Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA SHA SHIDA

Ka Dage Domin Bauta ta Gaskiya

Ka Dage Domin Bauta ta Gaskiya

Menene Littafi Mai Tsarki ya koyar game da amfani da sifofi wajen bauta?

Yaya Kiristoci suke ɗaukan ranaku masu tsarki na addinai?

Ta yaya za ka yi bayani game da abin da ka gaskata ba tare da sa wasu sun fusata ba?

A CE ka fahimci cewa dukan unguwarku ta gurɓata. Wani yana ta zuba guba a ɓoye, kuma yanayin wurin ya kasance yana da haɗari ga rayuwa. Me za ka yi? Hakika, za ka ƙaura idan ka sami dama. Amma bayan ka ƙaura ma, za ka tambayi kanka, ‘Gubar ta shafe ni ne?’

2 Yanayi mai kama da haka ta samu game da addini na ƙarya. Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa irin wannan bauta ta gurɓata da koyarwa marasa gaskiya da ayyuka marasa tsabta. (2 Korinthiyawa 6:17) Abin da ya sa ke nan yake da muhimmanci a gare ka ka fito daga “Babila Babba,” daular addinan ƙarya na duniya. (Ru’ya ta Yohanna 18:2, 4) Ka yi hakan kuwa? Idan ka yi haka, to, barkanka. Amma kana bukatar fiye da yin murabus daga addinin ƙarya. Bayan haka, dole ka tambayi kanka, ‘Shin da wani ɗigon bauta ta ƙarya da ta rage a gare ni?’ Ga wasu misalai.

SIFFOFI DA BAUTAR KAKANNI

Ire-iren bautar da ake yi a duniya

3 Wasu suna da siffofi ko kuma wuraren bauta a gidajensu na shekaru da yawa. Kai ma kana da su? Idan haka ne, to, kana iya jin cewa baƙon abu ne ko kuma ba daidai ba ne a yi wa Allah addu’a ba tare da waɗannan abubuwa da ake gani ba. Wataƙila ka ga cewa kana ƙaunar waɗannan abubuwa. Amma Allah ne mai faɗin yadda yake so a bauta masa, kuma Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa ba ya so mu yi amfani da siffofi. (Fitowa 20:4, 5; Zabura 115:4-8; Ishaya 42:8; 1 Yohanna 5:21) Saboda haka kana iya dagewa domin bauta ta gaskiya ta wajen halaka dukan wani abin da ka mallaka da yake da alaƙa da bauta ta ƙarya. Ka ɗauke su kamar yadda Jehobah yake ɗaukansu—abin “ƙyama.”—Kubawar Shari’a 27:15.

4 Yawancin addinan ƙarya suna bauta wa kakanni. Kafin su koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki, wasu sun gaskata cewa matattu suna raye a wani lardi marar-ganuwa, kuma za su iya taimaka wa ko yi wa rayayyu lahani. Wataƙila kana ƙoƙari matuƙa domin ka faranta wa kakanni da suka mutu rai. Amma kamar yadda ka fahimta daga Babi na 6 na wannan littafin, matattu ba sa rayuwa a ko’ina. Saboda haka, babu wani amfani a yi ƙoƙarin magana da su. Dukan wani saƙo daga waɗanda muke ƙauna da suka mutu ya fito ne daga aljanu. Saboda haka, Jehobah ya hana Isra’ilawa ƙoƙarin magana da matattu ko kuma su yi kowane irin sihiri.—Kubawar Shari’a 18:10-12.

5 Idan kana amfani da siffofi ko kuma kana bauta wa kakanni dā, me za ka yi? Ka karanta kuma ka yi bimbini bisa Nassosi da suka nuna yadda Allah yake ɗaukan waɗannan abubuwa. Ka yi wa Jehobah addu’a kullum game da muradin ka ka dage domin bauta ta gaskiya, kuma ka roƙe shi ya taimake ka ka riƙa tunani kamar yadda yake yi.—Ishaya 55:9

KIRISTOCI NA FARKO BA SU YI BIKIN KIRSIMATI BA

6 Bauta ta ƙarya za ta iya gurɓata bautar mutum ta wajen bukukuwa. Alal misali, ka yi la’akari da Kirsimati. Kirsimati wai bikin tuna haihuwar Yesu Kristi ne, kuma kusan dukan wani rukunin addini da ya ce shi Kirista ne yana bikin. Duk da haka, babu wani tabbaci cewa almajiran Yesu na ƙarni na farko sun yi wannan bikin. Littafin nan Sacred Origins of Profound Things ya ce: “Ƙarnuka biyu bayan haihuwar Kristi, babu wanda ya san ainihin lokacin da aka haife shi, mutane ƙalilan ne suka damu da ainihin lokacin da aka haife shi.”

