Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RATAYE

1914—Shekara Mai Muhimmanci a Annabcin Littafi Mai Tsarki

1914—Shekara Mai Muhimmanci a Annabcin Littafi Mai Tsarki

ƊALIBAN Littafi Mai Tsarki sun yi shelar cewa abubuwa masu muhimmanci za su faru a shekara ta 1914 na kusan shekara 40. Menene waɗannan abubuwa masu muhimmanci, kuma wane tabbaci ne ya nuna cewa shekara ta 1914 shekara ce mai muhimmanci?

Kamar yadda yake rubuce a Luka 21:24, Yesu ya ce: “Al’ummai za su tattake Urushalima kuma har zamanan Al’ummai sun cika.” Urushalima ita ce babbar birnin al’ummar Yahudawa—mazaunin gadon sarautar sarakuna daga zuriyar Dawuda. (Zabura 48:1, 2) Amma, waɗannan sarakuna sun bambanta da sarakunan wasu al’ummai. Suna zama ne bisa “kursiyin Ubangiji” suna wakiltan Allah kansa. (1 Labarbaru 29:23) Saboda haka Urushalima alama ce ta sarautar Jehobah.

Yaushe kuma ta yaya al’ummai suka fara “tattake” sarautar Allah? Wannan ya faru ne a shekara ta 607 K.Z., sa’ad da Babiloniyawa suka ci Urushalima a yaƙi. “Kursiyin Ubangiji” ya kasance babu kowa a kai, kuma aka taɓa zuriyar sarakuna da ta samo asali daga Dawuda. (2 Sarakuna 25:1-26) Wannan ‘tattakewa’ za ta ci gaba ne har abada? A’a, domin annabcin Ezekiel ya ce sarkin ƙarshe na Urushalima, Zedekiah: Ya “kawarda rawani, [kuma] tuɓe ƙambi:…har lokacin da wannan ya zo wanda wajibinsa ne, ni ma im ba shi.” (Ezekiel 21:26, 27) Wanda “wajibinsa” ne ƙambin zuriyar Dawuda Yesu Kristi ne. (Luka 1:32, 33) Saboda haka ‘tattakewa’ za ta ƙare sa’ad da Yesu ya zama Sarki.

Yaushe ne wannan babban abu zai faru? Yesu ya nuna cewa ’yan al’ummai za su yi sarauta na wani tabbataccen lokaci. Batun da ke cikin sura 4 na Daniel ya ƙunshi mabuɗin sanin tsawon wannan lokaci. Ya ba da labarin mafarki da Sarki Nebuchadnezzar na Babila ya yi. Ya ga wani babban itace da aka sare. Gindin sawayensa ba zai iya girma ba domin an ɗaure shi da ƙarfe da jangaci. Mala’ika ya sanar: ‘A bar wokatai guda bakwai kuma su bi ta bisa kansa.’—Daniel 4:10-16.

A Littafi Mai Tsarki, a wani lokaci ana amfani da itace wajen wakiltan sarauta. (Ezekiel 17:22-24; 31:2-5) Saboda haka sare wannan itace na alama yana nuna yadda za a taɓa sarakuna a Urushalima waɗanda suke wakiltan sarautar Allah. Wahayin kuma ya ba da gargaɗi za a “tattake Urushalima” na ɗan lokaci—“wokatai bakwai.” Yaya tsawon wannan lokaci yake?

Ru’ya ta Yohanna 12:6, 14 ta nuna cewa lokatai uku da rabi sun yi daidai da “kwana dubu da metin da sattin.” Saboda haka, “wokatai bakwai” zai ninka tsawon wannan, ko kuma kwanaki 2,520. Amma Al’ummai ba su daina tattake sarautar Allah ba bayan kwanaki 2,520 bayan faɗuwar Urushalima. A bayyane yake cewa lokaci na wannan annabci ya fi haka tsawo. Bisa ga abin da ke Littafin Lissafi 14:34 da kuma Ezekiel 4:6, waɗanda suka yi maganar “rana guda domin shekara guda,” “wokatai bakwai” zai kasance shekara 2,520.

Shekara 2,520 ya fara a watan Oktoba shekara ta 607 K.Z., sa’ad da Babiloniyawa suka ci Urushalima aka tunɓuke sarautar zuriyar Dauda daga kursiyinsa. Wannan lokaci ya ƙare a shekara ta 1914. A wannan lokaci, “zamanan al’ummai” ya ƙare, kuma aka naɗa Yesu Kristi ya zama Sarkin Mulkin Allah na samaniya.*—Zabura 2:1-6; Daniel 7:13, 14.

Kamar yadda Yesu ya annabta, ‘bayyanuwarsa’ Sarki a samaniya ya zo da aukuwa masu ban mamaki—yaƙi, yunwa, girgizar ƙasa, annoba. (Matta 24:3-8; Luka 21:11) Waɗannan aukuwa sun ba da tabbaci cewa shekara ta 1914 mafari ce ta Mulkin Allah kuma mafari ce ta “kwanaki na ƙarshe” na wannan mugun zamani.—2 Timothawus 3:1-5


*  Daga Oktoba na shekara ta 607 K.Z., zuwa 1 ga Oktoba K.Z., shekaru 606 ne. Tun da babu shekara ta sifiri, daga 1 ga Oktoba shekara ta 1 K.Z., zuwa Oktoba shekara ta 1914 shekaru 1,914 ne. Idan aka haɗa shekara 606 da shekara 1,914, sai mu sami shekaru 2,520. Domin bayani game da faɗuwar Urushalima a shekara ta 607 K.Z., ka dubi talifin nan “Chronology” (Tsarin Shekaru) a Littafin nan Insight on the Scriptures, da Shaidun Jehobah suka wallafa.

“BAKWAI BAKWAI”
Shekaru 2,520
Shekaru ta 606 1/4
Daga Oktoba 607 K.Z. zuwa
31 ga Disamba, 1 K.Z.
Shekaru 1,913 3/4
1 ga Janairu, 1 A.Z. zuwa
Oktoba 1914
607

“Al’ummai za su tattake Urushalima”

An halaka Urushalima
←K.Z. A.Z.→ 1914

“Wanda wajibinsa ne”

Yesu Kristi a matsayin Sarki

← Ka duba inda babin yake