kasance bayan haka. Ya nuna cewa Babila za ta halaka har abada abadin. Za ka ga tabbacin cikar wannan annabcin. Inda Babila ta dā take mil 50 ne yamma da Bagadaza ta Iraƙi kuma babu wanda yake zaune cikinta, hakan ya tabbatar da abin da Jehobah ya faɗa ta bakin Ishaya ya faru: “[Zan] share ta kuma da tsintsiyar hallaka.”—Ishaya 14:22, 23.%

Kango na Babila

Kangon Babila

17 Ganin yadda Littafi Mai Tsarki littafi ne na annabci da za a dogara da shi abin ƙarfafa bangaskiya ne, ko ba haka ba? Hakika, Jehobah Allah ya cika alkawuransa na dā, muna da kyawawan dalilai na gaskata cewa zai cika alkawuransa na aljanna a duniya. (Littafin Lissafi 23:19) Babu shakka, muna da “bege na rai mara-matuƙa, wanda Allah, da ba shi iya yin ƙarya, ya alkawarta tun gaban madawaman zamanu.”—Titus 1:2.^

“MAGANAR ALLAH MAI-RAI CE”

18 Daga abin da muka riga muka bincika a wannan babi, ya bayyana sarai cewa Littafi Mai Tsarki ba na biyunsa. Duk da haka, muhimmancinsa ya fice jituwarsa kawai, ƙwarewarsa a kimiyya da kuma tarihi, da hikima da kuma annabcin abin dogara. Manzo Bulus Kirista ya rubuta: “Maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa, ta fi kowane takobi mai-kaifi biyu ci, tana kuwa hudawa har zuwa rarraban rai da ruhu, da gaɓaɓuwa da ɓargo kuma, tana kuwa da hamzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.”—Ibraniyawa 4:12.

19 Karatun “maganar” Allah, ko kuma saƙon Littafi Mai Tsarki zai iya sāke rayuwarmu. Zai taimake mu mu binciki kanmu yadda ba mu taɓa yi ba. Za mu yi da’awar muna ƙaunar Allah, amma yadda muka amsa kiran hurarriyar Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, za ta bayyana tunaninmu, da kuma manufar zuciyarmu.

20 Littafi Mai Tsarki hakika littafi ne daga Allah. Littafi ne da za mu yi karatu, mu yi nazari, mu kuma ƙaunace shi. Ka nuna godiyarka ga wannan kyauta daga Allah ta wajen ci gaba da bincika abin da ya ƙunsa. Sa’ad da ka yi haka, za ka fahimci nufin Allah ga ’yan adam da kyau. Za a tattauna abin da wannan manufa take nufi da kuma yadda za ta kasance a babi na gaba.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

  • Littafi Mai Tsarki hurarre ne daga Allah saboda haka cikakke ne kuma abin dogara ne.—2 Timothawus 3:16.
  • Bayani da ke cikin Kalmar Allah yana da amfani a rayuwar yau da kullum.—Ishaya 48:17.
  • Alkawuran Allah da ke cikin Littafi Mai Tsarki a tabbace yake cewa zai cika su.—Littafin Lissafi 23:19.

*  Ko da yake wasu mutane sun ce wasu ɓangarori na Littafi Mai Tsarki ba su jitu da wasu ɓangarori ba, wannan da’awar ba ta da tushe. Ka dubi babi na 2 na littafin nan Sanin da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada da Shaidun Jehobah suka wallafa.

#  Alal misali, ka kula da cikakken zuriyarar Yesu da aka rubuta a Luka 3:23-38.

%  Domin ƙarin bayani game da annabcin Littafi Mai Tsarki, ka dubi shafuffuka na 27-29 na mujallar nan Littafi Don Dukan Mutane, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

^  Halakar Babila misali ne guda kawai na annabcin Littafi Mai Tsarki da ya cika. Wasu misalai sun haɗa da halakar Tyre da Nineveh. (Ezekiel 26:1-5; Zephaniah 2:13-15) Har ila, annabcin Daniel ya nuna dauloli da za su mallaki duniya da za su bayyana bayan Babila. Waɗannan sun haɗa da Media da Persia da kuma Hellas. (Daniel 8:5-7, 20-22) Dubi Rataye domin ƙarin bayani game da annabce-annabce masu yawa game da Almasihu da suka cika ga Yesu Kristi.


Tambayoyin Nazari

1, 2. A waɗanne hanyoyi ne Littafi Mai Tsarki kyauta ne mai ba da farin ciki daga Allah?

3. Menene muka koya game da Jehobah daga kyautar Littafi Mai Tsarki da ya yi mana, kuma me ya sa wannan yake da ban sha’awa?

4. Menene ya burge ka game da yadda Littafi Mai Tsarki ya bambanta?

5. A wace hanya ce Littafi Mai Tsarki “hurarre daga wurin Allah” ne?

6, 7.Me ya sa jituwa ta littattafai na Littafi Mai Tsarki abin kula ne musamman?

8. Ka ba da misalin da zai nuna cewa Littafi Mai Tsarki cikakke ne a batun kimiyya.

9. (a) A waɗanne hanyoyi ne Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa tarihinsa cikakken ne kuma abin dogara? (b) Menene faɗin gaskiya na marubutansa ya nuna maka game da Littafi Mai Tsarki?

10. Me ya sa ba abin mamaki ba ne cewa Littafi Mai Tsarki littafi ne mai amfani?

11, 12. (a) Waɗanne batutuwa Yesu ya yi magana a kan su a Huɗuba a kan Dutse? (b) Waɗanne batutuwa aka yi maganarsu cikin Littafi Mai Tsarki, kuma me ya sa wannan gargaɗi ba shi da lokaci?

13. Wane bayani ne dalla-dalla Jehobah ya huri annabi Ishaya ya rubuta game da Babila?

14, 15. Ta yaya wasu bayanai game da annabcin Ishaya suka cika game da Babila?

16. (a) Menene Ishaya ya faɗa game da ƙarshen Babila? (b) Ta yaya annabcin Ishaya game da halakar Babila ya cika?

17. Ta yaya ne cika annabcin Littafi Mai Tsarki yake ƙarfafa bangaskiya?

18. Wane bahasi mai ƙarfi manzo Bulus Kirista ya yi game da “maganar Allah”?

19, 20. (a) Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimake ka ka binciki kanka? (b) Ta yaya za ka nuna godiyarka ga wannan kyauta mai muhimmanci daga Allah Littafi Mai Tsarki?