Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA SHIDA

Ina Matattu Suke?

Ina Matattu Suke?

Me yake faruwa da mu sa’ad da muka mutu?

Me ya sa muke mutuwa?

Me ya sa sanin gaskiya game da mutuwa yake ba da kwanciyar hankali?

WAƊANNAN tambayoyi ne da mutane suka yi tunaninsu na shekaru dubbai. Tambayoyi ne masu muhimmanci ƙwarai. Ko su wanene mu, kuma ko ina muke zaune, amsoshin sun shafi kowannenmu.

2 A babi na baya, mun tattauna yadda hadayar fansa ta Yesu Kristi ta buɗe hanyar rai madawwami. Mun kuma koyi cewa Littafi Mai Tsarki ya yi maganar lokaci da “mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) Amma a yanzu, dukanmu muna mutuwa. “Masu-rai sun san za su mutu,” in ji Sarki Sulemanu mai hikima. (Mai-Wa’azi 9:5) Muna so mu sami tsawon rai. Duk da haka, muna tunanin menene zai faru da mu sa’ad da muka mutu.

3 Sa’ad da waɗanda muke ƙauna suka mutu, sai mu yi makoki. Wataƙila kuma mu yi tambaya: ‘Menene yake faruwa da su? Suna wahala ne? Suna kāre mu ne? Za mu iya taimakonsu kuwa? Za mu sake ganinsu kuwa?’ Addinai na duniya sun ba da amsoshi dabam dabam ga waɗannan tambayoyi. Wasu sun koyar da cewa idan ka yi rayuwa ta kirki, za ka tafi sama amma idan ka yi mummunar rayuwa, za a ƙona ka a wutar jahannama. Wasu kuma sun koyar da cewa sa’ad da mutum ya mutu, sai ya je duniyar matattu ya sadu da kakanni. Har ila wasu addinai kuma sun koyar da cewa matattu suna zuwa wata duniya inda za a yi musu shari’a sai kuma a sake haifansu da wani jiki dabam.

4 Dukan waɗannan koyarwa na addinai ra’ayin iri ɗaya ne—cewa wani ɓangaren jikinmu yana tsira bayan mutuwar jiki na zahiri. Kusan dukan wani addini na dā ko na zamani, ya nuna cewa muna rayuwa har abada ba tare da gani, ko ji ko kuma tunani ba. Amma, ta yaya hakan zai kasance? Hankalinmu, tare da tunaninmu, suna da nasaba da ƙwaƙwalwarmu. Sa’ad da muka mutu, ƙwaƙwalwarmu tana daina aiki. Tunaninmu, da kuma hankalinmu ba sa ci gaba da aiki ba tare da wani alaƙa ba ta wata hanya da ke da wuyar ganewa. Ba sa tsira wa halakar ƙwaƙwalwarmu.

MENENE AINIHI YAKE FARUWA A MUTUWA?

Kandir da aka kashe wutar

Ina wutar ta tafi?

5 Abin da yake faruwa a mutuwa ba mai wuya ba ne ga Jehobah, Mahaliccin ƙwaƙwalwa. Ya san gaskiya, kuma a cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, ya yi bayani game da yanayin matattu. Koyarwarsa mai sauƙin fahimta, ita ce: Sa’ad da mutum ya mutu, ya daina wanzuwa. Mutuwa kishiyar rai ce. Matattu ba sa gani, ba sa ji, ba sa tunani. Babu wani abin da yake tsira daga mutuwar jiki. Ba mu da kurwa marar mutuwa.*

6 Bayan Sulemanu ya lura cewa rayayyu sun san cewa za su mutu, sai ya rubuta: ‘Matattu ba su san komi ba.’ Sai ya ƙara bayani game da wannan gaskiya yana cewa matattu ba za su iya ƙauna ko ƙiyayya ba kuma “babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari inda za ka.” (Mai-Wa’azi 9:5, 6, 10) Hakazalika, Zabura 146:4 ta ce sa’ad da mutum ya mutu, “shawarwarinsa su kan lalace.” Mu mutane ne kuma ba ma tsira daga mutuwar jikinmu. Rai da muke da shi kamar wutar kyandir ne. Sa’ad da aka kashe wutar ba ta tafiya ko’ina. Hakika ta daina wanzuwa.