7 Ko da almajiran Yesu sun san ainihin ranar da aka haife shi, ba za su yi biki ba. Me ya sa? Domin kamar yadda The World Book Encyclopedia ya ce, Kiristoci na farko sun ɗauki “bikin ranar haihuwar mutum al’adar arna ne.” Bikin ranar haihuwa da aka faɗa a cikin Littafi Mai Tsarki na sarakuna ne biyu da ba sa bauta wa Jehobah. (Farawa 40:20; Markus 6:21) Ana kuma yin bikin haihuwa ga allolin arna domin a ɗaukaka su. Alal misali, a ranar 24 ga Mayu, Romawa suna bikin haihuwar Daina allahiya. Washegari, sai su yi bikin ranar haihuwar rana, allahnsu Apollo. Saboda haka, bikin ranar haihuwa na arna ne ba na Kiristoci ba.

8 Da kuma wani dalili da ya sa Kiristoci na ƙarni na farko ba za su yi bikin haihuwar Yesu ba. Wataƙila almajiransa sun sani cewa bikin ranar haihuwa yana cike da camfi. Alal misali, Helenawa da Romawa da yawa na zamanin dā sun gaskata cewa ruhu yana zuwa wurin haihuwar kowane mutum kuma ya kāre wannan a dukan rayuwarsa. “Wannan ruhun yana da dangantaka da allahn da a ranar haihuwarsa aka haifi mutumin,” in ji littafin nan The Lore of Birthdays. Hakika, Jehobah ba zai ji daɗin dukan wani biki ba da zai haɗa Yesu da camfi. (Ishaya 65:11, 12) To ta yaya mutane da yawa suka zo ga yin bikin Kirsimati?

ASALIN KIRSIMATI

9 Shekaru ɗarurruwa sun shige bayan Yesu ya rayu a duniya kafin mutane suka fara bikin haihuwarsa a ranar 25 ga Disamba. Amma wannan ma ba ranar haihuwar Yesu ba ce, domin an haife shi a watan Oktoba.* To, me ya sa aka zaɓi ranar 25 ga Disamba? Wasu da suke da’awar cewa su Kiristoci ne wataƙila “suna so ne ranar ta yi daidai da ranar bikin haihuwar rana da ba a nasara a kanta ta Romawa.’” (The New Encyclopædia Britannica) A lokacin sanyi, sa’ad da rana ba ta da zafi sosai, arna suna bukukuwa domin rana ta komo daga tafiya mai nisa da ta yi. Sun yi tunanin cewa ranar 25 ga Disamba ce ranar da rana take juyowa. Domin su sa arna su tuba, shugabannin addini suka karɓi wannan bikin kuma suka mai da shi ya kasance na “Kiristoci.”#

10 Da daɗewa aka fahimci asalin Kirsimati. Domin tushensa aka hana Kirsimati a Ingila da kuma wasu yankunan Amirka a ƙarni na 17. Duk wanda ya zauna a gida ranar Kirsimati zai biya diyya. Ba da daɗewa ba, tsohuwar al’adar ta komo, kuma aka daɗa wasu sababbi. Kirsimati ya ƙara zama ranar babban biki, kuma har a yanzu haka yake a ƙasashe da yawa. Amma, domin nasabar Kirsimati da bauta ta ƙarya, waɗanda suke so su faranta wa Allah rai ba sa yin bikin Kirsimati ko kuma wani biki da ya samo asali daga bautar arna.%

SHIN ASALIN BIKI YANA DA MUHIMMANCI KUWA?

Za ka sha minti da aka ɗauko a cikin kwata?

Minti a cikin kwata

11 Wasu sun yarda cewa irin wannan bukukuwa kamar su Kirsimati sun samo asali ne daga arna amma duk da haka suna jin cewa ba laifi ba ne a yi bikin. Ban da haka ma, mutane da yawa ba sa tunanin bauta ta ƙarya sa’ad da suke yin biki. Wannan lokaci kuma yana ba wa iyalai zarafin su matso kusa da juna. Haka kake ji? Idan haka ne, to wataƙila ƙaunar iyali ce, ba ƙaunar addinin ƙarya ba, yake sa dagewa ga bauta ta gaskiya yake da wuya. Ka kasance da tabbacin cewa Jehobah da ya kafa tushin iyali, yana son ka more dangantaka mai kyau da ’yan’uwanka. (Afisawa 3:14, 15) Kana iya ƙarfafa wannan dangantakar a hanyar da Allah ya amince da ita. Game da abin da ya kamata mu damu da shi, manzo Bulus ya rubuta: “Kuna gwada abin da ke na yarda ga Ubangiji.”—Afisawa 5:10.

