Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA SHA TARA

Ka Tsare Kanka Cikin Ƙaunar Allah

Ka Tsare Kanka Cikin Ƙaunar Allah

Menene yake nufi a ƙaunaci Allah?

Ta yaya za mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah?

Ta yaya Jehobah zai saka wa waɗanda suka kasance cikin ƙaunarsa?

KA YI tunani kana tafiya a cikin hadari mai iska. Gari ya yi duhu. Aka fara walƙiya, aradu ya fara kara, aka fara ruwa kamar da bakin kwarya. Ka fara sauri kana neman mafaka. A nan bakin hanya, ka ga gida. Wurin zai zama maka da muhimmanci!

Wani mutum yana neman mafaka daga hadari da iska

Za ka mai da Jehobah mafakanka a cikin wannan lokaci mai hadari da iska?

2 Muna rayuwa ne a lokacin hadari mai iska. Yanayin duniya yana daɗa ɓaci. Amma da mafaka, da za ta kāre mu daga rauni na dindindin. Mecece wannan? Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa: “Zan ce da Ubangiji, shi ne mafakata da marayata kuma; Allahna, a gareshi ni ke dogara.”—Zabura 91:2.

3 Ka yi tunanin wannan! Jehobah, Mahalicci, kuma Mamallakin sararin samaniya, zai zama maka mafaka mai kāriya. Zai iya kāre mu domin ya fi kowa da kome da zai iya yi mana rauni ƙarfi. Ko ma mun sami rauni, Jehobah yana iya magance wannan. Ta yaya za mu mai da Jehobah mafakarmu? Muna bukatar mu dogara a gare shi. Bugu da ƙari, Kalmar Allah ta aririce mu: “Ku tsare kanku cikin ƙaunar Allah.” (Yahuda 21) Hakika, muna bukatar mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah, muna kyautata dangantakarmu da Ubanmu na sama. Da haka muna iya tabbata cewa shi mafaka ne a gare mu. Amma ta yaya za mu iya ƙulla wannan dangantakar?

KA FAHIMCI KUMA KA AMSA ƘAUNAR ALLAH

4 Domin mu tsaya ga ƙaunar Allah, muna bukatar mu fahimci yadda Jehobah ya nuna ƙaunarsa a gare mu. Ka yi tunanin wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki da ka koya da taimakon wannan littafin. Tun da Mahalicci ne, Jehobah ya ba mu duniya ta zama mana gida mai ban sha’awa. Kuma ya cika ta da abinci da ruwa mai dumbin yawa, ma’adinai, dabbobi, da kuma kyawawan wurare. A matsayin Mawallafin Littafi Mai Tsarki, Allah ya bayyana mana sunansa da kuma halayensa. Ƙari ga haka, Kalmarsa ta nuna cewa ya aiko da Ɗansa da yake ƙauna zuwa duniya, ya ƙyale shi ya wahala kuma ya mutu dominmu. (Yohanna 3:16) Menene wannan kyauta take nufi a gare mu? Ta ba mu bege na rayuwa mai kyau a nan gaba.

5 Begenmu har ila ya dangana ne kuma bisa wani abin da Allah ya yi. Jehobah ya kafa gwamnati a sama, Mulkin Almasihu. Zai kawo ƙarshen dukan wahaloli ba da daɗewa ba kuma ya mai da duniya aljanna. Ka yi tunani! Za mu rayu a nan cikin salama da farin ciki har abada. (Zabura 37:29) A yanzu, Allah yana yi mana ja-gora a kan yadda za mu rayu a hanya mafi kyau. Kuma ya yi mana kyautar addu’a, hanyar magana da shi. Waɗannan wasu hanyoyi ne da Jehobah ya nuna ƙauna ga dukan mutane kuma musamman ma a gare ka.

6 Tambaya mai muhimmanci da ya kamata ka yi shi ne: Ta yaya zan amsa ƙaunar da Jehobah yake yi mini? Mutane da yawa za su ce, “Ni ma zan nuna ina ƙaunar Jehobah.” Kai ma haka kake ji? Yesu ya ce wannan doka ita ta fi kowace: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.” (Matta 22:37) Hakika kana da dalilai masu yawa na ƙaunar Jehobah Allah. Yadda kake ji shi ne ake nufi da ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarka, ranka, da kuma hankalinka?