ABIN DA YESU YA CE GAME DA MUTUWA

7 Yesu Kristi ya yi magana game da yanayin matattu. Ya yi hakan game da Li’azaru, mutum da ya sani sosai da ya mutu. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Abokinmu Li’azaru yana barci.” Almajiran suna tsammanin cewa Yesu yana nufin Li’azaru yana barcin hutawa ne, domin yana samun sauƙi daga rashin lafiyarsa. Amma ba haka yake nufi ba. Yesu ya yi bayani: “Li’azaru ya mutu.” (Yohanna 11:11-14) Ka lura cewa Yesu ya kwatanta mutuwa da hutu da kuma barci. Li’azaru bai je sama ba kuma ba a jefa shi jahannama ba. Ba ya tare da mala’iku ko kuma da kakanni. Kuma ba a haifi Li’azaru ba ya zama wani mutum dabam. Yana hutawa ne cikin mutuwa, kamar dai yana barci ne mai zurfi ba tare da mafarki ba. Wasu nassosi ma sun kwatanta mutuwa da barci. Alal misali, sa’ad da aka jejjefi Istafanus aka kashe shi, Littafi Mai Tsarki ya ce “ya yi barci.” (Ayukan Manzanni 7:60) Hakazalika, manzo Bulus ya rubuta game da wasu a zamaninsa da suka ‘yi barcin’ mutuwa.—1 Korinthiyawa 15:6.

Ma’aurata masu farin ciki

Jehobah ya halicci mutane su rayu har abada a duniya

8 Shin ainihin nufin Allah ne mutane su mutu? A’a! Jehobah ya halicci mutum domin ya rayu har abada a duniya. Kamar yadda muka koya a baya a wannan littafin, Allah ya saka ma’aurata na fari a cikin aljanna mai ni’ima. Ya albarkace su da ƙoshin lafiya. Jehobah ya bukaci musu abin da ke mai kyau. Da wani mahaifi da zai so ’ya’yansa su wahala daga azaba ta tsufa da kuma mutuwa? Hakika, babu! Jehobah yana ƙaunar ’ya’yansa kuma yana so su more rayuwa cikin farin ciki a duniya. Game da mutane, Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Jehobah] ya kuma sa madawaman zamanai a cikin zuciyarsu.”’ (Mai-Wa’azi 3:11) Allah ya halicce mu da muradin mu ci gaba da rayuwa har abada. Kuma ya buɗe hanyar biyan wannan muradi.

ABIN DA YA SA MUTANE SUKE MUTUWA

9 To, me ya sa mutane suke mutuwa? Domin mu sami amsar, dole ne mu bincika abin da ya faru sa’ad da mutane biyu ne kawai mata da miji suke duniya. Littafi Mai Tsarki ya yi bayani: “Kowane itacen da ke mai-sha’awan gani, masu-kyau kuwa domin ci, Ubangiji Allah ya sa ya tsiro daga ƙasa.” (Farawa 2:9) Amma, da wani abin da ya hana. Jehobah ya gaya wa Adamu: “An yarda maka ka ci daga kowane itacen gona a sāke: amma daga itace na sanin nagarta da mugunta ba za ka ɗiba ba ka ci: cikin rana da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.” (Farawa 2:16, 17) Wannan umurnin ba shi da wuyar a bi shi. Da wasu itatuwa da yawa da Adamu da Hauwa’u za su ci. Sai suka sami zarafi su nuna godiyarsu ta musamman ga Wanda ya ba su dukan abin da suke da shi, haɗe da kamiltaccen rai. Biyayyarsu za ta nuna cewa suna daraja ikon Ubansu na samaniya kuma suna son ja-gorarsa ta ƙauna.

10 Abin baƙin ciki, ma’aurata na farko suka zaɓi su yi wa Jehobah rashin biyayya. Da yake magana ta bakin maciji, Shaiɗan ya tambayi Hauwa’u: “Ashe, ko Allah ya ce, ba za ku ci daga dukan itatuwa na gona ba?” Hauwa’u ta amsa: “Daga ’ya’ya na itatuwan gona an yarda mamu mu ci: amma daga ’ya’yan itace wanda ke cikin tsakiyar gona, Allah ya ce, ba za ku ci ba, ba kuwa za ku taɓa ba, domin kada ku mutu.”—Farawa 3:1-3.