12 Wataƙila kana jin cewa asalin bukukuwa ba su da wani dangantaka da yadda ake yin su a yau. Shin asalinsa yana da wani muhimmanci ne? Hakika! Alal misali: A ce ka ga minti a cikin kwata. Za ka ɗauki mintin ne ka sha? Ba daidai ba ne! Wannan mintin ba shi da tsabta. Kamar wannan mintin, bukukuwa suna da daɗi, amma an ɗauko su ne daga wuri marar tsabta. Domin mu dage ga bauta ta gaskiya, muna bukatar mu kasance da ra’ayi irin na annabi Ishaya, wanda ya gaya wa masu bauta ta gaskiya: “Kada ku taɓa wani abu mai-ƙazamta.”—Ishaya 52:11.

NUNA FAHIMI WAJEN SHA’ANI DA MUTANE

13 Za ka fuskanci ƙalubale sa’ad da ka zaɓi ka daina yin bukukuwa. Alal misali, abokan aiki za su yi mamakin abin da ya sa ka daina saka hannu cikin wasu ayyukan bukukuwa a wurin aiki. To, idan aka ba ka kyauta ta Kirsimati fa? Ba daidai ba ne ka karɓa? Idan matarka ko mijinki bai gaskata abin da ka ko kika gaskata ba fa? Ta yaya za ka tabbata cewa yaranka ba sa jin cewa an cuce su domin ba ka yin bukukuwa?

14 Ana bukatar fahimi domin a magance kowane yanayi. Idan mutum ya yi maka barka domin bikin da ake yi, kana iya gode wa mutumin mai yi maka fatan alheri. Amma a ce kana tare ne da mutumin da kake gani ko kuma kake aiki da shi kullum. A irin wannan yanayi kana iya yi masa bayani. A dukan yanayi, ka yi magana cikin basira. Littafi Mai Tsarki ya ba da shawara: “Bari zancenku kullum ya kasance tare da alheri, gyartace da gishiri, domin ku sani yadda za ku amsa tambayar kowa.” (Kolossiyawa 4:6) Ka mai da hankali domin kada ka raina mutane. Maimakon haka, ka yi musu bayanin matsayinka cikin basira. Ka bayana musu cewa ba ka ƙin kyauta kuma ba ka ƙin gaisuwa amma ka fi son haka a wani lokaci dabam.

15 Idan wani yana so ya yi maka kyauta fa? Ya dangana bisa yanayin. Mai bayarwa yana iya cewa: “Na sani ba ka yin wannan bikin. Duk da haka, ina so in ba ka wannan.” Kana iya shawartawa cewa karɓan wannan kyauta a wannan yanayi ba ɗaya ba ne da yin bikin. Hakika, idan mai bayarwa bai san abin da ka gaskata ba, kana iya gaya masa cewa kai ba ka yin wannan biki. Wannan zai taimaka wajen yin bayanin abin da ya sa ka karɓi kyauta amma ba ka ba da kyauta a wannan lokaci ba. A wani ɓangare kuma, zai fi kyau kada ka karɓi kyauta idan an bayar ne domin a nuna cewa ba ka manne wa abin da ka gaskata ko kuma ka ƙi abin da ka gaskata saboda abin duniya.

WAƊANDA SUKE CIKIN IYALINKA KUMA FA?

16 Idan wani cikin iyali bai gaskata abin da ka gaskata ba fa? Har ila, ka nuna basira. Babu bukatar ka riƙa mita domin al’ada ko kuma biki da ɗan’uwanka ya zaɓi ya yi. Maimakon haka, ka fahimci cewa suna da ’yancin su kasance da ra’ayinsu, kamar yadda kake so su daraja naka ’yancin. (Matta 7:12) Ka guji dukan wani abin da zai sa ka saka hannu cikin bikin. Duk da haka, ka kasance mai sanin ya kamata idan ya kai ga batutuwa da ba su kasance yin bikin ba. Hakika, ko da yaushe ka yi abin da zai sa lamirinka ya kasance da tsabta.—1 Timothawus 1:18, 19.

17 Menene za ka yi domin kada ’ya’yanka su ji an cuce su domin ba ka yin bukukuwan arna? Yawanci ya dangana bisa abin da kake yi a wasu lokatai na shekara. Wasu iyaye suna zaɓan lokaci da za su yi wa ’ya’yansu kyauta. Kyauta mafi kyau da za ka yi wa ’ya’yanka ita ce lokaci da kula.