Ƙwallon tuffa

7 Kamar yadda aka kwatanta a cikin Littafi Mai Tsarki, ƙaunar Allah ta wuce motsin zuciya kawai. Hakika, jin muna ƙaunar Jehobah yana da muhimmanci, wannan motsin zuciyar farkon ƙauna ta gaskiya ce kawai. Ƙwallon mangwaro ne yake girma ya zama itacen mangwaro. Amma idan kana so ka sha mangwaro, sai wani ya ba ka ƙwallon, hakan zai ishe ka? Da ƙyar! Haka nan, jin kana ƙaunar Jehobah Allah mafari ne kawai. Littafi Mai Tsarki yana koyarwa: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.” (1 Yohanna 5:3) Domin ta kasance na gaskiya ƙaunar Allah dole ne ta ba da amfani masu kyau. Dole ne a nuna ta cikin ayyuka.—Matta 7:16-20.

8 Muna nuna ƙaunarmu ga Allah sa’ad da muka kiyaye dokokinsa kuma muka bi mizanansa. Ba shi da wuya a yi haka. Maimakon su kasance matsananta, Jehobah ya tsara su ne su taimake mu mu yi rayuwa mai kyau, mai farin ciki, mai gamsarwa. (Ishaya 48:17, 18) Ta wajen rayuwa cikin jituwa da ja-gorar Jehobah, muna nuna wa Ubanmu na sama cewa muna godiya ƙwarai domin dukan abubuwa da ya yi dominmu. Abin baƙin ciki, mutane ƙalilan ne a duniya a yau suke nuna irin wannan godiyar. Bai kamata mu zama masu butulci ba, kamar wasu mutane da suka rayu sa’ad da Yesu yake duniya. Yesu ya warkar da kutare goma, amma ɗaya ne kawai ya dawo ya yi masa godiya. (Luka 17:12-17) Hakika, za mu so mu zama kamar mai godiyan, ba kamar marasa godiyan ba!

9 To, menene dokokin Jehobah da muke bukatar mu kiyaye? Mun riga mun tattauna wasunsu cikin wannan littafin, amma bari mu maimaita wasu kaɗan. Kiyaye dokokin Allah zai taimake mu mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah.

KA KUSACI JEHOBAH SOSAI

10 Koyo game da Jehobah mataki ne na ɗaya na kusantarsa. Abu ne da bai kamata ya ƙare ba. Idan kana waje a cikin sanyin dare kana ɗuma jikinka da wuta, za ka bar wutar ta lafa ne ta mutu? A’a. Za ka ci gaba da ƙara itace domin wutar ta ci gaba da kamawa. Wataƙila ka dogara ne ma a kan wutar! Kamar yadda itace ke sa wuta ta ci, haka, “sanin Allah” yake ƙarfafa ƙaunarmu ga Jehobah.—Misalai 2:1-5.

Kamar wuta, ƙaunarka ga Jehobah tana bukatar a riƙa rura ta domin ta ci gaba da ci

Wani mutum yana shan ɗumin wuta

11 Yesu yana so mabiyansa su ci gaba da ƙaunar Jehobah da kuma gaskiyar Kalmarsa mai tamani. Bayan ya tashi daga matattu, Yesu ya koyar da almajiransa biyu game da wasu annabce-annabce a Nassosin Ibrananci da suka cika a kansa. Menene sakamakon haka? Daga baya suka ce: “Zuciyarmu ba ta ƙuna daga cikinmu ba, sa’anda yana yi mamu zance a kan hanya, yana bayyana mamu littattafai?”—Luka 24:32.