11 “Ba lallai ba za ku mutu ba,” in ji Shaiɗan. “Allah ya sani ran da kuka ci daga ciki, ran nan idanunku za su buɗe, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta.” (Farawa 3:4, 5) Shaiɗan yana so Hauwa’u ta gaskata cewa ita za ta amfana idan ta ci ’ya’yan itace da aka hana. In ji shi, za ta zaɓi wa kanta abin da ke nagarta da mugunta; za ta yi abin da take so. Shaiɗan kuma ya ce Jehobah ƙarya yake yi game da sakamakon cin ’ya’yan itacen. Hauwa’u ta gaskata Shaiɗan. Sai ta ci ’ya’yan itacen. Sai ta ba da wasu ga mijinta, shi ma ya ci. Ba cikin rashin sani ba ne suka yi hakan. Sun sani cewa suna yin abin da Allah ya gaya musu kada su yi. Ta wajen cin ’ya’yan itacen, sun ƙi yin biyayya da gangan ga umurni mai sauƙi. Sun nuna suna ƙyamar Ubansu na samaniya da kuma ikonsa. Irin wannan reni ga Mahaliccinsu mai ƙauna ba abin gafartawa ba ne!

12 Alal misali: Yaya za ka ji idan ka raini kuma ka ƙaunaci yaro ko yarinya wanda ya yi maka rashin biyayya a hanyar da ta nuna ba ya ganin mutuncinka ba ya ƙaunarka? Wannan zai ɓata maka rai ƙwarai. To, ka yi tunanin yadda Jehobah ya ji sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka bi tafarkin hamayya da shi.

Allah yana halittar Adamu daga turɓaya

Adamu ya fito daga turɓaya, kuma ya koma turɓaya

13 Jehobah ba shi da wani dalilin ci gaba da raya Adamu da Hauwa’u. Suka mutu, kamar yadda ya ce zai faru da su. Adamu da Hauwa’u suka daina wanzuwa. Ba su ƙaura zuwa duniyar ruhu ba. Mun fahimci haka domin abin da Jehobah ya gaya wa Adamu bayan ya gaya masa laifinsa. Allah ya ce: “[Za] ka koma ƙasa; gama daga cikinta aka ciro ka, gama turɓaya ne kai, ga turɓaya za ka koma.” (Farawa 3:19) Allah ya halicci Adamu daga turɓaya. (Farawa 2:7) Kafin nan, Adamu bai wanzu ba. Saboda haka, sa’ad da Jehobah ya ce Adamu zai koma turɓaya, yana nufi ne cewa Adamu zai koma yanayinsa na rashin wanzuwa. Adamu zai zama marar rai kamar turɓaya da aka yi sa da ita.

14 Da Adamu da Hauwa’u suna da rai a yau, amma sun mutu domin sun zaɓi su yi wa Allah rashin biyayya kuma saboda haka suka yi zunubi. Abin da ya sa muke mutuwa shi ne dukanmu zuriyarsa mun gāji yanayin zunubi da kuma mutuwa daga Adamu. (Romawa 5:12) Wannan zunubi kamar wata muguwar cuta ce da muka gāda da babu wanda zai tsira. Sakamakon ta mutuwa, la’ana ce. Mutuwa abokiyar gaba ce, ba abokiya ba. (1 Korinthiyawa 15:26) Ya kamata mu zama masu godiya matuƙa ga Jehobah wanda ya yi tanadin fansa domin ya cece mu daga wannan abokiyar gaba abar tsoro!

SANIN GASKIYA GAME DA MUTUWA YANA DA AMFANI

15 Abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da yanayin matattu yana sanyaya zuciya. Kamar yadda muka gani matattu ba sa shan azaba ko kuma akuba. Babu dalilin jin tsoronsu, domin ba za su iya mana illa ba. Ba sa bukatar taimako daga gare mu, kuma ba za su iya taimakonmu ba. Ba za mu iya magana da su ba, ba za su iya magana da mu ba. Shugaban addinai da yawa suna da’awar cewa za su iya taimakon waɗanda suka mutu, kuma mutane da suka gaskata irin waɗannan shugabanni sai su ba su kuɗi. Amma sanin gaskiya yana ƙare mu daga yaudarar waɗanda suke koyar da irin wannan ƙarya.

16 Shin addininka ya jitu da abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa game da matattu kuwa? Yawanci ba su jitu ba. Me ya sa? Domin Shaiɗan ya rinjayi koyarwarsu. Yana amfani da addinan ƙarya domin ya sa mutane su gaskata cewa bayan jikinsu ya mutu, za su ci gaba da rayuwa a wata duniya ta ruhu. Wannan wata ƙarya ce da Shaiɗan yake haɗawa da wasu ya sa mutane su juya wa Jehobah Allah baya. Ta yaya?

