Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RATAYE

Gano “Babila Babba”

Gano “Babila Babba”

LITTAFIN Ru’ya ta Yohanna ya ƙunshi kalamai da bai kamata a fahimce su a zahiri ba. (Ru’ya ta Yohanna 1:1) Alal misali, ya ambaci wata mace da take da suna “Babila Babba” a rubuce a goshinta. An ce kuma wannan macen tana zaune a kan ‘jama’a ce da al’ummai. (Ru’ya ta Yohanna 17:1, 5, 15) Tun da babu wata mace ta zahiri da za ta iya haka, wannan Babila Babba dole ne ta kasance ta alama. To, menene wannan karuwa ta alamar take wakilta?

A Ru’ya ta Yohanna 17:18, wannan macen aka sake kwatanta ta “babban birnin ne, wanda ke mulkin bisa sarakunan duniya.” Furcin nan “birni” na nuna ƙungiya ce mai tsari na mutane. Tun da wannan “babban birnin” yana mulki bisa “sarakunan duniya,” wannan mace mai sunan Babila Babba za ta kasance ƙungiya ce mai rinjaya a dukan duniya. Ana iya kiranta daula ta duniya. Wace irin daula? Ta Addini. Ka lura da yadda wasu ɓangarorin littafin Ru’ya ta Yohanna suka sa mu kammala hakan.

Daula tana iya kasancewa ta siyasa, ta ciniki, ko kuma ta addini. Macen mai suna Babila Babba ba daular siyasa ba ce domin Kalmar Allah ta ce “sarakunan duniya,” ko kuma ’yan siyasa na duniya sun “yi fasikanci da ita.” Fasikancinta yana nufin haɗa kai da ta yi da sarakunan duniya, wannan ya ba da bayanin abin da ya sa aka kira ta “babbar karuwa.”—Ru’ya ta Yohanna 17:1, 2; Yaƙub 4:4.

Babila Babba ba za ta kasance daular ciniki ba domin “dillalan duniya” da suke wakiltan ’yan ciniki, za su yi mata makoki sa’ad da aka halaka ta. Hakika, an kwatanta sarakuna da kuma attajirai suna kallonta daga “nesa.” (Ru’ya ta Yohanna 18:3, 9, 10, 15-17) Saboda haka, daidai ne a kammala cewa Babila Babba ba daular siyasa ba ce ko ta ciniki, amma ta addini.

Furcin nan ta yaudari dukan al’ummai da ‘sihirinta’ ya sake jaddada cewa Babila Babba addini ce. (Ru’ya ta Yohanna 18:23) Tun da dukan sihiri daga aljannu ne, ba abin mamaki ba ne da Littafi Mai Tsarki ya kira ta “gidan aljannu.” (Ru’ya ta Yohanna 18:2; Kubawar Shari’a 18:10-12) An kwatanta wannan daula kuma da yin hamayya da addini na gaskiya, tana tsananta wa “annabawa” da kuma “tsarkaka.” (Ru’ya ta Yohanna 18:24) Hakika, Babila Babba tana da tsananin ƙi ga addini na gaskiya da take tsananta wa har ma da kashe “shaidu na Yesu.” (Ru’ya ta Yohanna 17:6) Saboda haka, babu sauran shakka cewa wannan macen mai suna Babila Babba tana wakiltan daular addinin ƙarya na duniya, wanda ya haɗa da dukan wani addini da yake hamayya da Jehobah Allah.

← Ka duba inda babin yake