12 Sa’ad da ka koyi abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa da gaske, shin zuciyar ka ba ta yi annuri ba ne, ba ta cika da himma, da ƙauna ga Allah ba? Hakika haka yake. Mutane da yawa suna jin haka. Ƙalubalen yanzu shi ne ka ci gaba da wannan ƙauna kuma ka sa ta ƙarfafa. Ba ma so mu bi yayin duniya ta yau. Yesu ya annabta: “Ƙaunar yawancin mutane za ta yi sanyi.” (Matta 24:12) Ta yaya za ka kiyaye ƙaunarka ga Jehobah da kuma Littafi Mai Tsarki daga yin sanyi?

13 Ka ci gaba da ƙara sanin Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi. (Yohanna 17:3) Ka yi bimbini ko kuma tunani sosai, a kan abin da ka koya daga Kalmar Allah ka tambayi kanka: ‘Menene wannan yake koya mini game da Jehobah Allah? Waɗanne ƙarin dalilai wannan ya ba ni in ƙaunace shi da dukan zuciyata, hankalina, da kuma raina?’ (1 Timothawus 4:15) Irin wannan bimbini zai riƙa rura wutar ƙaunarka ga Jehobah.

14 Wata hanyar rura wutar ƙaunarmu ga Jehobah ita ce addu’a a kai a kai. (1 Tassalunikawa 5:17) A Babi na 17 na wannan littafin, mun koyi cewa addu’a kyauta ce mai muhimmanci daga Allah. Kamar yadda dangantaka tsakanin mutane take ci gaba domin sadawa da ke tsakaninsu, haka nan dangantakarmu da Jehobah za ta kasance a raye sa’ad da muka yi addu’a a gare shi a kai a kai. Yana da muhimmanci kada addu’armu ta zama je-ki-na-yi-ki, kalmomi kawai da muke furtawa babu motsin zuciya ko ma’ana. Muna bukatar mu yi magana ga Jehobah kamar yadda yaro zai yi magana da ubansa abin ƙauna. Hakika, muna bukatar mu yi magana da daraja, magana ta gaskiya daga zuciyarmu. (Zabura 62:8) Nazarin Littafi Mai Tsarki da kanmu da kuma addu’a daga zuciyarmu ɓangarorin bautarmu ne masu muhimmanci, kuma suna taimakonmu mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah.

KA YI FARIN CIKI A BAUTARKA

15 Nazarin Littafi Mai Tsarki na kanmu ɓangaren bauta ne da muke yi a gida. Amma bari yanzu mu bincika wani ɓangaren bautarmu da muke yi a fili: yin magana da wasu game da abin da muka gaskata. Ka riga ka sanar da wasu game da gaskiya ta Littafi Mai Tsarki kuwa? Idan haka ne, to, ka more gata mai ban sha’awa. (Luka 1:74) Sa’ad da muka sanar da mutane gaskiya da muka koya game da Jehobah Allah, muna yin wani aiki ne mai muhimmanci da aka bai wa dukan Kiristoci—aikin wa’azin bisharar Mulkin Allah.—Matta 24:14; 28:19, 20.

16 Manzo Bulus ya ɗauki hidimarsa da muhimmanci, ya kira ta kaya mai daraja. (2 Korinthiyawa 4:7) Yin magana da mutane game da Jehobah Allah da kuma nufinsa shi ne aiki mafi kyau da za ka yi. Hidima ce ga Maigida na kirki, kuma za ta kawo lada masu kyau. Ta wajen saka hannu cikin wannan aikin, kana taimakon mutane masu zukatan kirki su kusaci Ubanmu na sama kuma su kasance a kan hanyar zuwa rai! Wane aiki zai fi wannan gamsarwa? Ƙari ga haka, yin shaidar Jehobah da kuma Kalmarsa tana ƙara bangaskiyarmu kuma tana ƙarfafa ƙaunar da muke yi masa. Kuma Jehobah yana yin farin ciki da ƙoƙarce-ƙoƙarcenka. (Ibraniyawa 6:10) Duƙufa cikin irin wannan aikin yana taimakonka ka tsaya a kan ƙaunar da Allah yake mana.—1 Korinthiyawa 15:58.