17 Kamar yadda muka gani a baya, wasu addinai sun koyar da cewa idan mutum ya yi mummunar rayuwa, bayan ya mutu zai je wurin da ake azabtar da mutane ya dawwama yana wahala. Irin wannan koyarwar ba ta daraja Allah. Jehobah, Allah ne mai ƙauna ba zai taɓa sa mutane su wahala a wannan hanyar ba. (1 Yohanna 4:8) Yaya za ka ji game da mutumin da ya hori yaronsa marar biyayya ta wajen saka hannunsa cikin wuta? Za ka ɗauki wannan mutumin da mutunci? Za ka ma so ka san irin wannan mutumin? Ba za ka so ba! Wataƙila ka ce lalle mutumin azzalumi ne. Duk da haka, Shaiɗan yana so mu gaskata cewa Jehobah yana azabtar da mutane a cikin wuta har abada—na shekaru biliyoyi marasa iyaka!

18 Shaiɗan kuma yana amfani da wasu addinai ya koyar da cewa bayan mutane sun mutu suna zama ruhohi da dole ne rayayyu su daraja su. In ji irin wannan koyarwa, ruhun matattu suna zama aminai ko kuma abokan gaba. Mutane da yawa sun gaskata wannan ƙarya. Suna tsoron matattu sukan daraja su kuma suna bauta musu. Akasarin haka, Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa matattu suna barci kuma ya ce mu bauta wa Jehobah Allah shi kaɗai, Mahaliccinmu kuma Mai yi mana tanadi.—Ru’ya ta Yohanna 4:11.

19 Sanin gaskiya game da matattu zai kāre ka daga yaudara ta addini. Zai kuma taimake ka ka fahimci wasu koyarwa na Littafi Mai Tsarki. Alal misali, sa’ad da ka fahimci cewa mutane ba sa zuwa duniyar matattu, alkawarin rai madawwami zai kasance da ma’ana a gare ka.

20 A dā can, mutum adali Ayuba ya yi wannan tambayar: “Idan mutum ya mutu za ya sake rayuwa?” (Ayuba 14:14) Shin za a iya ta da mutumin da yake barcin mutuwa zuwa rai kuma? Koyarwar Littafi Mai Tsarki game da wannan yana sanyaya zuciya, kamar yadda babi na gaba zai nuna.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

  • Matattu ba sa gani ba sa ji ba sa tunani.—Mai-Wa’azi 9:5.
  • Matattu suna hutawa ne; ba sa wahala.—Yohanna 11:11.
  • Muna mutuwa domin mun gāji zunubi daga Adamu.—Romawa 5:12.

*  Domin tattaunawa game da kalmar nan “kurwa” ko kuma “ruhu,” don Allah ka dubi Rataye.


Tambayoyin Nazari

1-3. Waɗanne tambayoyi ne mutane suke yi game da matattu, kuma waɗanne amsoshi ne addinai dabam dabam suka bayar?

4. Wane ra’ayi iri ɗaya addinai da yawa suke da shi game da mutuwa?

5, 6. Menene Littafi Mai Tsarki ya koyar game da yanayin matattu?

7. Ta yaya Yesu ya yi bayanin yadda mutuwa take?

8. Ta yaya muka sani cewa ba nufin Allah ba ne mutane su mutu?

9. Wane hani Jehobah ya yi wa Adamu, kuma me ya sa wannan umurnin ba mai wuyan biyayya ba ne?

10, 11. (a) Ta yaya ma’aurata na fari suka yi wa Allah rashin biyayya? (b) Me ya sa rashin biyayya na Adamu da Hauwa’u abu ne mai tsanani?

12. Menene zai taimake mu mu fahimci yadda Jehobah ya ji sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka bi tafarkin hamayya da shi?

13. Menene Jehobah ya ce zai sami Adamu idan ya mutu, kuma menene wannan yake nufi?

14. Me ya sa muke mutuwa?

15. Me ya sa sanin gaskiya game da mutuwa yana sanyaya zuciya?

16. Waye ya rinjayi koyarwar addinai da yawa, kuma ta wace hanya?

17. Me ya sa koyarwar azabtarwa cikin wuta ba ta daraja Jehobah?

18. Bautar matattu ta kasance ne bisa wace ƙarya ta addini?

19. Sanin gaskiya game da mutuwa zai taimake mu mu fahimci wace koyarwa ta Littafi Mai Tsarki?

20. Wace tambaya za mu bincika a babi na gaba?