KA YI BAUTA TA GASKIYA

Wata iyali tana bauta wa Allah

Yin bauta ta gaskiya yana kawo farin ciki na gaske

18 Domin ka faranta wa Allah rai, dole ne ka guji bauta ta ƙarya ka dage domin bauta ta gaskiya. Menene wannan ya ƙunsa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu, kamar yadda waɗansu sun saba yi, amma mu gargaɗadda juna; balle fa yanzu, da kuna ganin ranan nan tana gusowa.” (Ibraniyawa 10:24, 25) Tarurruka na Kirista lokatai ne na farin ciki domin ka bauta wa Allah a hanyar da ya amince da ita. (Zabura 22:22; 122:1) A irin waɗannan tarurruka, ana “ƙarfafawa” juna a tsakanin Kiristoci masu aminci.—Romawa 1:12.

19 Wata hanya kuma da za ka dage domin bauta ta gaskiya ita ce ta wajen gaya wa mutane game da abubuwa da kake koya daga nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Mutane da yawa suna “ajiyar zuci, suna kuwa kuka” saboda mugunta da ake yi a duniya a yau. (Ezekiel 9:4) Wataƙila ka san mutane da suke jin haka. Ka gaya musu game da begenka daga Littafi Mai Tsarki game da nan gaba kuwa? Sa’ad da kake hulɗa da Kiristoci na gaskiya kuma kake gaya wa mutane game da gaskiya mai ban sha’awa ta Littafi Mai Tsarki da ka koya, za ka ga cewa dukan abin muradi da kake da shi na al’adun addinin ƙarya a hankali zai ɓace. Ka tabbata cewa za ka yi farin ciki ƙwarai kuma za ka sami albarkatu masu yawa idan ka dage domin bauta ta gaskiya.—Malachi 3:10.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

  • Ba a amince da siffofi ba ko bautar kakanni a bauta ta gaskiya.—Fitowa 20:4, 5; Kubawar Shari’a 18:10-12.
  • Ba daidai ba ne mu saka hannu cikin bukukuwa da suka samo asali daga bauta ta arna.—Afisawa 5:10.
  • Kiristoci na gaskiya su yi bayanin abin da suka gaskata ga wasu cikin basira.—Kolossiyawa 4:6.

*  Ka dubi Rataye.

#  Satunaliya wani bikin Romawa ma ya shafi zaɓan ranar 25 ga Disamba. Ana wannan bikin domin a ɗaukaka allahn Romawa na noma a ranakun 17-24 ga Disamba. Ana ci, ana sha, ana yin kyauta ga mutane a wannan ranaku na Satunaliya.

%  Domin ƙarin bayani game da yadda Kiristoci na gaskiya suke ɗaukan wasu ranakun biki, dubi Rataye.


Tambayoyin Nazari

1, 2. Wace tambaya kake bukatar ka tambayi kanka bayan ka bar addinin ƙarya, kuma me ya sa kake tsammanin wannan yana da muhimmanci?

3. (a) Menene Littafi Mai Tsarki ya ce game da amfani da siffofi, kuma me ya sa zai yi wa wasu wuya su amince da yadda Allah yake ɗaukansu? (b) Me ya kamata ka yi da dukan wani abin da ka mallaka da yake da alaƙa da bauta ta ƙarya?

4. (a) Ta yaya muka sani cewa bauta wa kakanni a banza ne? (b) Me ya sa Jehobah ya hana mutanensa su saka hannu cikin kowane irin sihiri?

5. Me za ka yi idan kana amfani da siffofi ko kuma bauta wa kakanni dā?

6, 7. (a) Kirsimati wai bikin menene ne, amma shin mabiyan Yesu na ƙarni farko sun yi wannan bikin kuwa? (b) Su waye suke bikin ranar haihuwa a lokacin almajiran Yesu na farko?

8. Ka yi bayani game da dangantaka da take tsakanin bikin ranar haihuwa da camfi.

9. Ta yaya aka zo ga kafa ranar 25 ga Disamba a zaman ranar bikin haihuwar Yesu?

10. A dā, me ya sa wasu mutane ba su yi bikin Kirsimati ba?

11. Me ya sa wasu mutane suke bukukuwa, amma me ya kamata mu damu da shi?

12. Ka ba da misalin abin da ya sa ya kamata mu guje wa al’adu da kuma bukukuwa da suke da mummunan asali.

13. Waɗanne ƙalubale ne za ka fuskanta sa’ad da ka daina yin bukukuwa?

14, 15. Menene za ka yi idan aka yi maka barka da wani biki ko kuma idan wani ya so ya ba ka kyauta?

16. Ta yaya za ka nuna basira sa’ad da kake bi da batutuwa da suka shafi bukukuwa?

17. Ta yaya za ka taimaki ’ya’yanka kada su ji cewa ka cuce su sa’ad da suka ga wasu suna yin bukukuwan?

18. Ta yaya halartar tarurruka na Kirista zai taimake ka ka dage domin bauta ta gaskiya?

19. Me ya sa yake da muhimmanci ka gaya wa mutane abin da ka koya daga Littafi Mai Tsarki?