17 Yana da muhimmanci mu tuna cewa aikin wa’azin Mulki aiki ne na gaggawa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi wa’azin kalma; ka yi naciya.” (2 Timothawus 4:2) Me ya sa aikin yake da gaggawa haka a yau? Kalmar Allah ta gaya mana: “Babbar ranar Ubangiji ta kusa, kurkusa ce, tana kuwa gaggabta ƙwarai.” (Zephaniah 1:14) Hakika, lokacin yana zuwa da sauri da Jehobah zai halaka wannan zamani. Mutane suna bukatar a yi musu kashedi! Suna bukatar su sani cewa yanzu lokaci ya yi da za su zaɓi Jehobah ya zama Mamallakinsu. Ƙarshen “ba za ta yi jinkiri ba.”—Habakkuk 2:3.

18 Jehobah yana so mu bauta masa a fili cikin cuɗanya da Kiristoci na gaskiya. Abin da ya sa ke nan Kalmarsa ta ce: “Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu, kamar yadda waɗansu sun saba yi, amma mu gargaɗadda juna; balle fa yanzu, da kuna ganin ranan nan tana gusowa.” (Ibraniyawa 10:24, 25) Sa’ad da muka taru da ’yan’uwanmu masu bi a taron Kiristoci, muna samun zarafi na bauta wa Allah kuma mu yabe shi. Muna kuma gina wasu muna ƙarfafa su.

19 Sa’ad da muka yi hulɗa da wasu masu bauta wa Jehobah, muna ƙarfafa ƙauna da kuma abota a cikin ikilisiya. Yana da muhimmanci kuma mu riƙa kula da halayen kirki na juna, kamar yadda Jehobah yake kula da halayenmu na kirki. Kada ka zaci cewa ’yan’uwanka Kiristoci kamilai ne. Ka tuna cewa kowa manyantarsa na ruhaniya ya bambanta, kuma dukanmu muna yin kuskure. (Kolossiyawa 3:13) Ka yi ƙoƙari ka ƙulla abota da waɗanda suke ƙaunar Jehobah ƙwarai, za ka ga cewa kana ƙaruwa ruhaniya. Hakika, bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwanka maza da mata na ruhaniya zai taimake ka ka tsare kanka cikin ƙaunar Allah. Ta yaya Jehobah yake ba da lada ga waɗanda suka bauta masa da aminci kuma suke tsare kansu cikin ƙaunarsa?

KA CANCANCI “RAI WANDA SHI KE NA HAKIKANIN RAI”

20 Jehobah yana bai wa bayinsa masu aminci ladar rai, amma wane irin rai? To, kana rayuwa kuwa a yanzu? Yawancinmu za mu ce hakika kuwa. Domin muna numfashi, muna ci muna sha. Babu shakka, muna raye. Kuma a lokacin da muke farin ciki, muna iya ma ce, “Kai muna more rayuwa da gaske!” Amma dai, Littafi Mai Tsarki ya nuna a wata hanya mai muhimmanci cewa babu mutumin da yake raye da gaske.

Wata iyalin da ke more yanayin aljanna

Jehobah yana so ka more “rai wanda shi ke hakikanin rai.” Za ka more kuwa?

21 Kalmar Allah ta aririce mu mu “ruski rai wanda shi ke hakikanin rai.” (1 Timothawus 6:19) Waɗannan kalmomi sun nuna cewa “rai wanda shi ke na hakikanin” wani abu ne da muke begen samu a nan gaba. Hakika, sa’ad da muka zama kamilai, za mu zama masu rai a cikakkiyar ma’anarta, domin za mu rayu kamar yadda Allah ya nufa tun farko. Sa’ad da muke raye cikin aljanna a duniya da cikakken koshin lafiya, salama, farin ciki, a ƙarshe za mu more “rai wanda shi ke hakikanin rai”—rai madawwami. (1 Timothawus 6:12) Wannan ba bege ba ne mai ban sha’awa?

22 Ta yaya za mu “ruski rai wanda shi ke hakikanin rai”? A cikin wasiƙar, Bulus ya aririci Kiristoci “su yi alheri” da kuma “mawadata cikin kyawawan ayyuka.” (1 Timothawus 6:18) To, a bayyane yake cewa ya dangane ne bisa yadda muka yi amfani da gaskiya da muka koya daga cikin Littafi Mai Tsarki. Amma Bulus yana nufi ne cewa za mu sami “rai wanda shi ke hakikanin rai” ta wajen yin ayyuka nagari? A’a, domin irin wannan bege ya dangana ne bisa samun “alherin” Allah. (Romawa 5:15) Duk da haka, Jehobah yana farin cikin ba da lada ga waɗanda suka bauta masa cikin aminci. Yana son ya ga ka sami “rai wanda shi ke hakikanin rai.” Irin wannan rai madawwami na farin ciki, da salama, yana gaban waɗanda suka tsaya a kan ƙaunar da Allah yake yi musu.

23 Yana da kyau kowanenmu ya tambayi kansa, ‘Ina bauta wa Allah a hanyar da ya kafa kuwa cikin Littafi Mai Tsarki?’ Idan mun tabbata, kowace rana, cewa amsar mu e ce, to, muna kan hanya da take daidai. Za mu yi ta tabbatawa cewa Jehobah mafakanmu ne. Zai kuma kāre mutanensa masu aminci a cikin waɗannan kwanaki na ƙarshe na bala’i na wannan zamani. Jehobah kuma zai kai mu cikin sabuwar duniya mai ɗaukaka da ta yi kusa. Zai kasance abin farin ciki mu ga wannan lokaci! Kuma za mu yi farin cikin mun zaɓi abin da ya fi a wannan kwanaki na ƙarshe! Idan ka zaɓi wannan a yanzu, za ka more “rai wanda shi ke hakikanin rai,” rayuwa kamar yadda Jehobah Allah ya nufa a cikin dukan dawwama!

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

  • Muna nuna ƙauna ta gaskiya ga Allah ta wajen kiyaye dokokinsa da kuma bin mizanansa.—1 Yohanna 5:3.
  • Nazarin Kalmar Allah, yin addu’a ga Jehobah daga zukatanmu, koyar da mutane game da shi, da kuma bauta masa a taron Kiristoci za su taimake mu mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah.—Matta 24:14; 28:19, 20; Yohanna 17:3; 1 Tassalunikawa 5:17; Ibraniyawa 10:24, 25.
  • Waɗanda suka tsare kansu cikin ƙaunar Allah suna da begen more “rai wanda shi ke hakikanin rai.”—1 Timothawus 6:12, 19; Yahuda 21.

Tambayoyin Nazari

1, 2. A ina za mu sami mafaka mai kyau a yau?

3. Ta yaya za mu mai da Jehobah mafakarmu?

4, 5. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya nuna yana ƙaunarmu?

6. Ta yaya za ka amsa ƙauna da Jehobah ya nuna maka?

7. Motsin zuciya ce kawai ƙaunar Allah? Ka yi bayani.

8, 9. Ta yaya za mu nuna ƙaunarmu ga Allah kuma mu nuna muna yi masa godiya?

10. Ka yi bayanin abin da ya sa yake da muhimmanci mu ci gaba da ƙara sani game da Jehobah Allah.

11. Yaya koyarwar Yesu ya shafi mabiyansa?

12, 13. (a) A tsakanin yawancin mutane a yau, menene ya faru da ƙaunar Allah da kuma Littafi Mai Tsarki? (b) Ta yaya za mu kiyaye ƙaunarmu daga yin sanyi?

14. Ta yaya addu’a za ta taimake mu mu rura wutar ƙaunarmu ga Jehobah?

15, 16. Me ya sa za mu ɗauki aikin wa’azin Mulki gata ce da kuma kaya mai daraja?

17. Me ya sa hidimar Kirista take da gaggawa a yau?

18. Me ya sa za mu bauta wa Jehobah a fili cikin cuɗanya da Kiristoci na gaskiya?

19. Ta yaya za mu ƙarfafa ƙauna a cikin ikilisiya ta Kirista?

20, 21. Menene “rai wanda shi ke hakikanin rai,” kuma me ya sa bege ne mai ban sha’awa?

22. Ta yaya za ka “ruski rai wanda shi ke hakikanin rai”?

23. Me ya sa yake da muhimmanci mu tsaya a kan ƙaunar da Allah yake yi mana?